Page 86-90

36 5 0
                                    

👺👺👺
👺 👺
👺
🏵❄🏵❄🏵❄🏵
*RASHIN SANI NE SILA.....*
❄🏵❄🏵❄🏵❄
👹👹👹
👹 👹
👹

*A TRUE LIFE STORY*

*By*

*Nusaiba i Usman Z.S*

'''SADAUKARWA GAREKU'''

_*NAFEESAT YUSUF*_
Feenah baby
_*SUWAIBA.U.ADAM'S*_
Subie
_*ZEEBNAB YAƘASAI*_
Queen
_*AYUSHA ILIASU*_
Queen
_*ANTY QUEENMERMUE*_

*_Wattpad StarNucee360_*

8️⃣6️⃣➡️9️⃣0️⃣

*GIDAN SU AMARYA*

  Amarya tasha kwalliya ta dawo  kamar wata Aljana don kyau StarNucee MakeUp tayi mata kwalliya tayi kyau harta gaji sai hotuna suke d'auka ana buga selfi haka suka wuni har akazo d'aukan Amarya

Amarya tunda taji tsayuwar motocin d'aukan ta taji wani mugun fad'uwar gaba ya ziyar ceta sai kuma idon ta yayi kwallah zatayi kuka nan tsofaffi suka zo suka tafi da ita gun iyaye aka mata nasiha yan uwa suma sukai nasu sannan aka wuce da ita gidan mijin ta da k'awayen ta domin ance ba mai kwana a gidan Amarya, ba haka wasu suka so ba sunso su kwana a wannan aljannar duniyar gidan domin inba a tv ba ba su taba ganin irin gidan ba sai wanda ya fita karkaran shine zaice ya ga fiye da shima.

  Abokanan Ango suka rako shi d'akin Amaryar sa suka tadda d'akin cike da k'awayen Amarya da sallama suka shiga d'akin

"Assalamu-Alaikum "

Dukka k'awayen Amaryan suka amsa

"Amin wa'alaikumussalam "
Gaggaisawa sukayi daga bisani sukayi siyan baki daga k'arshe akayi ma Amarya Da Ango addu'ar zaman lahiya da zuria d'aiyiba sannan sukayi ma Amarya da Ango sallama suka tafi suka kwashi k'awayen Amarya suka maidasu gida sannan suma suka wuce masaukin su.

Bayan tafiyar su Ango ya matso kusa da amaryar sa yace "Amarya bakya laifi " bai jira yaji mai zatace ba ya kuma cewa"ki tashi muyi alwala domin mu gode ma Allah daya nuna mana wannan rana mai Albarka damuka jima muna tsumayen zuwan smta "bayan sun idar da sallah addu'oin sosai yayi masu sannan ya je ya d'auko faranti da kofi ya ciro kazar daga leda ya aje akan farantin din ya zuba masu Hollandiyar sannan ya fara ciyar da ita shima yana ci sai da ya tabbatar da ta koshi sannan ya tattara komai ya maidashi mazaunin sa sannan ya kalli Amaryar tasa da kanta ke sunkuye  domin haryanzu bawai ta daina kukan bane tanayi kad'an-kad'an

"Amarsu Don Allah kukannan ya isa kiyi hak'uri haka ki rage kayan jikin ki ki watsa ruwa bara nima na watsa ruwa inko na dawo bakiyi ba ni zan maki"

Dariya yake k'asa-k'asa ya fita ya barmata d'akin, yana shiga d'akinsa rage kayan jikin sa yayi ya shiga bayi,  wanka yayi yana fitowa ya tsane jikinsa ya feshe jikin sa da turare mai sanyin k'amshi zura jallabiya fara sannan yajanyo d'akin ya koma d'akin Amarya

Yana fita ta tashi jiki ba kwari ta rage kayan jikin ta sannan ta zauna a bakin gado ta zabga tagumi, kamar an mintsineta ta tashi tuna abun daya ce kuma tasan zai aikata tashi tayi ta shiga bayin ta watsa ruwa sannan ta fito taje gurin wardrobe dinta ta ciro rigar bacci doguwa ja mai laushi ta sanya ta feshe jikin ta da turare sassanya sannan ta haura gado ta kwanta tayi lamoo tana tunani ga fargaba ga rashin sabo ga uwa uba kunya daya dabaibaye ta

Ahankali ya turo kofar d'akin da sallama

"Assalamu-Alaikum "

A hankali ta amsa cen k'asan mak'oshi "Amin Wa'alaikassalam "ahankali ya lallab'a ya kashe wutan d'akin sai ya lallab'a ya haye gadon ya janyo masu bargo ya rufesu

Asuba ta gari Amarya da ango Allah ya kawo zuri'a d'aiyi ba

_Vote_
_Comments_
_Share_
_And Follow_

*Muna Mugun Tare*🤝

*Taku Har Kullum*👱🏼‍♀

*_Star Nucee36O_*✨💫

RASHIN SANI NE SILA(Complete)  Where stories live. Discover now