Page 16-20

84 5 0
                                    

👺👺👺
👺 👺
👺
*RASHIN SANINE SILA.....*
👹👹👹
👹 👹
👹

*A TRUE LIFE STORY*

*By*

*Nusaiba i Usman Z.S*

*IDON MIKIYA WRITTER'S ASSO*🦅

'''SADAUKARWA GAREKU'''

_*NAFEESAT YUSUF*_
Feenah baby
_*SUWAIBA.U.ADAM'S*_
Subie
_*ZEEBNAB YAƘASAI*_
Queen
_*AYUSHA ILIASU*_
Queen
_*ANTY QUEENMERMUE*_

1⃣6⃣➡2⃣0⃣

*DA SAURAN RINA AKABA...*

BAYAN KWANKI

Kwance Aminu yake yana sharar barcinsa hankali kwance sai minshari yake da juyi, kamar daga sama yaji wasu irin abu na tsikarar sa ajiki yayi k'ok'arin ci gaba da barci amma hakan ya faskara saboda k'ayk'ayin da yafaraji ajikin sa ahankali ya fara shafa ta inda yakejin k'ayk'ayin saiyaji kamar ciyawa ya kuma shafawa still ya kumajin bafa katifa bace ciyawace cikin magagin barci wanda hankalin sa bai gama dawowa jikinsa ba ya bud'e idon sa taurari ya gani wanda suka k'awata sararin samaniya gunin sha'awa ahankali yake kalle kalle wata ya hango tana masa murmushi fuskar da bazai tab'a mantawa a rayuwar sa ba.
K'ara murza ido yayi kuma kallon watan saiyaga wannan fuskar daya fara gani ta b'ace.

_sai kuma ya fara tunanin shi dayake d'aki akwance to mai yakawo taurari da wata a saman d'akin sa?_

_To ko saman kwanon ya yaye ne?_

_To kuma ai ba iska ake ba da zai yaya?_

Saida hankalinsa ya gama dawowa jikin sa sannan ya fahimci a waje ya ke kuma cikin juji afirgice ya mik'e ya fara kalle kalle sannan ya gane a bayan gari yake a sukwane ya falfala cikin gari ba kowa sai koke koken karnuka da kukan kwad'i da gyare gudu yake don ji yake kamar binsa ake, saboda gudu k'afarsa kamar zata tab'o k'eyar sa k'ofar gidan su ya tunkara gadan gadan abunka da mai jini a jika kuma yanzu yake tashen k'arfi bugu d'aya yayi ma k'ofar ta b'alle baibi ta kan k'ofar ba yayi cikin gida d'akin sa ya koma yana shiga ya rufe ya koma cen k'uryan d'aki ya manne da jikin bango yana ta maida numfashi, zuciyar sa sai bugawa take da sauri sauri sai kalle kalle yake ga mugun tsoron daya diran masa duk k'una ficin barci da kuma akecewa barci b'arawo to dai wannan karan bashi da muhalli anan don ko ta gunsa ma bai tunkaro ba adai tsorace yake har aka kira sallar farko ya tashi ya nufi masallaci bayan sun ida sallar gari ya waye ya tashi yayi hangar gida a hanyar sa ta dawowa gida yake tunanin zuci.

_Ohni Aminu aini inasha komai ya wuce ce ne ashe akwai sauran rina akaba dole na sanar da mahaifiya ta wannan al'amari domin duk duniya bani da mai sharemin hawaye sai ita kuma bani da abokiyar shawara sai ita gashi kuma bana son hankalinta ya tashi shiyasa wancen lokacin na k'i sanar da ita komai akan abunda ya faru ya sauke ajiyar zuciya hmmmm! to amma bani da zab'i face sanar da ita halinda na shiga da wannan tunanin na shiga gida_

Da sallamar sa tsakar gidan ba kowa ya kuma wani sallamar akaro na biyu,
_Assalamu Alaikum_
Daga cen cikin d'aki ya tsinkayo muryar mahaifiyar tasa don haka tsaye d'akin, ya shiga ya tadda ita tana kishingid'e gaisheta yayi cikin fara'a ta amsa shi yanayin sa da fuskar sa ya sanar da ita da matsala cikin kulawa ta kuma kallon sa ta ce d'annan maiya faru _k'asancewar d'an fari ba kiran sunan sa y'an karkara suke ba da wasu yan cikin gari sai dai kaji sunce(D'annan, kai,kee kana Ina ko kina Ina dadai saran su)_ sanda kai k'asa yayi yace"inna wata matsala take tafe dani"muskutawa tayi tace"ina jinka Allah yasa mai sauk'i ce fad'i ina jinka duk da kunyar da inna ke kwada ma Aminu kasancewar shi d'an fari yau ta kau, tunda taji ya ambaci matsala hankalinta gaba d'aya ta maida kansa.

Inda yabata labarin sanda ya b'ace da inda ya tsinci kansa da kuma irin abubuwan da yagani sannan ya gangaro zuwa inda ya tsinci kansa jiya, nisawa inna tayi ta kalli Aminu da mugun tausayawa ta jinjina kai tace"gaskiya kaga iftila'i amma kai katab'a yi ma wani ko wata wani rashin k'yautawa ne kaga mutum daraja ne da shi nan da kake gani in kasan waye wani baka san wane wani ba domin akan samu wad'and'a ba mutane ba kuma kuyi ta hurd'a dasu batare da kasani ba, shiyasa aduk inda ka tsinci kanka kada kazama mai wulak'anta mutane domin bakasan na gari ba kuma baka san mugu ba.

Shiyasa duk inda kake kazama mai haba haba da mutane banda wulakanci Aminu yace"haka kikemin nasiha inna kuma ina k'ok'arin kiyayewa.

Inna ta ce to yanzu gayamin akwai abunda ya tab'a had'a ka da wani ko wata fad'ane acikin garinnan ko makaranta?,Aminu yace"eh to inna gaskiya natab'a samun matsala da wata 'Yar makarantar mu kuma 'Yar ajinmu abunda yafaru ko shine.

*FLASH BACK*

Zaune suke cikin *Biology Department*Garden na Ahmadu Bello University Zaria, gurin akwai dogayen itatuwa sunyi masa k'awanya kamar rumfa ga gurin da d'an duhu kujeru ne agun irin na d'alibai(student)na k'arfe an kakkafa su.....

*Muna Mugun Tare*🤝

*Take Har Kullum*👱🏼‍♀

*Star Nucee36O*✨💫

RASHIN SANI NE SILA(Complete)  Donde viven las historias. Descúbrelo ahora