page 11 to 12

779 52 0
                                    

*TYPING*📲


💔👭 *HASSANA* 👭💔

                *DA*

❣👭 *HUSSAINA* 👭❣




*TARE DA ALK'ALAMIN HASSANA D'AN LARABAWA*✍✍✍




*page 1⃣1⃣to 1⃣2⃣*


WATTPAD :hassana3329

*DEDICATED TO ALL MY FAN'S*🥰🥰🥰





*INA TAYAKI MURNAR SAMUN K'ARUWA K'ANWATA RAMLAT IBRAHEEM (HAJJA K'ARAMA)ALLAH YAYIWA BABY ABUBAKAR SADIK' ALBARKA YA RAYASHI BISA TAFARKIN MUSULUNCI DA IMANI TARE DA SAURAN YARAN MUSULMI ,KE KUMA ALLAH YA K'ARAMIKI LAFIYAR JIKI DA TA SHAYARWA*🙏🙏🙏😍😍😍






          ****Sosai sageer yake wani irin kallonsu ,idan ya kalli Hassana sai ya juya ya kalli Hussaina ,tunaninsa ya katse lokacin da yaji muryar Hassana me sanyin dad'i na gaida matar kusa dashi ......ta amsa tana cewa "nagode muku y'ammata " sannan tadubi Usman ta Shafa kansa tace "kaima nagode maka samari da ka rik'emin Muhammad d'ina .....may I know your name .....?ta tambayeshi cikin harshen turanci .

        Usman is my name " amma ana kirana autan Umma..... "yabata amsa yana mata murmushi ......sosai taji Usman ya kwanta mata a ranta shiyasa tai masa jinjina tace " good boy" ,you are a cleaver boy .

Aunty Nafeesa ce ta matso kusa ,sai Hassana ta gaisheta ,tayiwa sisinta alamun ta gaishesu itama ,......Hussaina ta matso ta gaidasu tanata hararar sageer ta k'asan ido ,yayinda sageer har lokacin bai fita daga mamaki ba .....

Hala Ku twins ne ....!?inji matar tana tambayar Hassana .......!naga kamar taku har ta b'aci wannan ai ba za'a iya bambance Ku ba ...

Usman ne ya amsa yace "eh twins ne ,ga Adda Hassana ....ya nuna Hassana ......" Ga kuma Adda Hussaina "ya nuna Hussaina da tafara gajiya da tsayuwar gurin sosai ....tun tana hararar sageer har tadawo hararar Hassana da Usman ....a ganinta duk sune suka tsaidasu .....

Masha Allah !abinda matar ta fad'a kenan tana dubansu .....Ai kuwa zan k'ulla zumunci daku ....naji ina sonku a raina ......ni mahaifiyar sageer da Nafeesa ce .....Anan kusa kuke ne ....!?

"Eh mamma " Kinga kidansu can fa .....anan layin suke.... Cewar Nafeesa tana nunawa mamansu gidan da hannunta .

Basu Ankara ba sai gani sukayi sageer yasaka kai zaiyi wucewar sa ,nan mamma tasaka baki tayi kiransa "Muhammad karka tafi .....pls kadawo Dan Allah ........Muhammad "

Ko kulata baiyi ba illah k'ara d'aga k'afa da yake Neman yi .....ba zato babu tsammani gaba d'aya sukaji muryar Hassana tace " Hamma sageeeeeeerrrrrr........"tawani ja sunan tamkar babu Wanda ya kaita iya ambatar sunan .

A wani irin slow ya juyo saboda muryar Hassana da ta zagaye jininsa ,kallonta yake idanunsa na lumshewa ,gaba d'aya fuskarsa babu annuri ,k'irjinsa na sama da k'asa alamun yana cikin b'acin rai sosai  .......Hassana bata cikin irin matan nan masu yiwa maza k'urulla ,amma batasan meyasa takasa dena kallon sageer ba ,wani dad'i takeji idan tana kallonsa .

Idanunta na kansa tabud'e baki da k'yar tace masa "Bakaji mamma na kiranka bane ....!?tundaga cikin gida fa tabiyoka tana faman kiranka kanak'in amsawa ....mahaifiyar kacefa .....haba Hamma sageer ....babu kyaufa mahaifiya na kiran d'anta yak'i amsawa ....kanason fad'awa cikin fushin Allah ne .....!?kasan kuwa aduk duniya idan kacire Allah da manzonsa bakada tamkarta a rayuwa .....ka amsa kiranta Hamma sageer ....kaje ka saurari batunta kaji .......kadena sakata cikin b'acin rai Hamma sageer pleaseeeee...

HASSANA DA HUSSAINA Where stories live. Discover now