Page 41-45

28 3 0
                                    

👺👺👺
👺 👺
👺
🏵❄🏵❄🏵❄🏵

*RASHIN SANI NE SILA.....*

❄🏵❄🏵❄🏵❄
👹👹👹
👹 👹
👹

*A TRUE LIFE STORY*

*By*

*Nusaiba i Usman Z.S*

'''SADAUKARWA GAREKU'''

_*NAFEESAT YUSUF*_
Feenah baby
_*SUWAIBA.U.ADAM'S*_
Subie
_*ZEEBNAB YAƘASAI*_
Queen
_*AYUSHA ILIASU*_
Queen
_*ANTY QUEENMERMUE*_

*_Wattpad StarNucee360_*

4⃣1⃣➡4⃣5⃣

_*Bismillahirrahmanirrahim*_

Ganin kukan da Aminin nasu ya keyi, suma basusan sanda kuka ya kwace masu ba,babu mai rarrashin wani cikin su saida sukayi mai isar su sannan sukayi hak'uri, jarrabta ce suna mai rok'a wa abokin su Allah ya bashi ikon cinye wa, babu mai iya wani magana cikin su ahaka sukai wa junan su sallama kowa ya kama kansa, jiki babu lakka.

_BAYAN KWANA BIYU_

Duk an tura kowannen su jihar da zaiyi tasa bautar k'asar Aminu ya ziyarce su, kuma har tasha yayii masu rakiya, kowannen su ya tafi zuciya babu dad'i,domin ko kwakwkwaran magana gazawa sukayi, Aminu saida yaga tashin motar kowannen su sannan ya bar tashar yayi gida.

_*BAYAN WASU SHEKARU*_

Aminu ne gurfane gaban mahaifin sa, yana mai k'ask'antar da kansa, fad'a Mahaifin nasa keyi sosai

"Waishin shi kud'innan hak'osa akeyi ko tsink'o su shekaru nawa kenan kana mai-mai ta aji guda, ga abokanayen ka nan duk suna aiki amma kai kullum jiya iyau, gaba d'aya kak'i maida hankali ga karatu da kai kake ma wasu fad'an su mai da hankali a karatu"

"To gaskiya na suk'e tunda abun ya zama haka, _don haka kabar karatun kadawo mucigaba da aikin gona tare_"

Yana kaiwa nan yace

"'Bacemin dagani "

'Kwata-kwata bai tsaya yaji dalilin saba jiki babu lakka ya tashi ya fice'

_*WAIWAYE ADON TAFIYA*_

_WAYE MUHAMMAD MAHMUD MAHUTA_

Malam Muhammad Mahmoud Mahuta haifaffen Mahuta ne,k'auyen na nan dab da shiga cikin shika Gari, kaka da kakanni duk anan suke,ya tashi cikin gata gun iyayen sa sun bashi tarbiya dai-dai gwargwado,amma basu barshi yayi zurfi gurin karatun boko ba, sai dai na mahammadiyya duk ko da son karatun da yayi, Mahaifin sa Malam Mahmoud Mahuta yace

"Noma ne kawai gatan da zai iya bashi ya rik'i iyalin sa".

Bayan girman sa, yana da shekara 17 Mahaifin sa yayi masa auren gata, _wato auren jeka ga d'akin ka_ da d'iyar abokin sa duk dai anan Mahutan da amaryar sa Fatimatu Mahaifiyar sa Amina taso d'an nata yafi haka kafin amasa aure amma bata da mafita hakanan ta rungumi abun da hannu bibbiyu.
Bayan biki ya watse ango ya tare a d'akin amaryar sa.

Zamane na amana da mutunta juna ke gudana tsakanin Mahmoud da Fatima, ba maijin kansu, ga girman iyayen sa da nauyin su da takeji, yanzu Fatimatu ce ke gudanar da kowanna aiki na gidan domin tuni ta hana surukar ta aiki. A haka suke zaune cikin kwanciyar hankali duk da an fara zuga Fatimatu wai sun maisheta baiwa a gidan da sauran gulmammaki Fatimatu tayi biris da maganganun mutane ta rungumi Mijin ta da iyayen sa.

_*BAYAN SHEKARA BIYAR*_

'Kauyen mahuta da kewayen su, sai tsegumimmika su keyi kan cewa Fatimatu bata haihu ai dama dangin su haka suke in sunyi su haihu d'aya shi kenan koma bazasu haihunba ma kwata-kwata.

Cikin ikon Allah saiga ciki ya bayyana ajikin Fatimatu wanda ita kanta batasan dashi ba saida ya fito, Murna da farin ciki baya musaltuwa gurin su Fatimatu da iyayen sa, kulawa ta musamman suke baiwa Fatimatu da abun dake cikin ta.

'Yan gaza gani kuwa bakin su yak'i mutuwa, domin gani suke kamar k'arya ne ba wani ciki kasancewar ba wani fita Fatimatun keyi ba, ga cikin yazo mata da laulayi sosai bata wani cika lahiya ba, ahaka-ahaka har Allah ya basu ikon kaiwa lokacin haihuwar.

Bayan dogon nak'uda da tasha, ta haife santala-santalan y'ay'a y'an biyu maza, manya tubarakallah Masha Allah, kwana biyu da haihuwar ta yaran sukace ga garinku nan, Allahu akbar kullinafseen za'ikatun maut, kowanna rai saiya d'and'ani mutuwa.

Allah yaji kan wad'and'a suka rigamu gidan gaskiya, in tamu tazo Allah shi sa mucika da kalmar shahada.

_Vote_
_Comments_
_Share_
_And Follow_

*Muna Mugun Tare*🤝

*Taku Har Kullum*👱🏼‍♀

*_Star Nucee36O_*✨💫

RASHIN SANI NE SILA(Complete)  Where stories live. Discover now