page75to76&77to78

592 32 2
                                    

[3/13, 2:05 PM] Hassana D'an Larabawa🥰: _________________________________

*TYPING*📲

💔👭 *HASSANA* 👭💔

                *DA*

❣👭 *HUSSAINA* 👭❣

*TAREDA ALK'ALAMIN HASSANA D'AN LARABAWA*✍✍✍


*page7⃣5⃣to7⃣6⃣*

WATTPAD:hassana3329

® _PEN : WRITERS  ASSOCIATION_
_________________________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~

https://www.facebook.com/groups/1061983803858837/










*TUNASARWA*👇

*MANZON ALLAH (S A W ) YACE "YARDAR ALLAH TANA TARE DA YARDAR IYAYE ,DUK WANDA YAKE SON A FAD'AD'A MASA ARZIK'INSA ,KUMA AYI MASA JINKIRI CIKIN GURABUNSA(WATO A RIK'A TUNA WA DA SHI HAR BAYANSA )TO SAI YA SADAR DA ZUMUNCIN SA*









*AIKI ME FALALA*👇

*MANZON ALLAH (S A W ) YACE " KUNYA BATA KAWO KOMAI SAI ALKAIRI ,KUMA YACE "KUNYA TANA DAGA CIKIN IMANI ,KUMA YACE " ABUBUWA GUDA HUD'U SUNA DAGA CIKIN HANYOYIN ANNABAWA ,(SUNNONI)SUNE KAMAR HAKA*:

1, KUNYA
2, SANYA TURARE
3, YIN ASUWAKI
4, DA KUMA YIN AURE.







SADAUKARWA GA

*KANO WRITERS FANS ,INAJIN DAD'IN ADDU'ARKU GARENI DA KUMA JIN DAD'IN YADDA LITTAFINNAN YASHIGA RANKU KULLUM KUKE NEMANSA ,WANNAN SHAFIN NAKUNE KUYI YADDA KUKESO DASHI ,ANA KYAWUN TARE SISTER'S*🥰😘😍💃🏻🤝🤞








*BARKANMU DA JUMA'A SISTERS ,ALLAH YABAMU ALBARKACIN WANNAN RANAR ,GA GORON JUMA'A NAN NABAKU ASHA KARATU LAFIYA*😘🥰😍👇







***Girgiza kansa yayi yana sunkuyar da kan k'asa ,a hankali ya furta "babu komai mammana ....."

Kusa dashi ta samu ta zauna tana rik'o hannunsa da tsananta kallonsa ganin yadda duk yayi wani iri ,cikin murmushi tace "Akwai wani Abu Muhammad ,duk wata mahaifiya tana gane yanayin da d'anta yake ciki na dad'in rai ko akasin haka ,menene yake faruwa ......!?

           Yaso ya b'oye mata saboda baima San ta inda zai fara gayamata maganarba ,sai dai nacin da ta nuna akan tanason ji yabashi k'warin gwiwar fara magana ,kansa na k'asa ya ambaci sunanta " mammah...."
"Na'am Muhammad Sageer ...." Ta amsa tana duban kyakkyawar fuskar d'anta mafi soyuwa a zuciyarta ,
"Wani alk'awari na d'aukarwa k'anwar sweety Wanda bazan iya cika mata shiba, harshena ne yayi azarb'ab'in furtawa ban Ankara ba mamma ....."

Har lokacin fuskarta cikin walwala take ,ta shafa kansa tace "babu kyau karya alk'awari Muhammad ,indai kanada yadda zakayi ya kamata kacika mata alk'awarinta ...domin rashin cika alk'awari yana daga alamomin munafuki da aka zayyana ..."

Yayi shiru k'irjinsa na bugawa yana Dana sanin furta alk'awarin ,har saida mamma tace "meyasa kayi shiru ...!?kayi magana kaji Muhammad ,
D'agowa yayi ya kalleta ya girgiza kansa sannan yace " banida ikon cika wannan alk'awarin ne ,domin idan zan cikashi zan sab'awa wadda banida kamarta duk duniya ...!?idonta na cikin nasa tace "wacece wannan ....!?tana direwa ya amsa cikin karsashi " mahaifiyata ....."wani irin lumshe idanu mamma tayi saboda jin dad'i tana k'ara k'ank'ame hannun sageer d'in a hannunta tace "me yakawo mahaifiyarka acikin alk'awarinka ....!?

             Ya kuma yin k'asa da kansa yana Jan numfashi yace " nayiwa mahaifiyata alk'awarin binta Abuja nida matata idan an d'aura mana aure, yayinda nayiwa k'anwar matata alk'awarin zama anan ba tare da tafiya Abuja ba saboda buk'atar ranta da son in kyautata mata ,Ashe ban saniba nayi kuskure Mammana ,buk'atar mahaifiyata itace gaba da komai ,Dan haka dole na zab'i alk'awari d'aya na cika na kuma yi watsi da d'aya alk'awarin duk da nasan akwai laifi a kaina "ya d'ago yana kallonta yayinda itama d'in fuskarsa take kallo cikin wani yanayi ,ya cigaba da cewa " ni Muhammad Sageer nazab'i alk'awarin mahaifiyata a matsayin Wanda zan cika ......"

HASSANA DA HUSSAINA Where stories live. Discover now