page 19to20

627 50 0
                                    

*TYPING*📲


💔👭 *HASSANA* 👭💔

                 *DA*

❣👭 *HUSSAINA* 👭❣



*TARE DA ALK'ALAMIN HASSANA D'AN LARABAWA*✍✍✍



*page 1⃣9⃣to2⃣0⃣*



WATTPAD:hassana3329


*GODOYA ME TARIN YAWA ZUWA GAREKU*👇

*NAGODE DA ADDU'AR KU MASOYA NA ,YAWAN ADDU'AR KU DA FATAN ALKAIRI HAR HAWAYEN MURNA YA SAKANI ,INAJI DAKU A RAINA DA WANDA NASANI DA WANDA BAN SANIBA ,ALLAH YACIGABA DA DAFA MANA AKAN AL'AMURAN MU NA KO YAUSHE*


*TUNASARWA*👇

*MANZON ALLAH (S A W ) YACE "LALLAI NAGA WANI MUTUM YANA JUJJUYAWA (WATO YANA KAIWA DA KAWOWA)A CIKIN GIDAN ALJANNA ,SABODA WATA ITACIYA DA YA D'AUKE TA DAGA KAN HANYA ,WACCE TA KASANCE TANA CUTAR DA MUTANE*



*AIKI ME FALALA*👇

*MANZON ALLAH (S A W ) YACE" MALA'IKU SUNA YIN SALATI GA D'AYANKU ,MATUK'AR YANA WURIN DA YAYI SALLAH ,KUMA MATUK'AR BAIYI HADASI BA (WATO BAI KARYA ALWALARSA BA ,SUNA CEWA "YA UBANGIJI KA GAFARTA MASA ,YA UBANGIJI KAYI MASA RAHAMA*






               Ba mamma ba hatta Aunty Nafeesa saida ta razana jin maganar Hassana ...gabad'aya suka zuba mata idanu jikinsu na rawa ....Aunty Nafeesa ce tayi k'ok'arin matsowa ta dafa kafad'ar Hassana a hankali tace" yanzu bazaki iya  taimakon mu ba Hassana ...bazaki share mana hawayen mu ba ...!?a hankali Hassanar ta d'ago da kanta ta kalli mamma da gabad'ayan ta takoma kalar tausayi ...sannan ta juya ta dubi Aunty Nafeesa da ke faman kallonta tace "ba nufina bazan taimaki mamma ba ....ah ah ...ina nufin bazan iya barin Hamma sageer cikin wannan halin ba ....zanyi k'ok'ari da jajircewa da addu'a Dan ganin yafita daga wannan halin .....labarin yak'ara tabbatar min da ingancin Hamma sageer ....kuma insha Allahu zan kasance sila wajen juyo da akalar Hamma sageer da taimakon rabbil izzati Aunty Nafeesa ...." Sannan tajuyo ta dubi mamma da furucin Hassana yasata shauk'i a ruhinta ta yadda fuskarta ta kasa b'oye murnar ta ...sosai Hassana ta duk'ar da kanta ta na wasa da yatsun k'afarta sannan ta bud'e baki a hankali tafara magana "Mamma naji labarinku me cike da abubuwa iri iri ....labarinku yana d'auke da darasi da tsoratarwa da tausayi da kuma raunata zuciya ....na rantse banta b'a cin karo da labari me kama da shiba ....a sanda kike bani labarin tamkar almara nake jinsa ....bantab'a tunanin zaki iya aikata hakaba ...Ashe dai mutanen cikin duniyar halayensu mabambanta ne .....!?Ashe da gaske akwai mata masu wulak'anta mazajen auren su .....!?Dole ne sageer ya tsani mata ya dinga kallon mu a bai bai ....Mamma kinyi kuskure ba k'arami ba ....sai dai baki makara gurin tuba ba idan har ya kasance taubatan nasuha zakiyi .... Manzon Allah (S A W )  yace " kowane d'an Adam yana kuskure ,amma mafi alkairin masu kuskure sune masu tuba "

            Idan mukayi duba da wannan hadisin zamuga Allah yana sonki da Rahama mamma shiyasa har yasa kika gane kuskurenki kika tuba kike Neman gafara a gurin Allah ......amma fa kisani Mamma Allah baya yafe laifin bawa akan bawa ,matuk'ar ba bawan ne ya yafe laifin ba ...duk da ina kyautata zaton daddy ya yafemiki kodan mafarkin da kikeyi dashi ....shawara ta agareki mamma itace kidage da yiwa daddy sadaka da addu'ar samun rahama.... Ki kuma k'ara kyautata tubanki ta hanyar istigfari da salatin Annabi da ambaton Allah a ko yaushe .....Batun Hamma sageer kuma kibar komai a hannuna .....amma dai ina buk'atar addu'ar Ku wadda zata zamemin jagora gurin tunkarar sa ....."

Mamma da hawayen ta ta sakko k'asa ta rungume Hassana ...godiya kuwa saida Hassana tasa hannu ta rufe bakin mamma sannan mamma d'in tayi shiru ....Aunty Nafeesa ma kallon Hassana takeyi da wata irin k'auna ...da hawayen ta ta furtawa Hassana cewa "Na rantse kinada kirki da mutunci Hassana ...ilimin ki da halayenki sun dace dake ....godiyar mu GAREKI bazata yanke ba ....mungode Hassana "

HASSANA DA HUSSAINA Where stories live. Discover now