Page 66-70

23 4 0
                                    

👺👺👺
👺 👺
👺
🏵❄🏵❄🏵❄🏵
*RASHIN SANI NE SILA.....*
❄🏵❄🏵❄🏵❄
👹👹👹
👹 👹
👹

*A TRUE LIFE STORY*

*By*

*Nusaiba i Usman Z.S*

'''SADAUKARWA GAREKU'''

_*NAFEESAT YUSUF*_
Feenah baby
_*SUWAIBA.U.ADAM'S*_
Subie
_*ZEEBNAB YAƘASAI*_
Queen
_*AYUSHA ILIASU*_
Queen
_*ANTY QUEENMERMUE*_

*_Wattpad StarNucee360_*

6️⃣6️⃣➡️7️⃣0️⃣

*_CIGABAN LABARI_*

   Dogon numfashi Inna ta sauke tace

" yanzu d'annan duk wad'annan abubuwan da suka faru kak'i gaya ma ni  ko Mahaifin ka  mai yasa"?

Aminu yace "Inna banason hankalin ku ya tashi ne amma ki gafarce ni "

Inna tace " tashi muje gun Mahaifin naka"

ba musu ya tashi suka nufi dakin Mahaifin nasa sun sameshi ya gama kimtsawa zai fita nan Inna ta dakatar dashi dacewa

"Har ka gama kimtsawa dama gurin ka muka zo nida d'annan Don Allah zamuyi magana da kai"

Baice kamai ba ya koma ya zauna bakin gado yana fuskantar su, Inna ta zauna gefa shi kuma Aminu ya zauna a k'asa ya sunkuyar da kai k'asa

Mahaifin Aminu yace"mai ke tafe daku tunda naganku  ku biyu to nasan babban abune"?

jinjina kai Inna tayi sannan ta koro masa bayanin abun da yake faruwa da tilon d'an su ba k'aramin tashin hankali Mahaifin Aminu ya shiga ba kallon Aminu yayi yace

" yanzu kai irin wannan abun na faruwa  da kai baka sanar da muba sai yanzu da abu ya gawurta ai bamuga ta zama ba tashi yanzu zamuyi mutafi gun Kaka Malam 

Tashi sukayi suka sakaya gidan suka nufi gidan Kaka Malam

  Zaune suke a zauren Kaka Malam gaggaisawa sukayi sannan aka taba barkwanci kasancewar Kaka Malam yanada ban dariya sannan aka maida hankali ga abun da ya kawo su kaka Malam ya tambaye su "mai ke tafe daku, domin yanayin fuskokinku yana d'auke da tashin hankali "

Mahaifin Aminu ya sanar da Kaka Malam duk abun da ke faruwa kamar yadda Mahaifiyar Aminu ta sanar da shi

Kaka Malam ya kalli Aminu yace haka akayi ko da k'ari"?

Aminu ya amsa da "eh" yana  jinjina kai

Kaka Malam yayi masa wasu tambayoyi sannan yace " to Malam Aminu bamu wuri"

Aminu ya fita daga waje yana jiran iyayen nasa.

_Vote_
_Comments_
_Share_
_And Follow_

*Muna Mugun Tare*🤝

*Taku Har Kullum*👱🏼‍♀

*_Star Nucee36O_*✨💫

RASHIN SANI NE SILA(Complete)  Where stories live. Discover now