Page 51-55

46 3 0
                                    

👺👺👺
👺 👺
👺
🏵❄🏵❄🏵❄🏵
*RASHIN SANI NE SILA.....*
❄🏵❄🏵❄🏵❄
👹👹👹
👹 👹
👹

*A TRUE LIFE STORY*

*By*

*Nusaiba i Usman Z.S*

'''SADAUKARWA GAREKU'''

_*NAFEESAT YUSUF*_
Feenah baby
_*SUWAIBA.U.ADAM'S*_
Subie
_*ZEEBNAB YAƘASAI*_
Queen
_*AYUSHA ILIASU*_
Queen
_*ANTY QUEENMERMUE*_

*_Wattpad StarNucee360_*

5️⃣1️⃣➡️5️⃣5️⃣

  Tun shigar sa ABU ya had'u da su Habib shi da D.E ya shigo don haka suna 200level yazo suna zaman amana da k'aunar junan su sosai suna maida hankali gurin karatun su, mafarin rashin shirin Aminu da Aliyu shine rashin maida hankali da Aliyu bayayi akaratunsa hakan yasa yayi ta masa nasiha da bashi shawara amma nasihar da shawarar bai d'auka sai ya koma masa da tsiya mafarin rashin shirin nasu kenan yanzu suna shekarar k'arshe wannan iftila'in ya fad'a ma Aminu

*** ******* ***

   Ficewar Aminu daga d'akin Mahaifin nasa keda wuya ya bar gidan ya fita ko zai samu sa'ida.

       Zaune yake bakin rafi yana jifa duwatsu cikin wani d'an rami dake kusa da rafin yana tunane-tunane kamar ance ya d'aga kai ya hangi wata budur wa  d'auke da tulu akai tayi hanyar cikin gari tana tafe cike da natsuwa, tsintar kansa yayi da mik'ewa ya bi bayan ta duka sukai cikin gari haryaga gidan da ta shiga, daganan sai shi kuma ya juya ya koma gida, ya shige d'akin sa yana jiran dare yayi.

  Yana idar da sallar isha'i  ko takan abinci bai biba ya kama hanyar gidan, tun daga nesa ya hangi yaro zaune bisa dakali a k'ofar gidan yana y'an kalle-kallen sa da isar sa, Aminu ya kalli yaron yace "d'an Samari " yaron ya kalle sa ya bushe da dariya yace"ni fa ba Saurayi bane, ni yaro ne irin su Yaya Nazifi ne ake ce masu Samari "dariya zancen tabaiwa Aminu ya ko dara sannan yace "ai kaima ka kai akiraka da Saurayi Yaron akwai son girma, cen sai ya d'aga kai alamar tunani, da ido Aminu ya bishi da kallo Yaron ya kalle shi ya ce "Yaya wane ma? "Aminu murmushi yayi domin Yaron ya burge sa sannan ya bashi amsa da  cewa "Aminu "  Yaron yace"yawwa Yaya Aminu to mu gaisa" Aminu ya mik'a masa hannu suka gaisa Aminu yace "to kai yaya sunan ka? " Yaron yace Zulkifilu

Ganin shirmen Zulkifilu bamai k'arewa bane sai Aminu ya tari numfashin sa da jefa masa tambaya yace

"yaya sunan yayar ka? "

Zulkifilu yace "Aunty Nuriyya"

suna mai dad'i Aminu ya aiyana hakan azuciyar sa sannan ya kuma jefo ma Zulkifilu wata tambayar

"ita kadai ce Babban Mace agidan? "

Kai Zulkifilu ya d'aga masa alamar eh

"Yawwa" yace

"Ana zuwa nemanta ta fito? "

"Eh ana zuwa amma batason fitowa"Zulkifilu ya bashi amsa

"To ni yanzu in ka kirata zata fito? "

Zulkifilu yace "kila ta fito"

Jinjina kai Aminu yayi yane wasu y'an tunane-tunane muryar Zulkifilu ce ta katse masa tunani

"Amma Yaya kai d'an wani gida ne? "

Aminu yayi murmushi yace " ni d'an gidan Malam Muhammadu ne"

Zulkifilu yace "laaa d'an bokon nan ko, ai naji agari ana cewa kaki aure sai karatu kake yeee nima inna girma fa zanyi karatu sosai na zama mai tuk'a jirgin sama "

Aminu dariya yayi sosai sannan yace"to ka dage da karatu insha Allah zakacimma burin ka kaji? "

"To "Zulkifilu yace

  Sannan Aminu yace "maza je ka kiramin Antyn  naku, da gudu Zulkifilu ya  shige gidan yana y'an tsalle-tsallen sa

Yana shiga zauren gidan ya fara kwad'ama  ta kira

"Anty!  Anty! Anty!!

Murmushi Aminu yayi yace Yaron nada shiga rai ga surutu kamar aku murmusawa ya kuma yi jin yadda yaketa kwada mata kira(I wish mu samu yaro mai wayau kamar sa, cab tunkan ma yarinyar ta ganka harka fara wannan hasashen Aminu da k'arfin hali)

_Vote_
_Comments_
_Share_
_And Follow_

*Muna Mugun Tare*🤝

*Taku Har Kullum*👱🏼‍♀

*_Star Nucee36O_*✨💫

RASHIN SANI NE SILA(Complete)  Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang