Page 1-5

583 18 0
                                    

👺👺👺
👺 👺
👺
*RASHIN SANINE SILA.....*
👹👹👹
👹 👹
👹

*A TRUE LIFE STORY*

*By*

*Nusaiba i Usman Z.S*

*IDON MIKIYA WRITTER'S ASSO*🦅

*_BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM_*

*_YA ALLAH INA ROƘONƘA DA ƘAƁANI IƘO YADDA NAFARA WANNAN LITTAFI MAI SUNA A SAMA CIƘIN LAHIYA NA GAMA LAHIYA..._*

*INA ALFAHARI DA KE KHADIJA CANDY AKO DA YAUSHE KECE SILA, KECE SANADI, KEKIKA SANI KAN HANYA, INA MAI ROK'ON ALLAH YA K'ARA DAUKAKA KI KIFIHAKA ALLAH KAREKI DAGA MAHASSADA NI TAKICE MAI ALFAHARI DAKE HAR ABAFA ALLAH KARA MAKI LAHIYA ALLAH BIYA MAKI BUKATUNKI NA ALKHAIRI*

*WANNAN LITTAFIN NAWA SADAUƘARWA NE GA ƘAWAYEN ARZIƘI INA GODIYA DA ƘARFIN GWAIWA DA ƘUƘE BANI INA ALFAHARI DA KU ALLAH BAR ZUMUNCI AMEEN SUMMA AMEEN*

_*NAFEESAT YUSUF*_
Feenah baby
_*SUWAIBA.U.ADAM'S*_
Subie
_*ZEEBNAB YAƘASAI*_
Queen
_*AYUSHA ILIASU*_
Queen
_*ANTY QUEENMERMUE*_

*View...*

nusaibaiusmanzs.WordPress.com

1⃣➡5⃣

Daji ne mai tsananin duhu wanda iya kallonka baida ƙarshe, duhu ne sosai wanda ba wani mahalukin da ya isa ya gane dare ko rana koda yaushe a duhu yake babu kowa a gun sai mutum d'aya tallin tal wanda shima kansa baisan sanda yazo gunba, buɗan idonsa Kawai yayi ya gansa cikin wannan mummunan dokan dajin mai ban tsaro, a tsorace yake ya miƙe ahankali yana kalle kalle ga wani tsoro da ya rufar masa, gaba d'aya baya cikin hankalin sa daya gaji da waige waige ya samu wata jikin bishiya ya rakube ya matse jikinsa gu gud'a ahaka ya d'auki tsawon lokaci, ga yunwa da k'ishin ruwa da sukabi suka addabe shi amma bata su yake ba a yanzu yadda zaifita daga wannan iftila'in da yake ciki so yake ya tunano wani abu amma kwanyar sa ta toshe ya kasa, koya fara k'ok'arin yin hakan sai wani abun razanarwa yazo ya tsorata sa, baya iya koda rufe ido ne, daya rufe sai yaga wani abun bantsoron ya tunkaro shi gadan gadan zai cutar da shi sai yayi maza ya bude ido ba shiri.

Ko wanna rana da irin tsoratarwar da ake yi masa a kwana a tashi koda bai gane dare ko rana ko yaushe dare ne.

Zaune yake bisa wani ɗanƙaramin dutse ya zabga tagumi tunani yake sonyi amma ya kasa wani ƙara yaji da kuwwan iska mai haɗe da guguwa,da rugugi da walkiya kamar za'ayi ruwa dajin sai amsa kowa yake, zabga zabgan itatuwan sai rausaya suke kamar zasu taɓa ƙasa in iskan ya buge su sai sutafi luuuuu kamar zasu karye sai kuma su ɗago cenn lafawar iskan sai wani sauti ya fara dokan dodon kunnuwan sa nan da nan jikin sa ya fara tsuman tsoro daga kansa sama keda wuya sai ya hango wasu halittu munana baƙaƙeƙirin da zabga zabgan kunnuwa idanun su baƙin ƙirin can cikin idon su ne zaki hango ɗan ɗigon ja kamar garwashin wuta gasu da rantama rantaman kai da zaƙo zaƙon haƙwara harcen su waje sai kore(green)ɗin miyau ke fita ta,bakin su girman hancin su ko ahaɗa da Little Princess da Sumay🤣tsab zasu shige harda sauran ragowar guri, sai bulbulowa suke kamar kiyashi na fitowa daga ramin su tsayin faratansu da tsinin su yakai tsinin allura,saukowa suke suna shiga ƙarƙashin ƙasa,na farko ƙasannan ba tsagewa tayiba kuma ba rami bane amma da sunzo sai su wuce abunsu haka zalika saman ma bawani ƙofa bace ta buɗe ba kuma tsagewa tayi ba suke fitowa.

Aminu suman tsaye yayi don tsananin tsoro yananan ahaka bai gusheba baiyi aune ba sai gani yayi wasu daga cikin su sunyo kansa ba shiri ya juya ya ranta anakare amma wani abun mamaki gudu yake iya ƙarfin sa amma yanana inda yake koda yaga haka sai tsoro ya kuma kama sa bai kuma daina gudu agu ɗaya ba.
Wani irin kuwwa ɗaya daga cikin waɗsnnan halittun yayi wanda bai da ɗaɗinji nan da nan dajin ya gauraye da wannan ƙarar yayi sauri ya toshe kunnen sa yana jujjuya wa agun sai kuma cen yaji ɗib kamar an ɗauke wuta ƙarar ya tsaya sai gurnanin su ahankal ya sauke hannun sa daga kunnen sa ya ɗago aiko ya kuma yin arba da waɗannan munanan halittun sun tsaya suna kallon sa atare suka ɗaga hannu suna shirin yagalgala shi kawo masa yaga sukayi atare kamar waɗanda aka basu umurni,Aminu ji yayi an fizzeshi kafin ƙiftawan ido saiya tsinci kansa a wani dajin da yafi wanda ya bari muni.

Shi kuma wannan dajin yafi wanda ya baro tsananin duhu ga wasu zabga zabgan itatuwa iya hangen ka basu da ƙarshe sai dai suna da yalwan rassa da ganyanyaki kuma baƙaƙe ƙirin bishiyoyin suna da suffan mutane gasu duk sun wani lallauye gasu da a murɗe yanayin fuska,baki,hanci,ido da kuma baki a wangale tsoro mai tsanani ya kuma lullube Aminu ya tashi da sauri ya fara tafiya yana sassarfa yana kuma nausawa cikin dajin wani kallan itatuwan ya kuma cigaba da yin karo da shi wasu itatuwan sunyi kalan tausayi wasu kalan dariya wasu kalan sarauta,wasu kalan jarumai,wasu kamar sun rungume ƴaƴa ahannun su,wasu kuma kuka suke harda wani irin ruwa na fitowa daga inda yayi kama da ido Aminu ya yawatu cikin dajin saida ya gaji sannan yasamu kan wani dutsi ya raƙuɓe ya zauna yana jiran tsammani hardai yanzu ko ruwa baisa abakin ba kuma ga yunwa na ƙwakulan sa harya fara cire rai ya kuma tsinke da gurin ga tsoro ga shi ya kasa tuna komai.

Kamar daga sama yaji alamar ƙarar wani abunda baisan ko meye ba ahankali ya tashi cikin tsoro ya fara bin inda yakejin wannan sautin na fita yayi tafiya mai tsayi sosai sannan ya kawo gun tunda ga nesa yake ganin haske gun ashe ruwa ne ke gangarowa ta jikin wani dutse mai tsayin gaske wanda yayi wa dajin ƙawanya.

Aminu jiki na ɓari ƙarasa gun ya taka wani dutse ya hau ya wanke hannu yayi bismillah ya sha ruwan yayi alwala duk da baisan inane gabas ba ya daiyi sallah kuma ya roƙi Allah da ya fitar da shi daga cikin wannan dajin ɗaga kansa sama sai ya tuna da Allah shi kaɗai zai fitar da shi daga cikin wannan tashin hankalin ya ɗaga kai sama saiya tuna da Allah shi kaɗai zaifitar da shi daga cikin wannan tashin hankali ya ɗaga hannu sama yayi addu'a na shafa afuska na Allah maji roƙon bawa.......

Taku Har Kullum👱🏼‍♀

Muna Mugun Tare🤝

_*Star Nucee36O*_✨💫

RASHIN SANI NE SILA(Complete)  Where stories live. Discover now