Page 32

27 2 0
                                    

💖💖GIDAN AUNTY💖💖

    (a heart touching love story)

Story & written

    By

Mss Lee 💖

PAID BOOK

MAI BUKATAR COMPLETE DIN GIDAN AUNTY YAMUN MAGANA TA WANNAN NUMBER 07041879581.

BOOK 1 📕

Page 32💖

Sanye take cikin wasu baka'ken kaya ba'a ganin ko ina na fuskarta hatta kwayar idanuwanta ta kulle su da bakin glass,magana take da wani da shima ba a iya ganin fuskarsa cikin wani yare mara dadin ji, wata yar karamar leda ya mika mata ,cikin ta wani farin abune aciki,tana ganin abun da ya bata ta kyalkyale da dariya kafun ta soma magana "tabbas a wannan karan burin mu na daf da cika, tunda munyi nasarar juyawa yarinyar kwakwalwa,ta Hakane zamuyi anfani da ita muka she wancan tsinannan ,burinmu na cika sai mu dora mata lefi,tabbas wannan karan za a jubda Jini",babbakewa da dariya mutumin yayi kafun ya soma magana,"tsawan shekaru na dauka ina jiran wannan lokacin, da dukiyar NAHYAN zata dawo hannuna,kina tunanin zanyi sake da wannan damar,basu kadai ba,duk Wanda yayi kokarin rutsemun ginin da na dade ina gidawa babu abunda zai hana muga bayinsa,kamar yadda muka ga bayan mohammad"lokaci d'aya suka babbake da dariya tare da zuya harshen su zuwa wani yare da baba ganewa.

🫧🫧🫧🫧🫧

Karfe 6:30am ya turo kofar dakin a hankali,tun futar dayi dazu be kara dawowa ba,a takure ya hangota kansaman gadon ta takure jikinta,ba a hango komai nata sai fuskar ta dake a ya mutse,a hankali ya fara taku tare da nufar bakin gadon ,gabaki d'aya dakin tashin kamshin imperial majesty yake,sosai kayan jikinsa sukai masa kyau,sanye yace cikin wani red suit me shegen kyau, fuskarsa sanye yake cikin wani bakin glass da baka iya hango kwayar idanuwansa,sosai glass yin yayi wa fuskarsa kyau musamman dan karamin pink lips dinsa da ya kara fito da ainahin sajan sa,gashin kasansa sai kyalli take kamar kullum kara mata yawa ake,kallan diamond watches dinsa yayi kafun ya mayar da kallansa kan fuskarta da take baccin ta har yanxu ,sabanin dazu yanxu harda dan turo dan karamin bakin ta duk da bacci take, guntun tsaki yaja kafun ya taba pillow da kanta yake,motsa fuskarta tayi tana kara cono bakinta gaba,wani tsakin ya kara ja yana dafe goshinsa da ke Sara masa, kara taba pillown yayi ganin bata motsa bane a hankali ya furta "ke", nan ma bata motsan ba ,da dan karfi ya daki pillow din a bazata ta mike da niyar guduwa, dan karamin tsaki yaja yana furta "matsoraciya kawai " cikin kasan makoshinsa,kafun ya kalleta,"baki iya sallah bane,komai sai an koya miki" ya furta yana kara tsuke fuskarsa , shiru kawai tayi tana faman rarraba ido kafun ta turo karamin bakinta, "dady" ya furta da shakakkiyar muryarta,kallan yadda tayi maganar yayi kafun ya furta "momy"shima yana harararta,dariya ta kyalkyale dashi,be bari ta kara magana ba ya furta je kiyo alwala, gyada masa kai kawai tayi,sosai ta gane kofar da zata kai ta toilet,baka kara cewa komai ba ta mike tsaye dukda kasan cewar bariga a jikinta haka ta mike ,tana nufar kofar, saurin kawar da kansa yayi da ka kallanta ,yana ganin ta shige kofar shima ya fita daga dakin.

*****tun da ta shiga toilet din tsayawa kawai tayi tana bin ban dakin da kallo kafun ta dafe kanta da taji ya fara mata ciwon, sosai ta tsaya kallan bandakin ,cikin karan bani ta nufi wani glass dake kewaye da ban dakin, tsayawa tayi tana zubawa wajan idanu "toh shi dady yasan nan wani dakin ne shine zaice mun nazo"har ta juya daniyar komawa sea taji tana jin fitsari,kallan Inda zatayi futsarin ta fara dubawa,har ta tsugunna sai kuma ta tashi,kallan toilet tayi kamar me san tuno wani abu,kafun ta karasa wajan a hankali ,bakin tight dinta tacire jin ta fara yin futsarin,amai makon fitsarin kuma sai ga Jini, a firgice ta saki kara cikin razana ganin Jinin da tayi "dady ,dady" ta ke furtawa cikin birkicewa, cikin sauri ta nufi kofar fita daga ban dakin, Daidai ta taba hannun kofar toilet da niyar fita kanta ya sara mata,Kallan kafar tata tayi kafun kuma ta koma cikin bandakin,kamar tasan yadda ake anfani da kayan toilet din,sosai kuwa ta wanke jikinta har da zarcewa da yin Wanka da kayan wankan toilet din,kamar wacce ake controlling dinta, ban dakin sai faman tashin kamshi yake,komai a nutse take yi bayan ta kammala wankan harda gyara ban dakin duk da babu abunda tayi, fito wa tayi daga toilet din tana bin wajan da kallo, trolley din da king ya shigo da ita jiya ta tsaya bi da kallo, kafun ta karasa wajanta,budewa tayi a hankali tana bun jerarrun kayan dake cikin jakar,tsayawa kallansu tayi sosai kafun ta dakko wata doguwar riga baka sai digo digon ja dake jikinta, kara kallan jakan tayi,kafun ta sa hannu ta dauki wata jaka a ciki, bude cikin jakar tayi inners ne a cikin jakar sai pad shima,pant da bra ta dauka har zata kulle jakar sai kuma ta dauki pad din guda d'aya ,tare da Mayar da trolley din ta rufe kamar yadda ta ganta, a nutse ta saka pad dinta da pant, a wannan lokacin har bra dinta ta saka kafun ta kalli rigar dake gefenta,murmushi ta saki da har dimples dinta na dama da hagu na lobawa kafun ta saka rigar, bakaramun kyau rigar tayi wa jikinta ba musamman da ta kasance fara sai kayan suka haskata kasan tuwar kalan kayan ne ja da baki, hips dinta sosai ya fito cikin rigar jikinta ,yalwataccen gashin kanta da ya sakko har gadon bayanta me shegen cikowa ta kama da niyar tufkewa amma ta kasa,sosai ta fara kiciniyar yadda zata kamashi,ganin ta kasane yasa ta dakko gyalan kayanta daniyar barin dakin, taku d'aya biyu tayi kanta ya sara mata,tsayawa tayi tana bin inda take da kallo , tunani ta shigayi kafun ta turo dan karamin bakinta"to ni ya naganni a nan ba nashiga can ba" ta karasa zan can nata tana nuna kofar toilet ,sai kuma idanuwanta suka sauka kan kayan jikin ta , wayo manyan idanuwanta tayi tana bun jikinta da kallo, kafun ta kai hannu ta shafa kamar me tsoran shafawa, cikin Sauri ta dauke hannunta,"ko dady ne yamun wayo ,yasamun kayannan " tunanin hakan yasa ta saki murmushi, cikin sauri ta karasa kofar fita daga dakin gashin kanta duk ya rufe mata fuska, bude komar datai ba wuya ta hango dadin nata na kokarin kai wani kyakkyawan cup bakinsa ,a guje ta nufi inda yake tana sakin gyalan hannunta,Daidai zai kai cup din bakinsa ta saki kara "dady",dan juyo da idanuwansa yayi yana kokarin Shan coffee dinsa ta daka tsalle tare da bare kofin hannunsa,hawaye duk ya bata fuskarta cikin rawar murya ta furta "dady karkasha ,ansa guba ".....

GIDAN AUNTYWhere stories live. Discover now