Page 56-60

28 4 0
                                    

👺👺👺
👺 👺
👺
🏵❄🏵❄🏵❄🏵
*RASHIN SANI NE SILA.....*
❄🏵❄🏵❄🏵❄
👹👹👹
👹 👹
👹

*A TRUE LIFE STORY*

*By*

*Nusaiba i Usman Z.S*

'''SADAUKARWA GAREKU'''

_*NAFEESAT YUSUF*_
Feenah baby
_*SUWAIBA.U.ADAM'S*_
Subie
_*ZEEBNAB YAƘASAI*_
Queen
_*AYUSHA ILIASU*_
Queen
_*ANTY QUEENMERMUE*_

*_Wattpad StarNucee360_*

5️⃣6️⃣➡️6️⃣0️⃣

"Anty ana kiranki awaje" turbune fuska tayi tace "waye? " Zulkifilu ya bata amsa da cewa "wannan d'an bokon na nan garin "yamutsa fuska tayi ta kuma cewa "waye shi? "

Zulkifilu yace"d'an gidan Baba Malam Muhammadu "

Ta kuma kallon k'anin nata tana mai nuna kanta da y'ar yatsar ta tace "ni kuwa? "

Zulkifilu yace "eh ke yace na kira masa"

Iyayen ta dasuke gefe suna sauraran su basu tanka ba

Share sa tayi taci gaba da cin tuwon ta, Zulkifilu kuma bai daina damunta da ta tashi taje ba

Mahaifinta ne yayai gyaran murya ya ce "haba y'ar nan" ta d'ago kanta daga inda take yace " to tashi kije mana muka sani ko Alkhairi ke tafe dashi, ina fa lura dake duk wanda yayi Sallama dake kin fita kike "

Inna ce ta karb'e zancen da cewa "to banda abunki in baki fita ba, so kike mu tasaki a gaba miyita gwada tsayi dake akasa gane wacece y'ar wacece uwar, in ba ankalli fuska ba" taci gaba da cewa "ko so kike muyi ta zama muna kallon ki, ke ba abun adon d'aki ko gida ba, yadda kowa ya keso kuma ya bar gidan iyayen sa, kema haka zaki bar gidan naki Baban maza tashi! "cikin daga murya Inna ta karisa maganar

Sum-sum-sum ta tashi kamar munafuka ta wanke hannu ta fita

Aminu na daga nesa ya hango tahowar nata, wani sassanyar ajiyar Zuciya ya sauke kasancewar akwai wutar nepa

Sallama tayi mashi

"Assalamu-Alaikum "

Amsawa yayi yana washe hakwara "Amenwa alaikissalam "

Fuskannan nata ba annuri sosai gaisheshi tayi

"Ina yini "

Ya amsa "yahiya Alhamdulillah ya gida da mutan gidan "

Ta amsa da" duk suna lahiya"

Aminu sai washe baki yake yana cikin shauki dake fizgan sa (abunka da ba sabamba), gabatar da kansa yayi agare ta

"Nidai Sunana Aminu Muhammadu Mahmoud, ni dan gidan Malam Muhammadu ne, Ma narzayo gurinki da k'ok'on barata da fatan zakiyimin duba na alkhairi ki dubani ni maraya ne a fagen soyayya ki dubi maraicina ki karbi soyayya ta, kece fitilar zuciya ta ki taimaka ki barni na zama, _kansilar karamar hukumar birnin zuciyar ki_ indai kika bani ni kuma insha Allah zanyi kokarin yin Adalci na rikeshi da amana"

Yadda ya marairaice yayi maganar sai hakan yaba ta dariya ta ko dara a zuciyar ta amma duk da haka bata saki fuska ba,domin da kyar take amsa sa shi har ya k'araci maganar sa yayi kid'an sa yayi rawar sa shi d'aya sannan yayi mata sallama,

"To ni zan tafi domin nasan sai kinyi tunani da fatan inkiyi tunani zan samu amsa mai dad'i "

Yamutsa fuska tayi sanna tace

"Sai da safe Nagode"

Abun kawai da ta iya fadi kenan ta juya ta shige gida cike da tunani irin maganganun sa masu ratsa zuciya

Aminu tafe yana tunanin zuci 'har ga Allah naji dad'in fitowar ta har kuma ta tsaya ta saurare ni insha Allah zanci nasara indai na samu nasara ah', haka dai yaci gaba da zacen zuci harya isa gida Zuciyar sa fal da tunane-tunane ko abincin dare bai iya ciba haka ya kwana cikin tunanin da neman mafita ta yadda zai shawo kanta

Washe Gari

Tundaga ranar Aminu yaci gaba dayi ma kansa kanfe har da Zulkifilu na taya sa da kyar yasamu ta bada kai bori ya hau, amma fa ta gara sa

Yanzu sun dawo sun dinke ba mai jin kansu burge y'an k'auyen suke sosai.

_Vote_
_Comments_
_Share_
_And Follow_

*Muna Mugun Tare*🤝

*Taku Har Kullum*👱🏼‍♀

*_Star Nucee36O_*✨💫

RASHIN SANI NE SILA(Complete)  Where stories live. Discover now