Page 22-23

34 2 0
                                    

💖💖GIDAN AUNTY 💖💖

(a heart touching love story)

Story & written

By

Mss Lee 💖

PAID BOOK

NA KUSA KAMMALA FREE PAGES DINA

Mesan KARANTA GIDAN AUNTY DAGA FARKO ZUWA KARSHE ZAI IYA BIYAN KUDINSA TA WANNAN ASUSUN 7041879581 palm pay ayshatou galadima sai a turo shaidar biya ta wanna number 07041879581

BOOK 1

Free page 22 and 23 🦋

A kwana a tashi ba wuya wajan Allah SWT, yau kusan sati biyu kenan da batan su oumma , Tsawan wannan lokaci babu Wanda ya damu da yasan inda suke ,hatta kaka ta bawa da ta share zancen, cikin wannan lokacin sosai bintalo ta fara bin maza ,ganin hankalin yan gidan su nasan komawa kanta ta koma wajan bokannan da mahaifiyarta Ke zuwa, gaba daya ta mallakesu ko dare zatayi babu me tanbayarta dalili, sosai ta baci da kazamin rayuwarnan, Dije kuwa kullum cikin farin ciki take idan bintalo ta Kawo mata kudi ko damuwa da inda ta ke samo kudin batayi,burinta ya cika tun lokacin da oumma tabar gidan,yanxu burinta ta kai bintalo can birni wajan da tahee take sannan itama tasa taheen ta shiga duniya.

🫧🫧🫧🫧🫧

A tsawan kwana kinnan sosai wata shakuwa me karfi tashiga tsakanin zoya da tahee, kullum in ta dawo daga makaranta zaki ganta wajan tahee tana fada mata abunda aka koya musu, yawancin lokuta suna part din ummey ko part din dada da yanxu take kulawa da ita sosai, ta bangaran yan gidan ma haka, momy tana sake mata sosai sabanin mamy da aunty,musamman aunty da ke nuna mata kyautata mata agaban yan gidan , abayansu kuma taita zaginta, ihsan da firdausi ma sosai suka sake mata a yan kwanakin nan, amrah da sumayya ne ko kallo basu isheta ba,ganin hakan yasa itama bata sake musu fuska. Cikin yan kwanakin nan sosai tayi kewar su oumma tanaso tacewa aunty ta kira mata su amma bata san ta yadda zata tanbaye taba.

Yau ma tunda ta tashi da kewar su oumma ta tashi,so take kawai taji muryarsu sabida mummunan mafarkin da tayi a kansu, sai faman zagaye take a daki tana tunanin ta yadda zata tanbaye ammi , ganin bata da wata mafitane yasa ta mikewa tare da fitowa falo a hankali kamar Mara gaskiya, Daidai tana fito wa shi kuma yana shigowa ciki, kamewa tahee tayi wajan tare da rintse idanuwanta,yau sati biyu kenan rabanta da ta gansa, sosai ya kara yi mata kyau kamar kullum kara masa shi ake , a hankali tayi kokarin bude idanuwanta jin yadda zuciyarta ke bugawa da sauri sauri ga kamshin turaransa da ya cika mata hanci, da gyar ta karasa bude idanuwannanta, Ganin baya wajan kamar yadda tayi tunani yasata sakin ajiyar zuciya, ta juya daniyar komawa kenan idanuwanta suka sauka a kansa, kyawawan fararan idanuwanta ta zuba masa duk da yadda zuciyarta ke faman bugawa, sosai shigarsa tayi mata kyau musamman gyaran gashinsa da ya tubke sai faman kyalli yake ,sak ya fito a balaraben sa dan Inba Hausa yayi baza ka taba tunanin yasan Menene kalmar ba, wayace a hannunsa sai faman dannawa yake cikin kwanciyar hankali,fuskarsa kwata kwata ba annuri kamar Wanda yayi rashin lapiya ga kafar sa da yayi crossing lokaci zuwa lokaci yana motsata, a hankali ya motsa pink lips dinsa kamar me sanyin magana sai kuma ya fasa tare da datse lips din nasa,tunda ta Kafe shi da ido ko motsi batayi sam ta manta ma agaban watake, a hankali ya dago da idanuwansa karaf suka hade da nata,bata janye idanuwan ba sai ma sarkewa da idanuwansu sukai cikin na junansu , bata farga da shirmen da take ba sai jin saukar tsawar sa tayi, sosai ta razana juyawa tayi daniyar guduwa ta ji saukar muryarsa "if you dare "ya karasa kamar be san yin magana , cak tahee ta Tsaya kamar me shirin sakin kuka , ahankali take juyo da fuskarta da ta dukar sosai take jin kunyar abunda tayi ,zuciyarta sai faman bugawa take da sauri da sauri kamar wacce tayi gudu. Lokaci zuwa lokaci take dago da idanta ganin hankalinsa baya kanta cikin rawar murya ta soma magana " ina wu..ni", be amsa mata ba haryanxu idanuwansa na kan wayarsa, kara dukar dakai tayi tana wasa da kasan hijabin jikinta,"ina wuni" ta kara gaishesa cikin rawar murya, yanxun ma be amsa mata , ganin hakan itama ta shareshi tana dan turo dan mitsitsin bakinta, dauke gansa yayi daka kallan dan mitsitsin bakin da ta motsa kafin cikin kasa kasa da murya ya furta "coffee",kara turo dan mitsitsin bakin nata tayi gaba kafin ta nufi hanyar kitchen din , cikin kan kanin lokaci ta kammala hada coffee din azuciyarta sai faman mitar Shan coffee din nasa take ,"coffee ,coffee", kafun kuma ta sassaita nutsuwarta ta fito falon, a yadda ta barsa a haka tazo ta samesan yana zaune da kafarsa da yayi crossing, duk da yadda zuciyarta ke rawa hakan be sa nutsuwarta fito wa ba" gashi" ta mika masa tana dan russunawa, be fi sakon biyu ba yasaka hannunsa kan dan karamin tray din da ta miko masa, sipping ya fara a hankali,ta kasan ido tahee take satar kallansa "shi wannan kullum cikin Shan coffee ko abincin arziki be ci,nan gaba inaji sai coffee dinnan ya fito masa a jiki", ita kadai take hirar ta a zuciya,kamar yasan me take tattaunawa ya dago da idanuwansa ,saurin sunkuyar dakanta kasa tayi, dan ta bile bakinsa yayi kafin ya soma magana" get me something to eat ",da sauri ta dago idanuwanta jin abinda yace , bata ce komai ba sai kitchen da ta nufa, a ba'kin gas ta tsaya tana karewa kitchen din kallo,tu nani ta fara me zata dora masa Mara sauki , ganin tana bata lokaci ne yasa ta nufar babbar freezer din kitchen, manyan tilapia fish ta dakko guda biyu , cikin kwarewa ta gyara kifin kafun ta feraye Irish potatoes dinta, bata dau dogon lokaci ba ta kammala hada grilled fish dinta ,da yaji sauce din Dankali sai faman tashin kamshi yake, kunun ayan da ta ga ammi ta jera a fridge ta dakko tare da zubawa cikin madaidai cin jug, cikin lokaci kankanin ta kammala hada abincin , kafin ta fito falo zuciyarta sai bugawa take, hanyanxun yana zaune a falon sabanin dazu yanzu ya dan jingida da jikin kujeran, sunkuyar da Kai tayi kasa,"ga abincin", be ce mata komai ma sai gyara zamansa da yayi kafun ya bude plate din, sosai yadda aka kawata abincin ya burgeshi amma a zahiri sai ma tabe bakinsa da yayi, be kulata ba ya faraci a hankali , 3 spoon yayi kawai tare da Shan kunun ayar Daidai lokacin da ake shigowa part din da sallama , ammi ce ta fara shigowa bayanta kuma su amrah ne , duk tsayawa sukai cirko cirko a tsaye kafun ammi ta karaso falon cikin mamaki,"son Yaushe ka shigo"kamar bazea ce komai ba sai kuma ya bude baki "am looking for u", murmushi ta sakar masa "sorry son ina tare da su ummey ne", lumshe mata idanuwansa yayi, cikin rawar murya su amrah suka bude baki tare da gaishesa, ba Wanda ya amsawa a cikin su saima cigaba da tsakurar abincin da yayi kamar Wanda aka saka dole , kallan tahee dake tsaye ammi tayi, "daughter yanaganki a tsaye ke kuma , kisa mu waje ki zauna mana " dan dago da kanta tayi kadan tare da satar kallansa ,be dena abunda yake ba hakan yasata sauke a jiyar zuciya kadan ,cikin rarrabewar murya ta furta "daman ina gyara dakine ", jinjina mata kai ammi tayi ba tare da tace komai ba ganin hakan tai saurin nufar dakin ta, da kallo su amrah suka bita dashi ko wannansu na mamakin ganinta a falon.



GIDAN AUNTYWhere stories live. Discover now