Page 36-40

105 6 0
                                    

👺👺👺
👺 👺
👺
🏵❄🏵❄🏵❄🏵
*RASHIN SANI NE SILA.....*
❄🏵❄🏵❄🏵❄
👹👹👹
👹 👹
👹

*A TRUE LIFE STORY*

*By*

*Nusaiba i Usman Z.S*

'''SADAUKARWA GAREKU'''

_*NAFEESAT YUSUF*_
Feenah baby
_*SUWAIBA.U.ADAM'S*_
Subie
_*ZEEBNAB YAƘASAI*_
Queen
_*AYUSHA ILIASU*_
Queen
_*ANTY QUEENMERMUE*_

*_Wattpad StarNucee360_*

3⃣6⃣➡4⃣0⃣

*_BAYAN SATI GUDA_*

Yau da wuri suka kammala jarabawar, domin haka sai suka nufi Hostel cen suka baje kolin su, sai hira sukeyi na irin rayuwar da kowannen su zaiyi da iyalin sa in Allah ya yarda kowa na fad'in tsarin yadda zaiyi agidan sa banda Aminu da ya koma gefe ya rakube ya zuba masu na mujiya yanajin su kawai, domin shi yariga da ya gama tsinkewa da al'amuran rayuwar sa na wannan abu domin duk *RASHIN SANI NE SILA* da yasan haka zata faru da bai fara ba ma.

Ganin shirun nasa yayi yawa ne, kuma bai tofa albarkacin bakin sa cikin hirar tasu ba yasa, suka fara tonon sa kodan ya saki jikin sa, tunda yaki sanar dasu damuwar sa, domin ga damuwa nan k'arara akan fuskan sa, amma da an tambaye sa sai yace ba komai, abun naci masu tuwo a kwarya amma ba yadda suka iya, sai tayasa da addu'a.

Akwana a tashi asarar mai rai

Acikin wannan mawuyacin halin Aminu suka kammala jarabawar su, sai kuma jiran sakamako, sai kuma suka daura aikin project, Aminu bai iya yin komai ba sai su bashir ne sukai masa

Bayan sun kammala komai sai kowa yakama kansa suka ci gaba da harkokin gaban su.

*_Bayan Wasu Watanni_*

Aminu na dawowa daga gona sai ga sak'o ya shigo wayar sa, da yayi biris bazai dubs, ba domin yana tunanin ko sak'on kamfani ne da suka saba turowa,amma sai wata zuciyar ta ce gara ya duba yagani

Zaro wayar yayi daga aljihun sa ya duba

sak'o ne daga abokin sa Habib, ga abun da sak'on ya kunsa

_Assalamu-Alaikum Mutumina gafamu a cikin Makaranta sakamako ya fita tin kwana biyu da suka wuce, nayi k'ok'arin samunka na sanar dakai yau zamu shigo amma hakan bai samu ba am sorry, suma sauran sun gwada ka still yak'i shgowa, shiyasa nayi maka text ko Allah zaisa ya shigo, plss komai kakeyi ka bari ka shigo Campus, kasan alk'awari ne sai mun had'u dukkanmu sannan zamu duba result ko, to kai kad'ai ne babu, plss ka gaishe da Innar mu saika shigo_

Aminu ya duba tun lokacin da aka turo sak'on, sai yaga tun 8:16am na safiya gashi yanzu kusan 3 da mintoci na rana, cikin azama ya tashi ya d'auki bokati ya d'ibi ruwa ya fada wanka cikin mintina da basu wuci 15 ba ya shirya, yayi ma Inna sallama ya kuma sanar da ita gaisuwa daga abokanayen sa, ta amsa da

"To madalla ina amsawa, nima ka gaishe mani dasu Allah yayi maku albarka "

Aminu ya amsa da

"Ameen Inna Mungode kwarai, ni na tafi "

Inna tai masa adawo lahiya da fatan su samu sakamako mai albarka

*CAMPUS*

Yana isowa a bakin notgate suka had'u sunfi k'arfin awanni bakwai agun suna jiran isowar sa,gaggaisawa suka shigayi, da tambayar junan su bayan saduwa.

Aliyu tace

"Ai da baka iso yanzu ba daka ganmu bakin k'ofar gida muna kwada'a sallama "

Aminu yace

"Kai dako kun kyauta, yau dako Inna tayi manyan bak'i "

Shigewa makarantar sukayi cikin raha da dariya suka nufi gurin dubawa kowa ya shiga duba nasa

Cikin Murna da jin dad'i dukkanin su suke kallon junan su domin dukkanin su sakamako yayi kyau, amma kash banda na abokin su domin shi dukka courses d'in ya fad'i, nan da nan kuma duk murnar da suke ciki ta koma ciki, tunda na abokin su kuma aminin su baiyi kyau ba, su sunmafi Aminun shiga tashin hankali, domin shi Aminun nema yake k'ara tausasu yake kwantar masi da hankali duk da shima irin tashin hankalin daya shiga, abun yayi mugun d'aga masa hankali, a haka sukai ta jimami, sai yamma lik'is sannan sukayi sallama kowa yakama kansa cikin tsantsan tashin hankali da rashin madafa

Aliyu, Habib da Bashir ganin baza su iya zura idanu komai ya tafi a haka ba yasa suka duk'ufa da Aljihun su gurin ganin ansamu komai ya dai-dai ta, amma inah hakan yaci tura, Habib ya sayar da system da wayar sa, Bashir ya sayar da roba-roban sa da bai jima da siya ba shi kuma Aliyu dukiyar Auren k'anwar sa ya d'auka, suka had'a suke bin malaman su suna sakin su don dai Aminu ya samu ya wuce, duk inda sukaje sai ace babu damuwa komai zai dai-dai ta, cikin jin dad'i suka koma gida, duk wannan abu da sukayi ba tare da sanin Aminu sukayi ba.

*Bayan wasu watanni*

Ganin lokacin bautar k'asa na k'ara k'aratowa yasa su Habib k'ara komawa gurin malaman su da sukace zasu taimaka masu donjin kwanan zancen, domin malaman sunce sujira zasu neme su amma shiru kakeji, duk ofishin da sukaje sai su fatattake su, mutun guda ne kawai yayi masu maganar fahimta,

Ganin haka yasa suka nemi Aminu suka labarta masa komai dake wakana, Aminu yaji dad'in kulawar abokanayen sa sosai akan sa, sunyi amfani da k'arfin su da dukiyar su, duk don su gyara masa goben sa, kai samun abokanaye irin haka a wannan marran sai an tona, baisan sanda hawaye ya wanke masa fuska ba😭

*Allah ka had'amu da abokanaye masu sonmu fisabilillah*

_Vote_
_Comments_
_Share_
_And Follow_

*Muna Mugun Tare*🤝

*Taku Har Kullum*👱🏼‍♀

*_Star Nucee36O_*✨💫

RASHIN SANI NE SILA(Complete)  Where stories live. Discover now