Page 61-65

26 4 0
                                    

👺👺👺
👺 👺
👺
🏵❄🏵❄🏵❄🏵
*RASHIN SANI NE SILA.....*
❄🏵❄🏵❄🏵❄
👹👹👹
👹 👹
👹

*A TRUE LIFE STORY*

*By*

*Nusaiba i Usman Z.S*

'''SADAUKARWA GAREKU'''

_*NAFEESAT YUSUF*_
Feenah baby
_*SUWAIBA.U.ADAM'S*_
Subie
_*ZEEBNAB YAƘASAI*_
Queen
_*AYUSHA ILIASU*_
Queen
_*ANTY QUEENMERMUE*_

*_Wattpad StarNucee360_*

6️⃣1️⃣➡️6️⃣5️⃣

*** ********* ***

Yanzu Aminu daga noma sai soyayya da Nuriyya yasa agaba sosai suke samun alheri a noman su kamar kullum yauma suna gona suna aiki da mahaifinsa, sai Mahaifin nasa yace mashi

" Am kai ni zan tafi gida don haka kayi k'ok'arin kammala noman nan kafin ka dawo gida "

Aminu cikin girmamawa ya amsa da "to "

Sannan mahaifin nasa ya tafi ya barshi bada jimawa ba ya kammala ya kakkab'e jikin sa ya sab'a fatanyar sa ya kama hanyar cikin gari.

Nisawa inna tayi tana gyara zaman ta shima Aminu muskutawa yayi sannan ya ci gaba da ba Inna labarin

Tafe make abuna cen na hango wata kyakkyawar doguwar buduruwar bafulatana fara tas tana tunkaro ni tasha kayan fulani fari sai wani rangwad'a takeyi k'ugunnan kamar zai karye dan rangwad'a tana da tsayin fuska da manyan idanu fari k'al eye boll dinta brown ga dogon hanci da ya zauna d'as kamar biro bakinta d'an k'arami hakwaran ta farare k'al da dimple a kumatun ta gashin ta har gadon baya tana rik'e da y'ar jakar fata k'arama ahannun ta tana lilo dashi sai da tazo dab da ni sannan tace

"Dan Samari zoka rakani"

Tun daganan ban kara sanin inda nake ba sai dai na farka na ganni a wani Makeken gida mai kyan gaske tsayawa tsara kyan gidan b'ata lokaci ne komai na gidan Golden color ne ga wasu mata nan kyawawa biyu a gefena na dama biyu ta gun k'afafun sa biyu ta kansa uku ta gefena na hagu shiru nayi ina nazarin su, yunkurawa nayi na tashi zaune zaunawar na keda wuya sai ga wannan mai kayan fulanin dayagani d'azu da tace 'nazo na rakata' amma yanzu ta sauya kaya kayan jikinta yanzu na alfarma ne irin kayan masu sarauta ta sanya, ita da wasu mata, d'aya a damar ta d'aya a hagun ta tana k'arasowa ta kalle ni tayi dariya tace

"d'an Samari zaka iya tuna shekaru biyu da suka wuce, yarinyar da kaso ka mara a makaranta"?,

Ni dai ban iya cewa komai ba sai ido na kawo na sanya masu nayi zuru wani irin yare tayi kawai sai naga wani irin bakinkirin d'in Mutun ya baiyana agun ga k'aton kai da ciki bashi da kyan gani cikin dai wancen yaren da ban fahimta ta kuma yima wannan Mummunar halittar magana kafin k'iftawa ido sai gamu cikin wani bak'in daji mai ban tsoro kafin kuma k'iftawar ido wannan Mummunar halittar ya b'ata ya barni ni d'aya (masu karatu in baku mantaba dajin da nayi maku bayani a farko kenan, daga nan har abubuwan da suka faru har ya samu ya dawo gida kuma naki sanar daku abun daya faru dani saboda banason hankalinku ya tashi shiyasa Inna.

*_CIGABAN LABARI_*

_Vote_
_Comments_
_Share_
_And Follow_

*Muna Mugun Tare*🤝

*Taku Har Kullum*👱🏼‍♀

*_Star Nucee36O_*✨💫

RASHIN SANI NE SILA(Complete)  Where stories live. Discover now