Page 6-10

176 8 0
                                    

👺👺👺
👺 👺
👺
*RASHIN SANINE SILA.....*
👹👹👹
👹 👹
👹

*A TRUE LIFE STORY*

*By*

*Nusaiba i Usman Z.S*

*IDON MIKIYA WRITTER'S ASSO*🦅

'''SADAUKARWA GAREKU'''

*_JINJINA TARE DA GAISUWA TA MUSAMMAN GAREKA YA ANAM D'ORAYI ALLAH K'ARA KAREKA KAI NA DABANNE_*

_*NAFEESAT YUSUF*_
Feenah baby
_*SUWAIBA.U.ADAM'S*_
Subie
_*ZEEBNAB YAƘASAI*_
Queen
_*AYUSHA ILIASU*_
Queen
_*ANTY QUEENMERMUE*_

*View...*

nusaibaiusmanzs.WordPress.com

6⃣➡🔟

Wani abun mamaki sai kawai na tsinci kaina a cikin gonna a zaune kuma cikin dare na juya gabas da yamma kudu da arewa dajine sosai kuma dajin dana sani acikin gonar Mahaifina nake tunda nasamu hankalina ya d'an dawo jikina na zabura na zura da gudu nayi cikin gari kasancewar gonar mahaifina tana nesa da gari na shiga cikin gari ba kowa awaje sai dai kukan karnuka da jemagu ina zuwa banyi wata wata ba nashiga cikin gidan mu na bud'e d'akina kasancewar dama bawai ina rufe d'akin bane tunda ba mai shiga min ko za'a shiga inna ta tana hanawa.

Koda na shiga d'akin ban rutsaba kuma ga daren yayi mani tsayi haryanzu tsoron dake jikina bai sakeni ba domin nashigo gida da misalin karfe 2:37 amma duk sanda zan d'aga kai na kalli agogo sai inga minti biyu ko uku ya k'aru ahaka har na k'agu ina nan dai ban gusheba ina zaman jiran asuba lokaci bai ida ba na fita karfe 3:42 na tafi masallaci na nayi alwala na shiga na dauki alqur'ani mai girma na fara karantawa har lokacin kiran sallah ladani yazo ya kira ahaka mutane d'aya bayan d'aya suka d'inga zuwa har masallaci ya cika liman na zuwa aka kabbara sallah, nima nashiga sahu mukai sallah muka idar ni kuma na cigaba da karatun Alqur'ani na har mutane suka tahi 'yan tsiraru ne suka rage a masallacin, bani na bar masallacin ba sai 7:39 nai hanyar gida a hanyar ne na had'u da k'anin budurwa ta Zulk'ifilu ya gaida ni yace " ya Aminu Anti Nuriyya tayi fushi da kai wai kayi tahiya har kwana biyar baka sanar da ita ba, jiya nazo ta k'ofar d'akin ta da dare naji tana kuka amma bangaya wa kowa ba sai kai" Aminu ya sha fa kansa ya laluba aljihun sa koda bai da tabbacin zaisamu kud'i ko babbu cikin sa'a kuwa sai ya lalubo naira ashirin ya mik'a masa yace "to ga wannan amma fa kada ka gaya wa kowa" yace to"yace "ga wannan ka sai k'osai"Zulk'ifilu cikin murna yana tsalle ya k'arb'a yace" nagode ya Aminu" ya ruga da gudu ya bar Aminu nan yana murmushi da tunanin zuci ni harga Allah Zulk'ifilu na burge ni duk da k'arancin shekarun sa don baiwuci shekaru 5 zuwa 6 ba amma sai wayau in ya fad'i wata maganar sai kace angaya masa dan in ban mantaba farko farkon had'uwa na da Nuriyya in naje zance tai ta share ni sai rannan naje gidan su da ta tashi fitowa sai ta fito da shi Zulk'ifilu domin k'a idar gidan Malam ke nan in anzo zance gun 'ya'yan sa sai sun fita da 'yan rakiya kannan ta, bayan sun gaisa gaisuwa ta k'are ya k'are sai ya fara zubo mata kalaman soyayya tana ta sussunne kai sai kace (Feenah da Subie sunga Habibaties d'in su😜)bata tanka shi ba harya gama zuban sa, yayi kid'an sa yayi rawar sa batace uffan ba haryayi yagama ya yayi mata sallama ya tafi.

Wanshekare haka ya koma wannan karan ma sai da ta b'ata lokaci sannan ta fito kuma tare da Zulk'ifilu yauma suka fito bayan sun gaisa bata kuma tanka shiba yanata zubar sa shi d'aya kada bakin Zulk'ifilu sai yace ma Antin sa"wai Anti in kinzo gun ya Aminu baki magana ne kada fa ki manta da ke naji ana labarin irin matan da suke masa yawon zuwa gunsa don ya so su amma ke cikin jin d'ad'i yazo ya ce yana sonki mukai ta murna kuma harda ke""Oho kodai hakanne jan ajin da naji su ya Najib suna magana da 'yan Matan su, suke masu kodai menene idan ya gaji ya canzaki ai shikenan kinga tahiya ta" yana k'arasa maganar ya na tahiya cikin gida, Nuriyya don kunya kamar ta tsaga k'asa ta shige takeji,a gaskiya don son Aminu ina son sa amma mazan sai da jan aji ne shiya sa, Aminu ya juyo da kansa daga kallon Zulk'ifilu d'aya shige gida ya maido kallon sa ga mosoyiyar tasa da kallon tuhuma yace"hakane zancen da Zulk'ifilu ya fad'a"kasa motsa bakin ta tayi ta d'ago tafin hannunwan ta ta rufe fuska tai Kasa da kai Aminu ya kuma maimaita kansa da gudu ta ranta ana kare ta shige gida tana murmushi,shima murmushin ta barshi yanayi barin gudun da tayi duk ta tafi da imanin sa ta dagula masa lissafi, ba lakka jikin sa ya bar k'ofar gidan ya koma gidan.

Sassanyar ajiyar zuciya ya sauke yana murmushi ya k'arasa gida tunda dama ba tazara tsakanin inda ya tsaya da k'ofar gidan yayi sallama ya shiga innar sa ya tadda a tsakar gida tana aikin had'a kalaci naje na rusuna na gaisheta ba yabo ba fallasa ta amsamin kafin ta jefomin tambaya "yanzu d'annan ina katafi har tsawon kwana biyar? bawanda yasan inda kaje?anya Aminu kataki hanya madaidaiciya kuwa in baka wa zai taimaka ma mahaifinka aikin gona?Aminu na nan dai kansa sunkuye yana kallon k'asa sai bata hak'uri yake ahaka har ta gama mani fad'a ta daura da nasi ha, tagama sannan ta bani kalaci na, na koma d'aki naci, ina daga cikin d'aki naji sallamar mahaifina sai da na bari ya shiga d'aki ya gama kalacin sa sannan na fito naje d'akin sa na gaida shi, bayan na gama gaidashi Baba ya d'ago kai ya kalleni ransa a matukar bace yace"ina ka shiga har tsawon kwana biyar ba tare da ka sanar da ni ko innar ka ba? yanzu Aminu abunda kayi yayi maka dai dai kenan? Ko rashin jin maganar taka har takai kasa k'afa ka fita gidannan ba tare da sanin muba? Oho kai kana ganin ka kawo kenan, ka girman da zaka iya yin gaban kankako? to kashiga taitayinka kuma kada ka k'ara sa k'afa kayi tahiya batare da sanin mu ba na gaya maka" ran sa amaruk'ar b'ace fusace yake wannan maganar, Aminu tundai d'aya sunkuyar da kai bai kuma d'agowa ba sai hak'uri da nake baiwa Baba daga bisani ya sallame ni na koma d'aki na,na kwanta sai tunani nake na irin halin da nashiga amma haryanzu a tsorace nake gaskiya ga yawan firgici da nake fama da shi koda d'an b'urunru b'era naji sai naji na firgita.......

Muna Mugun Tare🤝

Taku Har Kullum👱🏼‍♀

*Star Nucee36O✨💫*

RASHIN SANI NE SILA(Complete)  Where stories live. Discover now