Page 11-15

99 7 0
                                    

👺👺👺
👺 👺
👺
*RASHIN SANINE SILA.....*
👹👹👹
👹 👹
👹

*A TRUE LIFE STORY*

*By*

*Nusaiba i Usman Z.S*

*IDON MIKIYA WRITTER'S ASSO*🦅

'''SADAUKARWA GAREKU'''

_*NAFEESAT YUSUF*_
Feenah baby
_*SUWAIBA.U.ADAM'S*_
Subie
_*ZEEBNAB YAƘASAI*_
Queen
_*AYUSHA ILIASU*_
Queen
_*ANTY QUEENMERMUE*_

1⃣1⃣➡1⃣5⃣

Sukuku yayi yinin ranar bayan ya idar da Sallar isha'i ya nufi gidan su gimbiyar sa yayi sallama ta fito cikin fara'a bayan sungama gaisawa ta juya masa baya ta turbune fuska Habibin nata yariga da yasan kwanan zancen,sassautar da murya yayi ya fara bata baki da daddaɗar kalaman sa masu sanyaya zuciyar masoyiyar sa ahaka harya samo kanta sai ga Nuriyya na qyalqyala dariya kamar ba ita ta futo tana fushi ba nan suka gama hirar soyayyar su yayi mata sallama saida ya tabbatar ta shige gida sannan ya tafi sunata kewar junan su yana isa gidan ya rufe yaje ɗaki ya kwanta.

Akwana atashi ba wuya agun Allah yanzu komai ya wuce Aminu har wata yar ƙiba yayi ga wata muguwar shaƙuwa da fahimta da ta ƙara shiga tsakanin Nuriyya da Aminu yauma sune zaune bakin rafi ga yara nan nata ɗiban ruwa suna wasa Aminu ya ɗauki dutsi ya jefa cikin rafi,rafin na bada wani sauti mai daɗi da sanya nishaɗi Aminu ya juyo daga kallon rafin ya kalli Nuriyya wacce ta shagaltu da kallon ruwan da ya taru a gefe ƙananun gwadayi sai fareti sukeyi"yau bazakimin hirar soyayyar mu bane"tai murmushi batare da ta kalle shi ba ta ce"ai taren nan da muke yafi labarin da zan baka"Aminu yayi murmushi ya ce"toni bara nabaki tunda ke kinƙi bani"tai murmushi kawai nan ya fara bata labaru masu ɗaɗi da sa shauƙi nan da nan itama ta zage tana maida masa cikin sassanyar muryar, mai kashe masa jiki hira sosai sukayi don basu ankaraba saji sukai ana kiran Sallar la'asar cikin azama suka yunƙura daga gun suka gangara ƙasan rafi sukai alwala yaran dake gunma sukai alwala suka biyo su suka gabatar da Sallah Aminu yaja su suna idarwa yaran suka koma gun wasan su Aminu da masoyiyar sa Nuriyya nan suka kuma buɗe wani babin hirar soyayyar suka cigaba,basu suka bar bakin rafi ba sai biyar saura nan ma don Nuriyya zataje ta taya mama girki shiyasa suka tahi saida ya kaita har ƙofar gidan su nanma saida suka ɗan taɓa hira kafin yabarta ta shiga gida ƙarfe 5:17 biyar da minti sha baƙwai, da sallama ta shiga gida ƙannen ta ta fara cin karo da su suna wasa duk suka taso sukai mata sannu da zuwa sannan suka koma gun wasansu madafi(kitchen)ta nufa inda ta tarar da mama hartayi talge ta gaida ta ba yabo ba fallasa mama ta amsa ta, ta ce"sarauniyar soyayya sai yanzu kika rabu da shi yara kamar cingam to dai zan sanar da mahaifinki ya samu baban nasa suyi magana mu kauda ke kowa ya huta da wannan naci"ita dai Nuriyya bata da bakin magana saima ƙara sadda kanta ƙasa datayi tana wasa da bazar ɗin mayafin da taci ɗammara ɗashi a ƙugunta mama ta ce " maza tashi kije ki daka daddawa da kayan miya ki ɗaura miya kinsan mahaifinki bayason girkin dare"Nuriyya ta amsa to ta, tashi don gabatar da aikin da maman ta ta sata taje ta ɗauki daddawa guda biyu ta karkaɗe turmin da taɓarya sannan ta saka daddawan ta daka bayan ta gama ta ɗebo ruwa a roba ta cire hancin busashshen tattasai da harkono ta zuba tare da barkonon sannan tafara dakawa yana dakuwa ta kwashe ta ɗauko tukunya ta zuba man naira ashirin ta kunna murhun ta ɗaura tukunyar,manjan nayin zafi ta zuba dakan da tayi ta ɗan rufe kaɗan murfi,ta dawo kuma ta daka albasa ta kuma zubawa sannan ta ɗauko wake dai dai buƙatar ta ta daka ta haɗa ta soya yana soyuwa ta ɗebo ruwa dai dai buƙata ta zuba ta tsaida ruwan miyan ta barshi harya tafasu ta zuba sinadarin d'and'ano da farin magi da gishiri suma dai dai kasancewar miyar kuɓewa ba'asa mata tumatur domin yana hanata yauƙi miya,sai ƙamshi ke tashi saida ta tabbatar da ya nuna sannan ta kaɗa ba jimawa ta sauke ta zuba a madaidaicin roba ta ɗauka takai ma'ajiyar sa wato kusa da kwanukan tuwo.

Anata kiraye kirayen sallar mangariba ta ɗauro alwala ta wuce ɗaki ta gabatar da sallah tana idarwa bayan tayi adduo'in ta,tashi ta kwaso kwanukan tazo tafara kason abinci tana gamawa dai dai lokacin ƙannan ta da mahaifin ta suka dawo gida daga masallaci tai ma baban ta sannu da zuwa sannan ta kawo masa abinci da ruwan randa,albarka ya shiga sa mata da dukkan ƴaƴan sa(harda ku readers)itama Nuriyya ta koma ta ɗauki nata don tariga da tamika wa mama nata sannan itama ta koma gefe taima kanta mazauni ta fara cin nata abincin suna gamawa ana fara kiran sallar isha'i nan duk mazan suka rankaya masallaci baba ya tasa ƙeyar su,suma matan suka tashi suka ɗaura alwala sukaje sukai sallah suna idar wa suka fito tsakar gida suka dasa hira kasancewar duk dare sai sun baje a tsakar gida sunyi hira ƴaƴan da iyayen su yau sunsha hira sosai domin dare yayi sosai sannan suka tashi kowa yayi ɗakin sa sukai wa juna saida safe.…

Nima sai ince asuba ta gari.

Aminu na barin k'ofar gidan su Nuriyya gona ya wuce domin yin zagaye sai yan ciyayin da yayi yawa ya tsaya yana ciccire su abunda ya sa har ya d'ad'e a gonar kenan ana kiran sallar magariba yayi daidai da lokacin da ya k'araso cikin gari don haka baiyi wata wata ba ya wuce masallaci yana zuwa yayi alwala yaje yabi jam'i bayan sun idar nan ya tsaya masallacin ya fara karatun alqur'ani har zuwa lokacin da aka kira sallar isha'i sannan ya kama hanyar gida ya shiga ba kowa a tsakar gidan d'akin inna ya tunkara ya shiga da sallama ya tadda ita kan sallaya tana addu'oi nan ya zauna ya jirata saida ta ida suka shafa tare, tare da cewa amin sannu da niyya, gaisheta yayi cikin fara'a ta amsa masa tace" yau ina ka wuni baka gida kamar tun safe ka fita? "nok'e kai yayi ya kuma sadda kai k'asa murmushi tayi domin tagane inda ya dosa ta kuma cewa "kodai gun mutuniyar kaje? "murmushi yayi bai dai ce komai ba, "kaidai da wannan surukar tawa baku da dama Allah ya kaimu lokacin musha bidiri"dayake inna akwaita da barkwanci yadda ta maida d'anta kamar jikan ta amma bata d'aukan raini hira sukeyi sosai sannan ta bashi abincin sa nan yaci, saida safe yayi wa mahaifiyar sa ya wuce d'aki yayi shirin kwanciya, ya kwanta....

*DA SAURAN RINA AKABA...*

*BAYAN WASU KWANAKI*

*Muna Mugun Tare*🤝

*Taku Har Kullum*👱🏼‍♀

*Star Nucee36O*✨💫

RASHIN SANI NE SILA(Complete)  Where stories live. Discover now