Page 21-25

82 4 0
                                    

👺👺👺
👺 👺
👺
*RASHIN SANINE SILA.....*
👹👹👹
👹 👹
👹

*A TRUE LIFE STORY*

*By*

*Nusaiba i Usman Z.S*

*IDON MIKIYA WRITTER'S ASSO*🦅

'''SADAUKARWA GAREKU'''
_*NAFEESAT YUSUF*_
Feenah baby
_*SUWAIBA.U.ADAM'S*_
Subie
_*ZEEBNAB YAƘASAI*_
Queen
_*AYUSHA ILIASU*_
Queen
_*ANTY QUEENMERMUE*_

2⃣1⃣➡2⃣5⃣

*FLASH BACK*

Zaune suke cikin *Biology Department*Garden na Ahmadu Bello University Zaria, gurin akwai dogayen itatuwa sunyi masa k'awanya kamar rumfa ga gurin da d'an duhu kujeru ne agun irin na d'alibai(student)na k'arfe an kakkafa su gefe kuma madaidaicin ramin ne cike da ruwa, ruwan haryana gansa kuka ga ciyayi nan da suka tsiro acikin ruwan har sunfito waje sun kwanta wani dogon tiyo suka zura cikin ramin kasancewar ramin yasha siminti ko ince kankare rabin tiyon na cikin rami rabi na waje ba abunda suke yawo sai kwad'ina, cakwa, tana, matsatstsaku,gwadayi dadai sauran su.
Anan 'yan Biology suke zuwa su d'auki wani abun daga cikin ruwan in zasuyi practical.

Hira sukeyi sama sama yanayin iskan yana ratsasu, cen daga d'an nesa da su, sukaji an cikasu da hargowa yanayin mai Kiran nasu kamar yana d'an cikin b'acin rai yace

"haba mana kun barni cikin makaranta inata bulayi ni d'aya tunfa 10am ina cikin School amma saiyanzu na tuna da munafikin garden d'innan shine na biyo naga ko kuna gun ashe dai nan d'in kuke"

yana magana yana k'ara sowa gun da suke

bushewa da dariya dukkan su sukayi, suna tafawa kuma suna kallon sa,
Habib yace

"haha Aliyu kafasan in kashigo School nan zaka nufo don bamu da gurin zuwa zama sai nan amma kullum k'orafinka d'aya ne.

Bashir dama magana ba damunsa tayiba ya dago kai daga kallon littafin dayake karantawa yace

"sondai wahalar da kai kuke"

Aminu da tunda suka fara magana da Aliyu baisa masu baki ba, ya kalli agogon hannun sa ya ce

"zamu iya tahiya Hall"

Aliyu yaki murmushi yace

"to agogo sarkin aiko sai mu tahi tunda kai baka da aiki sai karatu, to ai *Rayuwa*goro ce saida ban iska, Aminu kallon sa yayi shek'ek'e yace

"to saika koma gida ka zauna ka daina zuwa School d'in kana b'arnatar da kud'in baba a iska d'an rainin hankali dariya suka kuma bushewa dashi a karo na biyu inda sabo sun saba da halin su kasancewar Aminu na mugun son karatu kuma ya tsani yaga mai wasa da karatun sa kuma indai wasa ne gun karatu to aikin Aliyu ne bawani shiri suke ba kawai dai don yana team d'in su ne shiyasa gaba d'aya suka tashi suka nufi Hall way suna cigaba da hira, sun shiga ba da d'ewa malamin su ya shigo suka fara d'aukan darasi saida sai da suka kwashe tsawon sa'a uku kafin malamin yafita, suna fitowa masallaci suka nufa kai tsaye, bakuma, subar masallacin ba saida suka tsaya suka gabatar da sallar la'asar sannan suka koma Hall don d'aukan wani darasin.

Nan suka fara d'aukan darasin bayan malamin ya gama yayi masu yan tambayoyi domin yaga ko karatun na shiga kuma ga dukkan alamu karatun na shiga fannin da ya tambayi Aminu Muhammad Muhuta yayi masa bayani dalla dalla kuma ya fad'ad'a bayanin sa nan Hall ya d'auka da kuwwan d'aliban dan wasu cikin d'aliban sunji d'ad'in k'ara fad'ad'a bayanin sa wasu kuma haushin sa sukeji wai yacika iyayi da nuna yamafi malaman iyawa ga girman kai da miskilanci(wai duk shi d'aya)
yadda ya tsaya yin bayanin sa har kusan 6:10pm wasu sunkai k'ololuwa gun b'acin rai wai ya b'ata masu lokaci nan malamin ya sallami kowa ya kira Aminu suka fice tare suna magana, nan da nan kowa ya watse.

Aminu da malam Abdullahi tafe suke suna hira inda malamin ke karaba Aminu shawarwari na ya rike karatunsa da kyau yacigaba da kokarin indai, ya d'aure ahaka zaiga riban hakan gaba Aminu rike yake da jakar malam sai godiya yake har mota yaraka malam yayi masa sallama sannan yakoma gun abokansa suka kama hanyar gida Aminu yabuga mashin d'in,sa yakwashi mutun biyu Habib da Aliyu, Habib yana zaune a dogarawa, Aliyu kuma a layin, zomo, shi kuma Aminu a mahuta yake, shi kuma Bashir ba dan jigar Kaduna bane dan asali yola ne karatu ne ya kawosa nan shi nan cikin makaranta yake zaune a Hostel d'in su yawuce a bakin Mengate ya ijesu sukai sallama yanufi hangar unguwarsu suma nan inda ake lodi suka hau bada jimawaba suka tashi, Aliyu ya fara sauka sannan Habib ya sauka a randar Kano yatsallaka ya kuma taro napep da zai karasa dashi cikin Dogarawo, Aminu yana isa gida har anshiga sallar magarib dan haka yanashigar da mashin d'insa bai tarar dakowa ba a tsakar gidan don haka Alwala kawai yayi ya kama hanyar masallaci bayan sun idar yayo gida don akame(yunwa) ya dawo yayi kuma sa'a inna ta ida abinci yana gaidata yana sosa keya inda sabo inna ta saba da in ya dawo makaranta yana jin yunwa haka yake yi murmushi tayi ta d'auko abincin da ke kusa da ita ta mika masa ya k'arba yana godiya d'aki ya koma ya fara ci da bisimillah yana k'arewa ya shingida yana maida numfashi bada jimawaba aka kira sallar isha'i tashi yayi ya fiddo da kwanukan ya kama hanya ya tahi masallaci suna ida sallan yayo gida sai da safe ya leka yayi wa su inna da baba sallama sannan ya je ya shiga dakin sa ya sa kaya addu'a yayi ya kwanta ya janyo littafansa yana kishingide yana karatu baisan sanda barci barawo ya sace sa ba.

*WASHE GARI...*

*Muna Mugun Tare*🤝

*Taku Har Kullum*👱🏼‍♀

*Star Nucee36O*✨💫

RASHIN SANI NE SILA(Complete)  Where stories live. Discover now