Page 91-95

43 4 0
                                    

👺👺👺
👺 👺
👺
🏵❄🏵❄🏵❄🏵
*RASHIN SANI NE SILA.....*
❄🏵❄🏵❄🏵❄
👹👹👹
👹 👹
👹

*A TRUE LIFE STORY*

*By*

*Nusaiba i Usman Z.S*

'''SADAUKARWA GAREKU'''

_*NAFEESAT YUSUF*_
Feenah baby
_*SUWAIBA.U.ADAM'S*_
Subie
_*ZEEBNAB YAƘASAI*_
Queen
_*AYUSHA ILIASU*_
Queen
_*ANTY QUEENMERMUE*_

*_Wattpad StarNucee360_*

9️⃣1️⃣➡️9️⃣5️⃣

*WASHE GARI*

Washe gari bak'i suka watse sai tsiraru suka rage yan dangi na kusa sosai Ango da Amarya sun cika bak'in su da shatara na arziki sannan suka tafi suna fatan nan da wata tara su dawo suna

Amarya da Ango sai karb'an bak'i sukeyi masu zuwa ganin d'aki wasu kawai suzo suga gidan abunda ke kawo su kenan yara kuwa sai godiyar Allah duk wanda yazo gidan sai ya fita da k'unshin cincin da diblan

Aminan Aminu sun isa gida lahiya su da matan su sunata godiya da irin sha tara na arziki da Iyayen Aminu da shi kansa Aminun suka cika su dashi kamar kada su rabu haka sukeji

Aminu suna tacin amarcin su ruwa-ruwa domin masallaci ma Aminu da kyar yake iya fita Sam bayason abun da zai sa yayi nisa da matar sa a yadda sukeji ji suke kamar su had'iye junan su

*BAYAN KWANA BIYU*

Ango da Amarya zaune gaban Mahaifan Aminu nasiha suke ta masu daga bisani suka sanya masu Albarka sannan Aminu ya mik'a ma Inna leda cike da kaya haka ma ya mik'a ma Abba nashi ledan yace

"ga shi inji Nuriyya wai kunya take ta baku ayi hak'uri ba yawa"

Abba cikin sigar zolaya yace " sai kai ne mara kunya ka iya bamu ko?"

Dukkanin su kai dariya sannan suka tashi sukai masu sallama, Aminu yace " to mu muntafi sai da safen ku" yana mik'ewa yana magana,Amsa masu sukayi da "Allah ya tashemu lahiya" itama Nuriyya mik'ewa tayi tai masu sallama suka fice suka nufi gidan su

Bayan fitan su ne Inna ta bud'e ledar taga abun dake ciki atamface da takalmi sai hijabi da turare shima Abba shadda ne da takalmi sai sallaya da turare sukai godiya suna kara sanya masu albarka Inna tace "oh y'annan irin wannan abu raga-raga duk mu kad'ai Allah yayi Albarka ya k'ara had'a kawunan su

Daga nan gidan su Aminu gidan su Nuriyya suka wuce, nan ma kamar yadda suka baiwa su Inna haka suka basu suma da k'annen ta sai Albarka suke ta sa masu daganan gida suka wuce, soyayyar su tana burge y'an karkaran sosai

Yanzu Hankulan iyayen Aminu da Nuriyya ya kwanta ganin yadda suke kula da junan su ba wani sab'ani da ke shiga tsakanin su sai wanda ba'a rasa ba, tunda ko harce da hak'ori ana sab'awa

Yanzu Aminu tunda ya dage da addu'oin da Kaka Malam ya bashi bai kuma jin komai ba domin yaje Kaka Malam yace yace masa 'insha Allah komai ya wuce don ba abun da yafi k'arfin addu'a shine babban takobin mumini, kaka Malam ya k'ara da cewa kada kaga sun kyaleka kai ma ka watsar da addu'oi kamar wawtar da kayi da domin aljanu shu'umai ne barin ma bak'ak'en cikin su zasu iya yin komai don su cimma burin su don haka ka dage muma nan muna nan muna taya ku ' godiya Aminu yayi sannan yayi mashi sallama dama ya kawo masu Amarya ne su gaisa sunko sha nasiha sosai

_Vote_
_Comments_
_Share_
_And Follow_

*Muna Mugun Tare*🤝

*Taku Har Kullum*👱🏼‍♀

*_Star Nucee36O_*✨💫

RASHIN SANI NE SILA(Complete)  Where stories live. Discover now