Page 46-50

24 4 0
                                    

👺👺👺
👺 👺
👺
🏵❄🏵❄🏵❄🏵
*RASHIN SANI NE SILA.....*
❄🏵❄🏵❄🏵❄
👹👹👹
👹 👹
👹

*A TRUE LIFE STORY*

*By*

*Nusaiba i Usman Z.S*

'''SADAUKARWA GAREKU'''

_*NAFEESAT YUSUF*_
Feenah baby
_*SUWAIBA.U.ADAM'S*_
Subie
_*ZEEBNAB YAƘASAI*_
Queen
_*AYUSHA ILIASU*_
Queen
_*ANTY QUEENMERMUE*_

*_Wattpad StarNucee360_*

4⃣6⃣➡5⃣0⃣

_*Bismillahirrahmanirrahim*_

Fatimatu tayi kuka sosai, haka ma mijinta iyayen sune masu tausan su, har Allah ya basu dangana, ahaka Fatimatu taci gaba da wanka har tayi arba'in.

Bayan wañi dogon lokaci Allah yabaiwa Fatimatu wani cikin, sunyi murna ba kad'an ba, shima haka suka maida hankali ga rainon wannan cikin, harya isa haifewa, bayan ta haife ta da sa'a guda Allah ya karb'i ran abun data haifa, shima sunyi kuka ba kad'an ba.

Bayan haka akai-akai tana haihuwa yaran basa zama sai akan Aminu ne Allah ya tsallakar dashi ya rayu shiyasa suka d'auki son duniya suka d'aura masa, iyaye da kakannin sa.

Ranar sunan sa kuwa k'auyen Mahuta da kewayen su saida suka shaida wannan radin suna, don kakannin sa ba k'aramin kud'i suka barar ba, duk da dai su ba wasu masu shi bane amma sunada wadatar zuci ga zuciyar yi.

Yaro yaci sunan Muhammad Aminu sunan sa ya kafa tarihi a k'auyen Mahuta da kewayen su.

Suna ya tashi lahiya sai fatan Allah ya raya jariri ya kuma k'ara wa mai jego lahiya.

Yanzu kuma sun maida hankali ga rainon Aminu, da bashi kulawa ta musamman.

A kwana A tashi asarar mai rai, Aminu sai girma keyi kamar Kazan agric, gashi ya tashi cikin gatan iyaye da kakanni bashi da wata matsala, ga wayau gurin Aminu kamar me.

Aminu nada shekaru Hudu ya fara zuwa makarantar boko da islamiyya, Aminu najin dad'in makarantar da yake zuwa sosai don yana ganin yara kamar sa suna wasa, sab'anin gida da saidai iyayen sa da kakannin sa, ga kulawar da iyayen sa ke basa ta fannin karatun sa.

Yanzu Aminu nada shekaru Goma sha biyu, yana fahimtar karatun sa yadda ya kamata kwarai da gaske ga ladabi da biyayya, ana tsaka da haka ne sai kakan Aminu wato Mahaifin babansa ya kunno Kai da zancen a fidda Aminu a makarantar boko ya koma noma, gashi ya rura masu wuta, wannan magana ba k'aramin dugunzuma hankalin iyayen Amuni yayi ba da shi kansa Aminun.

Tausar tsohon akeyi amma ya tsaya kai da fata sai an fidda shi daga makarantar boko, sanda aka sako wadanda yakejin kunya sannan ya tausu amma da sharad'in dole Aminu ya dinga zuwa gona, babu yadda suka iya hakanan suka d'auki sharadin.

Aminu ya kammala Sakandare kuma Alhamdulillah sakamakon jarabawar sa sunyi kyau, cikin ikon Allah ya samu gurbin karatu a makarantar gaba da Sakandare, Ahmadu Bello University Zaria, ba k'aramin dad'i Mahifansa da kakannin sa sukayi ba.

Bayan ya kammala yin Registration, sai suka fara yin karatu, babu kama Hannun yaro, Aminu da hazak'ar sa ya fara karatu, inda tashi guda malamai da d'alibai suka gane sa, gashi bashi da girmai, yanada zanyi.

Shekarar Aminu d'aya da shiga ABU Allah yayi ma kakan sa Rasuwa, bayan anyi jana'idar sai aka cigaba da karb'ar gaisuwa, bayan anyi bakwai kowa ya watse.

Bayan kwana biyu, Katsam kuma sai suka kuma tashi da wani tashin hankalin rashin kakar Aminu, Mahaifiyar Baban sa Ba k'aramin tashin hankali ba suka shiga gaba d'ayan su, itama haka akai jana'idar ta aka kaita gidan ta na gaskiya, suka ci gaba da karb'ar gaisuwa.😭

_Vote_
_Share_
_Comments_
_And Follow_

*Muna  Mugun Tare*🤝

*Taku Har Kullum*👱🏼‍♀

*_Star Nucee36O_*✨💫

RASHIN SANI NE SILA(Complete)  Where stories live. Discover now