Page 71-75

27 4 0
                                    

👺👺👺
👺 👺
👺
🏵❄🏵❄🏵❄🏵
*RASHIN SANI NE SILA.....*
❄🏵❄🏵❄🏵❄
👹👹👹
👹 👹
👹

*A TRUE LIFE STORY*

*By*

*Nusaiba i Usman Z.S*

'''SADAUKARWA GAREKU'''

_*NAFEESAT YUSUF*_
Feenah baby
_*SUWAIBA.U.ADAM'S*_
Subie
_*ZEEBNAB YAƘASAI*_
Queen
_*AYUSHA ILIASU*_
Queen
_*ANTY QUEENMERMUE*_

*_Wattpad StarNucee360_*

7️⃣1️⃣➡️7️⃣5️⃣

Kaka Malam ya kalle su cike da kulawa yace" gaskiya da alama yaronnan gamo yayi da bak'aken jinnu kuma ya bata masu rai don gaskiya da hannun sa ya sauka bisa jikin yarinyar nan da abun da zai faru saiya fi haka domin su basu cika yafiya ba tunda ba mutane bane su aljanu akowani lokaci suna iya komawa mutane su shiga cikin jama'a ba tare da kowa ya sani ba kuyita mu'amula da su idan ba dalili babba ba ko wanda Allah ya basu ikon sani ba to za'a tab'a ganewa ba domin muna tare damu gun kasuwanci, makarantu, asibitoci, mak'ota, cikin malamai ko abokanai kai dama ko inane shiyasa daraja mutum yake da kyau ko ka sansa ko baka sansa ba "

numfasawa Kaka Malam yayi sannan ya kuma kai kallon sa ga Malam Muhammadu sannan ya d'aura da cewa

"Gaskiya anan yayi wauta amma yanzu abu na farko da zaku farayi  masa shine a nemo masa Matar aure, kafin auren zamuyi ta masa sauka da addu'oi da sadaka, shi ma da ku sai kun dage da addu'a zan baku irin addu'oin da zakunayi ku k'ara akan wanda kukeyi sannan shi yaron yana wasa da addu'oi gaskiya addu'ar fita gida azkarin safe da maraice amma sai fa ya dage kuma dole sai kun sanya masa ido da taimaka masa kada ya sanya wasa Allah yayi jagora.

( iyaye sai muna taimakon yaran mu wajen kula da dagewa ganin sunayin addu'oin da kokari wajen koya masu domin addu'a shine takobin kowanna musulmi mumini)

Kaka Malam ya basu wasu addu'oin a rubuce a wata takarda yace" ga wad'annan addu'oin ku dage da yinsu kuma kada ku bari a d'auki lokaci ayi masa aure " Kaka Malam sai k'ara jaddada masu yake ayi ma Aminu aure

Godiya sosai su Inna sukai ma Kaka Malam sannan sukayi masa sallama suka fita, suka samu Aminu zaune bisa dakali yana tsimayen fitawar nasu tashi yayi suka nufi gida shi kuma Mahaifin nasa ya wuce gun kasuwancin nasa

Isan su gida bada jimawa na Inna ta kira Aminu bayan yazo tace " ga wannan addu'oin  ka dage dayi da kuma azikarin safe da maraice, Kaka Malam yace kana sakaci da addu'a Don Allah ka dage d'annan Allah ya kara tsare mu da sharrin su, itama tsayuwar dare ka k'ok'arta ka farayi ka nemi tsari da kariya"

Godiya Aminu yayi" Inna nagode kwarai insha Allah kuma zan dage akai"

sannan ya tashi ya fice ya tafi d'aki

Nannauyan numfashi Inna ta sauke ta bishi da kallon tausayi harya b'ace ma ganin ta

Aminu ya dage da addu'oin da Kaka Malam ya bashi ya kara akan wanda yakeyi ya had'a da sallan dare, cikin yardan Allah sai abubuwa da dama suka sauya ma Aminu ba kamar da ba yanzu yana samun nutsuwa bayanwan fad'uwar gaba da yake fama dashi ba yawan mafarke-mafarken da yakeyi da suke firgita shi
 

Sai dai maganan karatu har yanzu jiya iyau ba abun daya canza

_Vote_
_Comments_
_Share_
_And Follow_

*Muna Mugun Tare*🤝

*Taku Har Kullum*👱🏼‍♀

*_Star Nucee36O_*✨💫

RASHIN SANI NE SILA(Complete)  Where stories live. Discover now