Page 96-100

61 3 0
                                    

👺👺👺
👺 👺
👺
🏵❄🏵❄🏵❄🏵
*RASHIN SANI NE SILA.....*
❄🏵❄🏵❄🏵❄
👹👹👹
👹 👹
👹

*A TRUE LIFE STORY*

*By*

*Nusaiba i Usman Z.S*

'''SADAUKARWA GAREKU'''

_*NAFEESAT YUSUF*_
Feenah baby
_*SUWAIBA.U.ADAM'S*_
Subie
_*ZEEBNAB YAƘASAI*_
Queen
_*AYUSHA ILIASU*_
Queen
_*ANTY QUEENMERMUE*_

*_Wattpad StarNucee360_*

9️⃣6️⃣➡️1️⃣0️⃣0️⃣

Tarihi dai na k'ok'arin k'ara mai-mai ta kansa domin kuwa yanzu kimanin shekaru hudu kenan dayin auren Aminu da Nuriyya amma shiru kakeji babu ciki babu alamar sa ko b'atan wata bata tab'ayi ba, har asibiti Aminu ya d'auki Nuriyya ya kaita aduba ko lahiya da kansa adubashi ko lahiya amma a bincike likitoci sunce lahiya suke lokaci ne dai baiyi ba sai sanda Allah yaso, jin lahiyar su k'alau yasa hankalin sa ya d'an kwanta

Domin tsoron shi kada yadda iyayen sa suka haifeshi tilo shima ya kasance haka, domin Aminu ya tashi ba yayye ba k'anne to yana mugun son yaga yara kusa dashi sosai, idan kuma yayi la'akari da gidan su matar shi su suna haihuwa da yawa domin Nuriyya tana da k'anne dawa amma duk ba wannan ba Allah shike tsara komai kuma yadda yaso haka zai kasance kowa da irin tasa k'addara baiwa, tuna hakan da yayi sai ya fawwala ma Allah komai ya cigaba da addu'a

*BAYAN WASU WATANNI*

Ita dai Nuriyya bata gane ma kanta ba amma zurfin ciki irin nata bata bari Mai gidan nata ya sani ba, ga yawan motsi da takeji acikin cikin ta kamar d'an k'adan gare bata gaya ma kowa ba har cikin ya fara mata k'arfi sai ta koma yawo da hijabi ko acikin gida ne

Ana haka sai tafiya ta Kama Aminu zaije ziyarar Aminan sa ga ita Nuriyya tak'i ta bisa kuma inyaje zai jima tunda ba guri d'aya zai tsaya ba

Ya shirya ya tafi, da albarka iyaye ya isa lahiya,yayi kwanakin da zaiyi bayan ya gama zagaye gidagen abokan nasa gurin Aliyu ne k'arshe sai kuma aiki ya tsareshi ya tsaya zai taimaki abokin nasa akan wani babban aiki daya taso a kamfanin su Aliyu,

Aminu ya kira gida ya sanar dasu halin da ake ciki wasa-wasa sai da aikin ya kai Aminu kusan watanni 8 sannan suka gama aranar da akin ya kammala a ranar Aminu yayi ma Mahuta diran mikiya ya kuma dawo da motar sa da Aliyu ya siya mashi y'ar dai-dai da ita, kai tsaye gida ya nufo da sallama ya shigo gidan

"Assalamu-Alaik..."sauran sallamar mak'alewa sukayi a mak'ogoron sa ganin halin da Nuriyya ke ciki, adurk'ushe take bisa guiwoyin ta sai zufa ke keto mata da hawaye ai bai tsaya wata-wata ba ya d'auke ta yayi mota da ita sai AbuTeaching hospital shika suna isowa aka k'arb'e su, sai da ya samu nutsuwa sannan ya samu zarran kiran gida aka samu masu zuwa aka aika gidan su Nuriyya suma

Mutum uku suka zo, sai ga wata Nurse ta fito da farar takar da a hannu ta mik'a ma Aminu tace"ga abun da ake buk'ata da sauri plss" da sauri Nurse d'in ta koma ciki su kuma suna zauna ak kujerun da aka tanada don zaman wad'anda suka kawo mai haihuwa (labour Ward) sannan Aminu ya samu yaje ya siyo kayan jarirai da duk abun da aka bashi a rubuce ya dawo jikin sa duk ya jik'e da jini sai k'ari keyi amma sam bayajin haka, shiga ciki yayi ya basu sannan ya dawo yanata safa fa marwa ya kasa zama cikin matan da suka zo y'ar uwan Inna tazo kusa dashi ta kira sa gefe tace " ya kamata kaje gida ka canza kyan nan kila kafin ka dawo ta haihu "

Shiru yayi sannan yace "inna to bara na... " shiru yayi sakamakon tambayar da wata Nurse da yanzu ta fito tayi" su waye suka kawo Nuriyya Abubakar Nura Mahuta"?

Da sauri Aminu ya nufi gurin ta magana sukayi k'asa-k'asa sannan ta juya ta koma ciki, daskarewa Aminu yayi agurin

Da sauri suka k'araso suna tambayar sa "lahiya maiya faru"?

Shiru bai basu amsa ba duk sunbi sun rud'e

_Vote_
_Comments_
_Share_
_And Follow_

*Muna Mugun Tare*🤝

*Taku Har Kullum*👱🏼‍♀

*_Star Nucee36O_*✨💫

RASHIN SANI NE SILA(Complete)  Where stories live. Discover now