Page 26-30

66 5 0
                                    

👺👺👺
👺 👺
👺
🏵❄🏵❄🏵❄🏵
*RASHIN SANI NE SILA.....*
❄🏵❄🏵❄🏵❄
👹👹👹
👹 👹
👹

*A TRUE LIFE STORY*

*By*

*Nusaiba i Usman Z.S*

'''SADAUKARWA GAREKU'''

_*NAFEESAT YUSUF*_
Feenah baby
_*SUWAIBA.U.ADAM'S*_
Subie
_*ZEEBNAB YAƘASAI*_
Queen
_*AYUSHA ILIASU*_
Queen
_*ANTY QUEENMERMUE*_

*_Wattpad StarNucee360_*

*Ina mai baiwa mabiya wannan littafi hakuri da jinshi shiru da kukayi na tsahon lokaci, amma daga yanzu har k'arshe insha Allah zaku sameshi ba mushkila, Ngd kwarai da kulawar ku.*

2⃣6⃣➡3⃣0⃣

*_WASHE GARI_*

Tunda yayi sallar asuba yafara shiri sabo da tazarar dayake tsakanin Mahuta da Samaru, gama goge mashin d'in kenan yaga fitowa Inna ya k'arasa kusa da ita ya rusuna ya gaishe da ita yace

"Inna kwallafiya "

cikin sakin fuska ta amsa da

"Lahiya lau da fatan katashin lahiya "

Ya amsa da

"Lahiya Alhamdulillah inna ta "

Sannan ya d'aura da cewa

"Inna ni nayi harama zan tafi makaranta, Inna tai masa addu'a kamar kullum sukai sallama ya kama hanya.

*_Ahmadu Bello University_*

Da isan sa kai tsaye ya nufi Hall d'in da zasuyi darasi, ya kafe babur d'insa ya kulle ya nufin bakin Hall d'in in da sauran d'alibai y'an uwansa suke, da isan sa ya tadda su Habib agun gaisawa sukayi irin tasu ta samari, sukayi musabaha suka d'an tab'a hira sannan suka shiga Hall domin d'aukan darasi, amma Malamin bai shigo da wuri ba sai 7:13am ya shigo.

Bada b'ata lokaci ba ya fara gabatar da darasin da zasuyi da topic din da zasu tattauna akai, nan yafara masu bayani dalla-dalla kamar yadda ya saba, kowa najin dad'in yadda yake fahimtar da su.

Aminu dai tunda Malamin ya shigo suka gaishe shi bai k'ara sanin abunda suke tattaunawa ba, sai dai yaga bakin Malamin da na d'aliban suna motsawa, sai dai yaji suna wani irin magana kamar an kunna radio batai tangaras ba, sai da Malamin yayi masu sallama suka fita bada jimawa ba sannan ya fara fahimtar maganganun su.

Fitar su bada jimawa ba, suka kuma komawa wani darasin.

Aminu dai kasa magana yayi don ya rasa maike damun sa, bai kuma k'ara tsinkewa ba sai da yaga sun shiga aji sun fara darasi kamar d'azu, tunda suka gaishe da Malamin bai kuma fahimtar abun da Malamin ke cewa ba sai da yaga Malamin ya rubuta Test a allo da Questions sannan ya gane, test za'a masu ya yago takardar da zaiyi rubutu akai, y fiddo alk'alamin sa ya d'aura bisa takardar zai fara rubutun wani abun mamaki sai kawai yaga hayak'i baya iya ganin mai yake rubutawa, yayi-yayi amma bai iya tab'uka komai ba ya kulle idanun sa ya murza su sosai sannan ya bude amma sammakal duk d'aya, yayi-yayi-yayi amma haryanzu hayakinnan ne dai yake gani, babu yadda ya iya duk son sa da rubuta test d'in haka nan ya hak'ura, ganin baiyi komai ba yasa Habib yi masa test d'in yana gamawa yaje ya kai sannan ya dawo suka fito daga d'akin karatun.

Da fitowar su basu wani tsaya hira ba kasancewar yamma tayi, sallama suka yi kowa ya kama gaban sa.

*_BAYAN WASU KWANAKI_*

"Aminu wai mai yake damun Kane cikin kwanaki biyun nan ne duk fa kabi ka canza ko makarantar ba kullum kake zuwa ba in mun tambaye ka amsa d'aya kake bamu ".

Nisawa Bashir yayi cikin zafin rai ya d'aura da cewa

"Wai mai kakeson ka maida mune inda wanda yasan waye kai to bayan mune shekara d'ay-d'ay-d'ay har shekaru uku da watanni muna tare bakai mana haka ba sai yanzu da muka kusa kammala karatun mu ".

Habib ya cafe zancen da cewa

"Yanzu gaba d'aya bakason maida hankali a karatun ka gaba d'aya ka susuce duk kayi yaushi akan rashin maida hankali a karatu shiyasa bakwa shiri da Aliyu ada amma yanzu kai kakeyin hakan da kanka ".

Aminu binsu da kallo kawai yakeyi, cikin kallon nikad'ai nasan halin da nake ciki, ya jima yana kallon su ba tare daya basu amsa ba, har sun fara k'uluwa da irin kallon da yake masu ba tare daya basu amsar ba sannan ya nisa cikin sanyi ya fara magana yace masu

"Ku tayani da addu'a nima bansan maike damuna ba ne, addu'ar ku ita ce zata nunamin abotar mu ta gaskiya ce "

Binsa da na mujiya sukayi, cikin tunanin anya wannan kansa babu motsi kuwa ".

Aliyu ne yayi k'arfin halin cewa

"Bamu gane ba to maike damun ka da zakace hakan, ya kamata kaje Asibiti a duba ka, yanzu ma ka tashi mu raka ka Asibitin cikin makaranta su duba ka "

Murmushin k'arfin hali Aminu yayi, irin murmushin bazaku gane ba yace

"Bafa komai ".

Habib ya nisa sannan ya jefo masa tambaya yace

"To mai yake hanaka zuwa Makaranta kullum kamar yadda ka sabah? ".

_Vote_
_Comments_
_Share_
_And Follow_

*Muna Mugun Tare*🤝

*Taku Har Kullum*👱🏼‍♀

*_Star Nucee36O_*✨💫

RASHIN SANI NE SILA(Complete)  Where stories live. Discover now