page35to36&37to38

735 40 16
                                    

[1/30, 11:17 AM] Hassana D'an Larabawa🥰: _________________________________

*TYPING*📲

💔👭 *HASSANA* 👭💔

                *DA*

❣👭 *HUSSAINA* 👭❣

*TAREDA ALK'ALAMIN HASSANA D'AN LARABAWA*✍✍✍


*page3⃣5⃣to3⃣6⃣*

WATTPAD:hassana3329

® _PEN : WRITERS  ASSOCIATION_
_________________________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~

https://www.facebook.com/groups/1061983803858837/





*TUNASARWA*👇

*MANZON ALLAH (S A W)YACE "BAYA HALATTA GA MUSULMI MAI IMANI YA K'AURACEWA D'AN UWANSA MUSULMI SAMA DA KWANA UKU ,(MA'ANA YAYI GABA DASHI)DUK WANDA YA AIKATA HAKA,ZAI SHIGA WUTA KO YA MUTU*




*AIKI ME FALALA*👇

*MANZON ALLAH (S A W )YACE " BABU WATA RANA DA BAYI SUKE WAYAR GARI  FACE MALA'IKU GUDA BIYU SUN SAKKO ,D'AYANSU YACE "YA ALLAH KABAIWA MAI CIYARWA MAYEWA " D'AYANSU KUMA YANA CEWA "YA ALLAH KABAIWA MAI RIK'EWA MAMMAK'O (ASARA)*







****Hassana da Hussaina zaune cikin d'akinsu tare da Zahra takawo musu ziyara ,hirar su sukeyi da yadda za'a tsara biki a k'awatashi sosai ,Zahra tana ta ambato abubuwan da za'a gabatar a bikin, su dai dariya kawai sukeyi suna jinta.

       Hussaina ce tace" Zahra duk abubuwan da kike zayyanowa ba masu yiwuwa bane ,dan ko Baba ya yarda nasan Hamma sulaiman ba zai amince ba ...haka zaice albarkar auren ake nema ba yawan shirme ba "Hassana tace " abinda nakeson fad'a kenan sisina kika rigani ,koni ina bayan Hamma sulaiman ...bancika son yawan party a biki ba ,saboda wallahi duk anan ake zubarda albarkar auren, kiga aure da anyi anfara samun matsala, saboda mun bar fad'ar ma'aiki muna aikata son ranmu ",Hussaina ta gyara zamanta tana kallon Hassana tace " kin san kuwa yadda ya Abdurrahman yaci buri akan bikin nan ...!?ai wallahi yace dole ayi party a bikin mu ,yacemin fa abokansu dake k'asar waje ma zasuzo bikin ..."Zahra tayi shewa tace "wallahi inayin ya Abdurrahman ko garin ba kowa ...!ai ni ina bala'in son harkar rak'ashewa ...yama za'ayi ace za'ayi bikinku lami ...!?zan samu Aunty sakeena ta lallab'a mana Hamma sulaiman ya amince mu gwangwaje a bikin nan " Hassana ta tuntsire da dariya tace "kijawo mata matsala dai ...!na rantse akan hakan Hamma zai iya yimata yajin magana na sati guda..." Zahra tace "yaseen sai dai in bata lafe abinta a bed ba ...sanda zai amince bazaiyi shawara da kowa ba " Hussaina ta d'alawa Zahra duka a cinya tana dariya tace "bakida mutunci Zahra ,mu Hamman mu baya lafewa a bed " Zahra ta Sosa cinyarta ta kanne ido d'aya ta d'aga girarta tace "Allah ko. ..!?Ashe baya lafewa a bed ...!?inajin Aunty sakeena a ruwa tasamo sadauki da k'annensa ko ...!?sai Hussaina ta d'ora hannu aka tace " Zahra kinfi k'arfina ....na rantse Aure zamuyi miki kema ...tunda kin tafasa kafin ki k'one "Zahra ta juya idanu tace " aini aure ba yanzu ba sai nazama professor tukun ".


         A dai dai wannan lokacin wayar Hassana tayi k'ara alamar shigowar sak'o ,tana dariyar maganar su Zahra ta d'auki wayar tana dubawa sai taga Hamma sageer ne ya turo sak'on .


*Nakasa komai sweety ,ganinki kawai nake son yi wallahi ,ina waje kifito*


Fuskarta ta k'ara washewa da fara'a tanajin son Hamma sageer nakuma mamaye ruhinta ,kawai sai ta mik'e daman ashirye take tsaf da ita, illah turare da ta d'auka takuma fesawa ,sannan tazaro hijab d'inta wankakke gogagge tasa a jikinta.

HASSANA DA HUSSAINA Where stories live. Discover now