page49to50

532 30 1
                                    

_________________________________

*TYPING*📲

💔👭 *HASSANA* 👭💔

                *DA*

❣👭 *HUSSAINA* 👭❣

*TAREDA ALK'ALAMIN HASSANA D'AN LARABAWA*✍✍✍


*page4⃣9⃣to5⃣0⃣*

WATTPAD:hassana3329

® _PEN : WRITERS  ASSOCIATION_
_________________________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~

https://www.facebook.com/groups/1061983803858837/









*TUNASARWA*👇

TAFKI

*WANNAN TAFKI SHINE ALKAUSARA DUK WANDA YASHA DAGA CIKINSA BAZAI K'ARA JIN K'ISHI BA HAR ABADA,KOWANE ANNABI YANADA NASA TAFKIN AMMA TAFKIN ANNABI MUHAMMAD (S A W)YAFI GIRMA ,RUWANSA YAFI NONO FARI ,YAFI ZUMA DAD'I ,YAFI ALMISKI K'AMSHI ,ZASU SASHI DA MOD'A TA ZINARIYA DA AZURFA ,ADADINTA ADADIN TAURARI NE ,TSAWON TAFKIN YAFI NISA DAGA GARIN AILATU A JORDAN ZUWA ADAN,RUWANSA YANA TAWOWA DAGA KOGIN ALKAUSARA ,(WATO CIKIN ALJANNA)*




*AIKI ME FALALA*👇

*MANZON ALLAH (S A W)YACE "DUK WANDA YABADA KARIYA GA MUTUNCIN D'AN UWANSA ,ALLAH TA'ALA ZAI KAWAR MASA DA WUTA DAGA FUSKARSA RANAR K'IYAMA*










SANARWA

*Gareku wad'anda kukace kun dena karanta littafin nan saboda rasuwar Hassana ,shin kun manta ita mutuwa dolece ne ..!?nasan labarin akwai tab'a zuciyar me karatu sosai ,ammafa kusani  ko kalma d'ayace ta wuceka a littafin nan kayi missing ,idan nak'ara nausawa gaba akwai lokacin da zakuso karanta nabaya da ya wuceku ,Wanda nikuma babu Wanda zan turawa alokacin ,mutum ma idan yanajin sai a gaba zai karanta to yatarawa kansa,babu Wanda zan turawa a lokacin*



*HASSANA D'AN LARABAWA NA GAIDA MASOYANTA DA MASOYAN RUBUTUNTA ADUK INDA SUKE ,SAK'ONNIN KU NA FATAN ALKAIRI DA ADDU'AR KU NA ISKENI ,ALLAH YABAR ZUMUNCI DA ZAMAN TARE*







***Girgiza kanta takeyi cikin tsananin kuka da ciwon zuciya amma takasa magana ...hawayenta na tsiyaya akan hannun Abdurrahman Wanda shima zuciyarsa take bugawa da k'arfin gaske ....saida tayi namijin k'ok'ari sannan ta iya fizgo maganar da takeso tayi ....ta rik'e hannayen Abdurrahman k'am tace" Y'ar uwata tagujeni ta tafi ta barni a wannan lokaci ....kaima ya Abdurrahman zaka gujeni ....meyasa kukaimin haka ....ka tausayamin ya Abdurrahman kar kayimin haka ...ni ...."Abdurrahman ya katseta yace "wait tawan listen to me " da hanzari ta mik'e tsaye kanta na juyawa tace "me zaka gayamin ....!?mezan saurara naji .....!?yanzu na tabbatar ba sona kakeba tunda har zaka iya sadaukar da soyayyata ....daman wasa kakemin ko kuma yaudarata kakeyi kenan .....!?a rud'e yatashi ya zagaya gabanta duk yadda yaso ya hana hawayensa zubowa saida suka zubo ,durk'usawa yayi agabanta kansa a sunkuye yace " karki min wannan zargin please ,don't think of me as a player ,na rantse bantab'a kallonki da sunan yaudara ba ...kar ki manta ni d'an uwanki ne ...banida buri illah naga kin kasance cikin farinciki ...nidai kawai nayi niyyar yin abinda yadace ne ...kuma zancika alk'awarin zuciya ta da na Hassana "sai ya mik'e tsaye ya tsaya dab da ita har yanajin hucin zazzafan numfashinta dake fita ,Yakama hannunta yarik'e yana juyar da kanta zuwa b'arin da Sageer yake ya nuna matashi yace " kalli Sageer kiga yadda yakoma cikin kwana shida kacal adalilin rashin Y'ar uwarki ...dubi yadda ya lalace yafita hayyacinsa saboda tashin hankali da tunani ...ki amince ki tallafi wannan bawan Allah zaki samu lada ...kiyi k'ok'arin cikawa Y'ar uwarki burinta zatayi farinciki da hakan ...sageer yafini buk'atarki a halin yanzu ...please kiyi hak'uri da yadda kika samu kanki kowa da irin tasa k'addarar ....."Hamma Sageer ya mik'e tsaye yana layi tamkar ya zube k'asa ya k'araso gabansu ya tsaya shima ,cikin raunin zuciya da rud'ewa yafara magana "Abdurrahman kayi hak'uri bazan iya auren matar da kakeso ba ....kuma bazan iya auren kowace mace ba domin idan nayi haka naci amanar sweety na ...."Hussaina ma cikin kuka tace " yawwa Hamma Sageer kagayamasa gaskiya ....nima bazan iya auren burin Y'ar uwata ba ,idan nayi haka naci amanarta ..."

             Abdurrahman yayi murmushin takaici ya kallesu dukansu yaga basa cikin nutsuwar su ...ya juya ya kalli kowa dake falon duk sun zuba musu idanu wasu na hawaye yayinda wasu suka matse Kansu tsakanin cinyoyinsu suna kuka ...sai ya runtse idanu yace "lallai yau na tabbatar da cewa bakwa son Hassana kamar yadda take sonku ...Baku damu da ita ba kamar yadda tadamu daku ...kullum maganarta bata wuce Ku biyun nan amma kuk'i yarda kucika mata burinta ....!?da sauri Hamma sageer Yakama kafad'un Abdurrahman cikin wata irin murya da bata fita sosai yace " me kake fad'ane haka Abdul ....!?Abdurrahman ya k'ura masa idanu yace "abinda kunnenka yaji shina fad'a " Sageer yamatsa ya kwantarda kansa kan kafad'ar Sageer ya fashe da kuka yace "wallahi ina sonta ...na rantse ina k'aunarta kaima shedane Abdul...." Sai Hussaina ma ta kwantarda kanta a gefen d'aya kafad'ar Abdurrahman tana kuka tace "nima inason rabin raina ...ina k'aunar rabin jikina Ya Abdurrahman ....." Sai Abdurrahman ya zame jikinsa daga jikinsu yace "indai abinda ke bakinku shine a zukatanku ,toh Ku nuna mata k'aunarku ta hanyar cika mata burinta .....Ku auri junanku ...."

Yana fad'in haka yafice da sauri saboda kukan da yatawo masa ,bayason yayi kuka saboda zai k'ara raunata zuciyarsu ...shikuma k'warin gwiwa yakeson basu .....ya barsu a tsaye cirko cirko suna faman kuka da hawayen su .

           Baba ne yasa baki yayi kiransu ...duk suka d'ago kawunansu suna kallonsa hawaye na zuba ...yace "kuzo nan " suka fara tafiya har gaban Baba suka tsuguna ,yasa hannayensa yadafa kawunansu yace "kuyi hak'uri Ku yadda da k'addarar da ta sami rayuwar Ku ...kamar yadda Hassana tarok'i alfarmar Abdurrahmanu har ya amince yakamata kuma Ku sanyaya zukatanku Ku amince da jarrabawar ubangiji ....a ranar da tayi magana da Abdurrahmanu nima tayi magana dani nida yayanku Sulaiman ....tayimana maganganun da suka saka jikinmu sanyi Wanda tun alokacin nasan da k'yar idan ba rasuwa zatayi ba ...yawanci irinsu bayin Allah nagari Allah yana nuna musu alamomin mutuwa tun kan ta riskesu ....shawarata agareku kuyi hak'uri Ku karb'i jarrabawarku hannu bibiyu ....kuma kurage k'iyayyar da kuke nunawa junanku ...domin ko anan kunga ishara agurin Allah ...gashinan k'iyayyarku tana niyyar zama tsani zuwa ga auren junan Ku " Baba yamik'a hannu ya karb'i kud'in hannun Hamma Sulaiman ya dank'asu a hannun Hussaina yace "ga sadakin ki nan ...kamar yadda Abdurrahman yace insha Allah gobe iyanzu kinzama matar Sageer ,Dan haka tun yanzu Ku koyi juriya ..Ku koyi sarrafa zuciyarku ..a k'arshe inai muku wasiyya da kuji tsoran Allah aduk inda kuke ......!

Baba yana kammala maganar sa yamik'e domin fita daga d'akin ...sannan yabawa kowa damar fita, haka dukansu suka mik'e suka fita ,aka bar Hamma sageer shida Hussaina a durk'ushe cikin fitar hayyaci .

Hamma sageer kansa a k'asa hawayensa na d'iga akan kafet d'in d'akin ...jiyake inama ya mutu ya huta shima ...ta Yaya zai auri yarinyar da ko kad'an bata tab'a burgeshi ba ....!?ta Yaya zai auri macen da bai tab'a jin sonta ko misk'ala zarratin ba ...!?ta Yaya zai auri wadda ta tsaneshi a duniya fiyeda kowa ...!?ta Yaya zai iya rayuwar zaman aure da ita ...!?wace mummunar k'addarace take shirin afka masa ta auren Y'ar uwar sweetyn sa ....!?

  Ya d'ago yadubi Hussaina daketa faman kuka harda fad'uwa k'asa tana birgima sai kiran HASSANAr sa takeyi cikin raunin zuciya ...yaji kansa nawata irin sarawa tamkar ya zauce ...musamman da ya kalli fuskarta yaga tamkar sweetynsa yake kallo ....da hanzari ya mik'e yafice daga d'akin yana layi tamkar ya kifa ...ya tabbatar tsananin tashin hankalin da yake ciki k'ila zuwa safiyar goben shima zaibi sweetyn sa lahira .....!

Haka Hussaina ta kwana kuka da ciwon zuciya ,k'irjinta kamar ya tsage don ciwo ...kowa saida yagaji da rarrashinta banda Hamma Sulaiman da akabashi amanarta ...ranar agidan ya kwana tare da sakeenan da yaransu ,saboda addu'ar bakwai da za'ayi a safiyar ....

     Shima Hamma sageer hakance ta kasance dashi baiyi bacci ko na minti d'aya ba ,yadda yaga rana haka yaga dare....tunanin Hassana ya gallabeshi da ya rife idanunsa ita yake gani tanai masa  murmushinta me kyawun kallo da burgewa ....sai kurum ya mik'e ya d'auro alwala yafara jero salloli ....









***************




Ranar juma'a sati d'aya da rasuwar Hassana ,d'aruruwan mutane suka samu halartar addu'ar sadakar bakwai ,bayan an kammala addu'a aka d'aura auren MUHAMMAD SAGEER DA HUSSAINA ,Auren da yazowa jama'a a bazata saboda sauyin da sukaga ansamu ...maimakon Abdurrahman sai aka d'aura da sageer ,ana gama d'aurawa hawaye ya wanke fuskar Abdurrahman ,ya d'aga hannayensa sama hawayen na kwarara yace "nagodewa ubangijina da yabani damar cika alk'awarin Hassana da zuciyata ....Allah ka k'aramin hak'uri da juriya abisa wannan gingimemiyar sadaukarwa da nayi.....😭"






Comments
Share
Vote
Pls

















*HASSANA D'AN LARABAWA*✍✍✍

HASSANA DA HUSSAINA Where stories live. Discover now