Page 31-35

61 4 0
                                    

👺👺👺
👺 👺
👺
🏵❄🏵❄🏵❄🏵
*RASHIN SANI NE SILA.....*
❄🏵❄🏵❄🏵❄
👹👹👹
👹 👹
👹

*A TRUE LIFE STORY*

*By*

*Nusaiba i Usman Z.S*

'''SADAUKARWA GAREKU'''

_*NAFEESAT YUSUF*_
Feenah baby
_*SUWAIBA.U.ADAM'S*_
Subie
_*ZEEBNAB YAƘASAI*_
Queen
_*AYUSHA ILIASU*_
Queen
_*ANTY QUEENMERMUE*_

*_Wattpad StarNucee360_*

3⃣1⃣➡3⃣5⃣

Habib ya nisa sannan ya jefo masa tambaya yace

"To mai yake hanaka zuwa Makaranta kullum kamar yadda ka Sabah? "

Tambayar tazo ma Aminu a bazata don haka sai kawai ya bashi amsa kai tsaye da cewa

"Na gaya maku mashin d'inne take bani matsala kwana biyu nan "

Harya k'osa da tambayoyin da suka titsiye shi suna jifan sa da su, sai kace wasu iyayen sa, ko wasu y'an jarida, tashi yayi tsam daga gunda yake zaune yace masu

"Toni zan wuce gida saduwar Alkhairi ya wuce yaje ya buga mashin d'insa yayi gaba abin sa yayi gida.

Su Habib suman zaune sukayi domin yau abokin nasu ya shayar dasu mamakin sa kwarai da gaske, hakanan suka tashi da mamakin abun da yayi masu, suna maida yadda akayi, suka watse.

Abufa sai gaba-gaba yake k'ara ma Aminu kusan kulluma sai yazo tahiya makaranta sai mashin tai masa lalata tak'i tashi, in kuma ya samu yaje makarantar kwata-kwata bai fahimtar komai game da karatun sa koman yaya zaiyi ya k'ok'arta abun taci tura.

*_BAYAN WASU WATANNI_*

A kwan a tashi inji Hausawa sukace asarar mai rai, Sannu-sannu kuma bata hana zuwa sai dai a dad'e ba'aje ba

Ayau ne su Aminu zasu fara Final Exams d'in su d'alibai duk hankali a tashe, wad'anda suka yarda da kansu su ko a jikin su, su Habib sai raba idanu sukeyi suga abokin nasu amma shiru, sune k'arshen shiga Hall d'in, jiki duk babu lakka domin sun tsinke da lamarin Aminu, suna shiga suka fara nasu jarabawar.

Buga Mashin d'in yakeyi babu k'ak'k'autawa amma abun yaci tura domin ko alamar tashi bata da niyya

Inna na daga cikin d'akin ta, taji mashin d'in tak'i tashi yasa ta fitowa, ta kalli d'an nata cikin tausayawa domin yau mashin d'in ta wahalar dashi kwarai da gaske tace

"Dan nan wai haryanzu mashin d'in tak'i tashi ne? "

Aminu ya d'ago ya kalli Mahaifiyar tasa ya bata amsa da cewa

"Eh wallahi inna nayi-nayi abun yak'i ko kad'an "

Inna ta nisa sannan ta d'aura da cewa

"Kuma kace yau zaku fara jarabawa ko? "

Aminu ya bata amsa da

"Eh Inna gashi yanzu har an kusa shiga "

'Daki Inna ta koma ta d'aga bankad'en matashinta ta d'auko 200 ta fito taje ta mik'a masa tace

"Wannan ai zai kaika ya dawo da kai ko? "

Aminu yace

"Eh Inna nagode kwarai "

Inna ta amsa da

"To maza kaje kada ka makara sosai "

Ya amsa da

"To Inna "

Da sassarfa ya fita daga gidan yayi sa'an samun d'an mashin ya kawo fasinja ya tsaida shi sukayi ciniki zai kai shi har cikin ABU akan 100 sannan ya hau suka wuce, suna isa ya mik'a wa mai mashin hakkin sa ya shike da sauri.

Da gudu Aminu ya shigo Hall d'in yaje ya karb'i Question paper da Answer sheet ya samu wajen zama ya zauna ya fara rubutu, Sunan sa da exams Card No kawai ya iya rubutawa kamar jira ake ya ida, sai ga wannan hayak'i daya saba rufe masa takarta yazo yayi k'ok'arin, k'ok'artawa ya samu ya tabuka wani abun amma hakan ya faskara, abun yaci tura, a tak'aice bai samu yayi komai ba, ahaka yaje ya kai ya fito.

Su Aliyu suna ta dakin fitowar sa don suji lafiya, yana ko suka fara tambayar shi dalilin zuwan sa latti,Bashir yace

"Wai haryanzu baza ka canza ba friend? Yanzu time d'in wasa fa ya wuce, mu fuskanci abundake gaban mu wannan jarabawar itace ta k'arshe fa, plss and plss kabar irin haka "

Aliyu ya karbe zancen da cewa

"Ni Wallahi nazata ma bazai zo bane ba, domin na shiga Hall dinnan amma hankali na baya tare da ni, kacokan yana gurin tunanin sa gashi ba halin kiran waya ballantana muji halin dayake ciki "

Habib ya yalle su baki d'aya ya nisa sannan yace

"Ni nasan ba abun da zai hanasa zuwa zana jarabawar nan sai dai in mutuwa ko tsananin rashin lahiyar da hankalin sa ya gushe, bai san inda kansa yake ba, Allah shi kyauta "

Kallon Aminu Habib yayi ya auno masa tambaya da cewa

"Kodai yauma mashin dince ta lalace maka a hanya?

Aminu da duk yama rasa ta cewa, nisawa yayi ya sanya hannun sa biyu ya shafa kansa ya furzar da wata zazzafar iska, sannan ya gaya masu yadda akayi,jajanta masa sukayi.

Sannan suka tashi suka shiga paper ta gaba, bayan tilawar karatun sa sukayi

Wannan karan sammakal kamar d'azu bai iya tab'uka komai ba daga exams no sai sunan sa kawai ya iya rubutawa, ahaka ya kuma kaiwa ya fita Hall d'in abin naci masa rai kwaran gaske amma bashi da tayi

Ahaka su Bashir suka cimmasa Aliyu yace

"Kaga gurayen aji sabo da tsabagen kariga da ka gama bige wannan paper ana shiga ka farfasa ta kai fitowar ka oh mazaje kenan "

Ya bashi hannu suka tafa

Habib yace

"Kasan wanda yariga da yasan hannun sa, to wanna b'ata lokaci zaiyi, kawai Baba cigaba da ba maza kashi kanabi ta kansu kana tattakewa haka muke so.

Aminu dai sai buga masu yak'e yake yi, irin yak'en baza ku gane ba Maza, na ciki na ciki.

A ranar dai sanda suka rubuta paper uku.

*_BAYAN SATI 'DAYA_*

_Vote_
_Comments_
_Share_
_And Follow_

*Muna Mugun Tare*🤝

*Taku Har Kullum*👱🏼‍♀

*_Star Nucee36O_*✨💫

RASHIN SANI NE SILA(Complete)  Where stories live. Discover now