page 53to 54

529 35 0
                                    

_________________________________

*TYPING*📲

💔👭 *HASSANA* 👭💔

                *DA*

❣👭 *HUSSAINA* 👭❣

*TAREDA ALK'ALAMIN HASSANA D'AN LARABAWA*✍✍✍


*page5⃣3⃣to5⃣4⃣*

WATTPAD:hassana3329

® _PEN : WRITERS  ASSOCIATION_
_________________________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~

https://www.facebook.com/groups/1061983803858837/











*TUNASARWA*👇

JARRABAWAR DA ZA'A YIWA MUMINAI

*AK'ARSHEN RANAR ALK'IYAMA KAFIRAI ZASUBI ABINDA SUKE BAUTAWA SAI SU KAISU HAR WUTA,JAMA'A JAMA'A TAMKAR GARKEN DABBOBI,ZASU SHIGA DA K'AFAFUNSU KO DA FUSKOKINSU,BABU WANDA ZAI SAURA SAI MUMINAI DA MUNAFUKAI ,SAI UBANGIJI YAZO MUSU YACE "ME KUKE JIRA ?SAI SUCE " MUNA TSIMAYAN UBANGIJINMU NE ,SAI SU GANSHI TA KWABRINSA IDAN YA YAYESHI ,SAI SU FAD'I SUYI SUJJADA ,SAI DAI MUNAFUKAI BAZASU IYA YIN SUJJADAR BA ,KAMAR YADDA ALLAH YACE "RANAR DA ZA'A YAYE GA BARIN KWABRI KUMA AKIRASU ZUWA SUJJADA BA ZASU IYABA", SANNAN SAI SU BISHI SAIYA SANYA SIRAD'I KUNA A GWADA MUSU HASKE.SA'ANNAN A D'AUKE HASKEN MUNAFUKAI*







*AIKI ME FALALA*👇


*DUK WANDA BURINSA SHINE LAHIRA ,TO ALLAH ZAI SANYA MASA WADATARSA A ZUCIYARSA ,KUMA SAI (ALLAH)YA TARA MASA K'ARFINSA A WURI GUDA ,KUMA DUNIYA ZATA ZOMASA ALHALI TANA K'ASK'ANTACCIYA ,ABISA DOLENTA*





SADAUKARWA GAREKU 👇

*Hassan (A T K)*

*Hussain (80k)*

*kamal (no love)*

ALLAH YASAKA MUKU DA ALKAIRI YABIYAKU DA ALJANNA ABISA K'OK'ARINKU GAREMU.






*INA TAYAKI MURNAR KAMMALA LITTAFINKI SISTER NABEELA DIKKO ,ME SUNA (TARBIYYA)ALLAH YABAKI LADAN FAD'AKARWA ,ALLAH KUMA YA YAFE KURA KURAN CIKINSA*🥰🥰🙏🙏










***Ana saura kwana d'aya tafiyar tasu duk shirye shirye sun kammala ,Hamma Sageer da Hussaina zasu fara yin gaba su sauka a hotel ,yayinda bayan kwana uku mamma zata bisu saboda ragowar shirin da bata k'arasa ba ...inyaso ranar da tabisu sai su tare agidan ta dake unguwar maitama a babban birnin tarayya Abuja .


Ranar gidan acike yake ,Adda Nabeela tazo ,ga sakeena da Sadiya ma sunzo ,hatta mummy Aisha da Ya Abdurrahman duk suna gidan ,Abdurrahman yana d'akin su safwan suna D'an tab'a hira dasu Babangida ...duk da bayajin dad'in zuciyarsa sosai ....amma yana yawaita addu'a shiyasa yasamu sauk'in damuwarsa.


Cikin gida kuwa sun taru akan Hussaina gabad'ayansu sunayi mata nasiha da fad'an zaman gidan aure, kowa yatofa albarkacin bakinsa sunata lallab'ata ,yayinda Hussaina ke kuka tamkar ranta zai fita ...duk wani kayanta da zata buk'ata an had'asu waje d'aya ,bawasu kayane masu yawa ba tunda Mamma tace akwai komai a can basai and'ibi kaya da yawa ba .


Magunguna iri iri masu kyau na gyaran jiki Aunty Sakeena tasa ta a gaba tana d'uramata amma Hussaina tak'isha ,ga garwashi a gefe anzuba wani turaren tsuguno me masifar k'amshi anyi anyi da ita ta zauna akan wata kujera ZA'A saka turaren k'ark'ashin kujerar yadda zai ratsata amma tak'i ,saida Aunty Sadiya taje takirawo Abdurrahman ,suka dawo d'akin tare ,yana shiga ya kalli Hussaina daketa shirgar kuka idanuwanta har sun nutse ciki Dan azabar kuka, matsanancin tausayinta ya kamashi,yasan tana cikin jarrabawa ,yaji tamkar ya rungumeta ya lallasheta ...amma yayi saurin tsarkake zuciyarsa da tunawa cewa yanzun tazama matar Amininsa tayi masa nisa na har abada ....

HASSANA DA HUSSAINA Where stories live. Discover now