page 1&2

2.6K 112 4
                                    

*TYPING*📲

💔👭 *HASSANA*  👭💔

                  *DA*

❣👭 *HUSSAINA*👭❣

*TARE DA ALK'ALAMIN HASSANA D'AN LARABAWA*✍✍✍

*LABARI AKAN WASU Y'AN BIYU ,LABARI NE ME TAB'A ZUCIYAR ME KARATU*


*DA SUNAN ALLAH ME RAHAMA ME JIN K'AI ,SARKI MABUWAYI ME GIRMA ,INA ROK'ON KA ALLAH KASA NAFARA LITTAFINNAN LAFIYA NA GAMA LAFIYA ,KUMA ALLAH KABAWA DUBUN DUBATAR MUTANE DAMAR KARANTA SHI DOMIN SU K'ARU DA ABINDA YAKE CIKINSA*


*MASOYA NA NADAWO GAREKU BAYAN HUTAWAR DA NAYI LOKACIN DA NA KAMMALA SANADIN HOTO ,DAFATAN WANNAN LITTAFIN ZAI KARB'U FIYE DA SANADIN HOTON ,SAI KU BINI DAN JIN WANNAN KARON WANE SAK'O NAKE D'AUKE DASHI*




SADAUKARWA

*KYAN ALK'AWARI CIKAWA ,GAREKI FATEEMA SARDAUNA MARUBUCIYAR (SHU'UMIN NAMIJI) ,FEJIN FARKO NA WANNAN LITTAFI NAKINE FATEEMA ,NAGODE DA K'AUNARKI GARENI ,HASSANA D'AN LARABAWA NA MATUK'AR K'AUNARKI ,KUMA INA GODIYA DA GUDUMMAWAR DA KIKA BANI ,ALLAH YA BARKI DA SARDAUNAN KI*🥰🥰🥰


*page 1⃣to 2⃣*






***Kamar kullum k'arfe 5:30 pm suka taso daga makarantar islamiyya dake can nesa da layinsu ,tafe suke a jere sanye da unifoam kalar green me haske Riga da wando da zumbulelen hijabi har k'asa ,sai nik'ab da suka sanyawa fuskarsu suka rufeta ruf ,k'afarsu sanye da safa bak'a da takalmi sau ciki irin na mata ,kafad'arsu rataye da jakunkunan su wadda ke d'auke da alk'ur'ani me girma da sauran litattafai na addini da tajweed.

         A nutse suke tafiya cikin takun natsuwa da hankali duk da suna saurin isa gida ganin yamma tayi sosai magriba ta kusa ,ta cikin nik'ab d'in fuskarsu suke magana da juna hannunsu sark'e da na juna kafad'arsu na gogar juna ,tsawonsu d'aya ,yanayin jikinsu d'aya ,sun kasance wad'anda basu cikin halittar mata masu tsananin k'iba ko tsananin sirantaka ,su d'in matsakaita ne da Allah yayi musu halitta me kyau da tsarin jiki me kyau duk da basu kasance da kyawu matsananci ba ,sai dai sunada kyawunsu dai dai misali.

     Hassana ce tak'ara damk'ar hannun hussaina ,sannan a hankali ta furta cewa .

      "My sister muyi hanzarin isa gida banason muna waje ayi kiran sallah ,yau Malam huzaifa ya tsayar damu wallahi ,nasan yanzu Baba yana gida yana tsumayin dawowar mu shida su Hamma.

    Ta cikin nik'ab d'in Hussaina tayi murmushi sannan tace "to ai rabin jikina kece bakida sauri wallahi ,jibifa yanda kike tafiya kamar bakyason taka k'asa ,amma tunda mun kusa k'arasawa karki damu kinji "

      Hassana tayi murmushi kawai ba tace komai ba, saboda batada yawan magana ,in kaga tana magana sosai to da Hussainar tane ko y'an gidansu .

           Dai dai wannan lokacin suka iso cikin layinsu ,mutane jefi jefi a gurare da dama nata haramar d'aura alwala domin isa masallaci Dan sallatar magariba .


      Zaune yake kamar kullum akan wani dakali na farkon shigowa layinsu ,sanye yake da k'ananan kaya bak'ak'e  da hula hana sallah , kasancewar sa fari tas sai kayan suka amsheshi yayi matuk'ar kyawu naban mamaki ..........yau ma taba ce sigari a hannunsa yana faman zuk'arta yana fesar da hayak'in cikin gwaninta da k'warewa,MUHAMMAD SAGEER KENAN.


Karyowar su cikin layin su yayi dai dai da sanda SAGEER yagama shan tabarsa sai wata Y'ar guntuwa a hannunsa ,a maimakon ya yarda ita a k'asa ya take ta sai yayi cilli da ita ,bata sauka a ko'ina ba sai akan hijabin Hassana da suke shigowa layin a dai dai wannan lokacin.

HASSANA DA HUSSAINA Where stories live. Discover now