Page 10

36 2 0
                                    

💖💖GIDAN AUNTY💖💖

    ( A heart touching love story)

Story &written

     By

Mss Lee💖

PAID BOOK

MAISAN AYI MASA TALLAN KAYANSA YAMUN MAGANA TA WANNAN NUMBER 07041879581

BOOK 1 📕

Free page 10 🦋

Shigowar bintalo dakin kamar wacce aka jefo ta ko sallama babu, yasa dije kamewa, komai sai ya tsaya mata, kallan kanta da dungayi ganin duk ta ya mutsa jikinta, kallan ta bintalo tayi rai a bace tana toshe hanci "Haba Dije , kazantar taki har takai kiyi kashi a jikinki, gaskiya kina bada ni , ji beki katuwar kawai sai wari kike faman yi , ga kashin ki me shegen d'oyi, ta karasa da hararanta. Dije ce ta soma magana "Haba bintalo , Kema kinsan haka kawai bazanyi kashi a jiki ba , lalurace ta sameni , ni kaina bansan ya akai hakan ta faru ba", ta kare zance da zunbula hijabi, gudun kar yan gidan su ganta, tayi sauri tashige bayi bayan dan ruwan da ta dauka a buta.

Su tahee ma ransu fess suka koma daki, bayan sun gama aikin su , haka suka yini a daki, lokaci zuwa lokacin tunanin dan iskan da akace za a aura mata yana fado mata arai.

*******

A kwana a tashi ba wuya wajan Allah SWT, yau watan su tahee 1 da 'yan kwanaki a bunkure, abubuwa da dama ya faru ciki harda maganar Auran tahee da tanimu da tayi mugun tsana. A yan kwanakinan ba karamun wuya suke shaba wajan mutanan gidan, musamman kaka tabawa da dije datayi mugun tsanar su, kullum da kalar ukubar da zasuyi musu, abu daya ne ke kwatarsu , duk lokacin da kaka ta bawa ta wahalar da su ranar bata iya baccin arziki sai safiya , a lokacin su tahee ke samun damar hutawa . Taheer ma yanxu ya koyi faci, Inya futa tun safe bashi ke dawowa ba sai 6 na yamma, a gida kuwa daga oumma sai tahee, yanxu ma kwance take kan cinyar oumma tana taje mata uban tilin gashin kanta da ya zubo har gadan bayanta da cikon da yake dashi, "oumma"cewar tahee,"naam aunty tahee"oumma ta amsa mata cikin zolaya , dariya tahee ta saka, "Allah oumma ni banasan wannan gashin kan nawa wani lokuta, kallifa ko tajeshi bana iyayi da kyau, "aikinsan hanyar iliya me aski, sai kije ya aske miki", turo baki kawai tahee tayi dan tasan magana oumma ta fada mata.

Suna zaune sukaji an banko kofar dakin , duk kallan kofar sukai lokaci daya , bintalo dake tsaye se faman cika take ta kalli tahee ba ko sallama , "toh matar mashayi sai kije angwan naki yazo", tana gama fadar hakan ta banko musu kofa. Tsaki tahee taja tana kokarin kontawa oumma ta dakatar da ita "tashi kije"bata ce wa oumma komai ba ta zura hijabinta tare da ficewa waje.

A tsaye ta ganshi cikin wasu yan iskan Riga da wando, sai faman tashin warin giya yake, saurin toshe hanci tahee tayi jin zata yi amai, ga bakikkirin bakar fuskarsa sai faman naso nake , cikin Maye ya zuba wa tahee jajan idanuwansa" ke dan uwarki , shine zan dunga kiranki kina kin zuwa, ke gaki yar iska ko" ya karasa yana tangal tangal kamar ze fado mata, matsala tahee tayi baya tana binsa n da kallan tsana "inka gama zan wuce dan banda lokacin dan iska", wayo idanuwansa yayi cikin maye yana kifkifta kana nun inaduwansa" ke, ni kike cewa dan iska dan uwarki, toh bari na nuna miki iskanci, kafun na bada sadaki zan d'anaki nasan zakiyi ruwa" ya karasa tare da daga hannunsa zai tabata, saukar marin da yaji a fuskarsa ne yasa shi tangal tangal zai fadi, ganin yana ganin biyu biyu ne yasashi kara ware mummunar fuskarsa " kutumar ubancan , ya na fara ganin garin yana juyawa ko an fara hazo ne "be kammala maganar tasaba tahee da idanuwanta suka juye ta kara tsinka masa mari" saurin dafe fuskar tasa yayi har yanxu bakin nashi be mutu ba" auzubillahi, ko an fara tafiya lahira ne ban sani ba" saukar marin da yaki a fuskarsa ne ya sashi zabura da fita "shikenan  a fara sha hada , an fara mutuwa ", sai da ya bace wa ganin ta sannan idanuwan ta suka dawo Daidai ganin ba kowa a wajan yasata dage kafada da komawa cikin gida . Koda ta kowa cikin gidan oumma bata ce mata komai ma , itama tahee batace komai ba sai hirarsu da suka cigaba .

GIDAN AUNTYWhere stories live. Discover now