Page 106-110

76 6 0
                                    

👺👺👺
👺 👺
👺
🏵❄🏵❄🏵❄🏵
*RASHIN SANI NE SILA.....*
❄🏵❄🏵❄🏵❄
👹👹👹
👹 👹
👹

*A TRUE LIFE STORY*

*By*

*Nusaiba i Usman Z.S*

'''SADAUKARWA GAREKU'''

_*NAFEESAT YUSUF*_
Feenah baby
_*SUWAIBA.U.ADAM'S*_
Subie
_*ZEEBNAB YAƘASAI*_
Queen
_*AYUSHA ILIASU*_
Queen
_*ANTY QUEENMERMUE*_

*_Wattpad StarNucee360_*

*''END''*

1️⃣0️⃣6️⃣➡️1️⃣1️⃣0️⃣

   Tab'e baki Nuriyya tayi sannan ta bashi amsa

"Wai dan nace sai ta gama jinga(home work) da aka bata a makaranta sannan taje gun su Inna  shine take wannan zunbure-zunburen 

Murmushi Aminu yayi sannan yace"yauwa Hussy na zonan kyale Mommy kizo muje ki gama sai ki tahi abinki kinsan Mommy ki kaifi d'aya ce bata magana biyu in kin gama sai ki tahi"

Da gudu ta zo ta rungume Abban nata ya ya lakaci hancin ta ya ce

"Oya ba Mommy ki hak'uri kada ki k'ara fushi da ita ko so kike Allah Uban gijinmu yayi fushi da ke kema "?

girgiza kai tayi taje ta duk'a a gaban Mommy tace

"Mommy don Allah kiyi hak'uri kada Allah nima yayi fushi dani"

Nuriyya d'agota tayi tana shafa kanta tace"to ki daina idan ance kiyi wani aikin kina zumbure-zumburen ko ki k'iyi ba kyau kinji na yafe maki "

Dariya Husnah tayi tana murna Mommy ta yafe mata tace "to Mommy  na gode "

Shima Aminu murmushi yayi masu domin harcikin ranshi yakejin dad'in iyalan sa

Husnah ce babban y'ar su, y'ar kimanin shekaru takwas sai y'an biyu Amir da Ammar yan kimanin shekaru 5 sai y'ar auta khairat y'ar shekara d'aya da watanni ita taci sunan Inna,

D'aki suka shiga ya d'auko sweet d'in ya baiwa kowannen su, suna ta murna suna mashi godiya, Husnah tana kammala Home work d'in ta, ta tasa k'eyar k'annan ta suka nufi gidan kakannin nasu

Suna fita Nuriyya ta d'auko ma Mijin nata Abinci ta jera masa sanan ta duk'a tace masa"sannu da zuwa ina yini ya gajiyan aiki "

Murmushi Aminu yayi ya rungumo ta yana shak'an daddad'an kamshi ta sannan ya amsa da " lahiya Alhamdulillah Matass ya hidimar gida da yara"? Da" lahiya Alhamdulillah ta amsa sai ka kammala cin abincin muje kayi wanka " Aminu ya amsa da "to" nan ya wanke hannu ya fara cin abincin data kawo masa, ita kuma tana gefe tana masa hira sama-sama harya kammala cin abincin hamdala yayi

Ya tashi yaje yayi wanka Nuriyya ta taimaka masa, yana fitowa ya shirya ta fito masa da kaya marasa nauyi ya sa ya kwanta yana hutawa,.
Nuriyya na kwance gefe tana shinfid'e khairat da tai bacci kallo takai ga Mai gidan nata cike da so da k'aunar sa tace

" Hasken k'albi na  haryanzu baka bani labarin dakace zaka ban bafa kuma abun na rai na sai jamin aji kake "?

Aminu yace "a'a ni na isa naja maki aji ai wannan aikin sai mata " Murmushi tayi domin tasan sa da zolaya nan ya fara bata labarin abun daya faru ya k'ara da cewa " damuna da kike yi na nemi aiki tunda nayi karatu, ai ban kammala ba badai wanda ya sani daga ni sai iyayena da Kaka Malam sai ke dana gaya maki yanzu ko Aminai na bawai duka abin da ya faru suka sani ba" nisawa yayi yana kallon matar tasa yadda hawaye ya wanke mata fuska

Nuriyya ta shafa gefen fuskan mijin nata tace" Allah sarki ashe kaga rayuwa " Murmushi yayi yace "ai komai ya wuce kuma na samu Abokai na gari wanda yanzu a wannan zamanin ba'a cika samun su ba su suke taimakamin

"Da ace dukka abokai haka suke suna taimakon abokansu marasa k'arfi da yanzu anfi haka duk da ba duka aka taru aka zama d'aya ba " Nuriyya tace " gaskiya kam Allah ne abun godiya Allah mun gode maka akan komai da kai mana " suka amsa da amin gaba d'ayan su.

Alhamdulillah

Tammat bi hamdulillah

  Allah na gode maka da kabani ikon kammala wannan labari.
Kuskuren da nayi Allah ya yafe mani Allah ya bamu ladar dake ciki baki d'aya

_Daraja d'an Adam_
Shi d'an Adam aduk inda yake daraga ne dashi duk inda mukaga mutum mu daraja shi domin bamusan waye shiba kuma kila wata rana zai iya mana rana

_K'addara_
Yin imani da kaddara mai kyau ko akasin haka shine cikan imanin mumini domin Allah zai iya jarabtar mu ya ga yadda zamuyi zamu iya tsallakewa ko akasin haka

Sai mun had'u a littafi na gaba mai suna *ITA WACECE ?*

_To *ITA WACECE?* d'in_🤔

_Vote_
_Comments_
_Share_
_And Follow_

*Muna Mugun Tare*🤝

*Taku Har Kullum*👱🏼‍♀

*_Star Nucee36O_*✨💫

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jul 14, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

RASHIN SANI NE SILA(Complete)  Where stories live. Discover now