page 43to 44

573 42 5
                                    

_________________________________

*TYPING*📲

💔👭 *HASSANA* 👭💔

                *DA*

❣👭 *HUSSAINA* 👭❣

*TAREDA ALK'ALAMIN HASSANA D'AN LARABAWA*✍✍✍


*page4⃣3⃣to4⃣4⃣*

WATTPAD:hassana3329

® _PEN : WRITERS  ASSOCIATION_
_________________________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~

https://www.facebook.com/groups/1061983803858837/




*TUNASARWA*👇

TAFIYA TA DIN DIN DIN

*K'ABARI SHINE MATAKIN FARKO DAGA CIKIN MATAKAN LAHIRA,RAMI NE DAGA CIKIN RAMUKAN WUTA DANGANE DA KAFIRI DA MUNAFUKI ,AMMA DANGANE DA MUMINI,DAUSAYI NE NA ALJANNA,KUMA AN RAWAITO CEWA ,ANAYIN AZABA ACIKINSA SAKAMAKON WASU LAIFUKA ,DAGA CIKINSU AKWAI*:

RASHIN TSARKAKA YAYIN FITSARI
YAD'A ANNAMIMANCI
BARIN SALLAH SABODA BARCI DA GANGAN
K'AURACEWA ALK'UR'ANI
ZINA DA LUWAD'I
DA SAURANSU .

*KUMA DAGA CIKIN ABUBUWAN DA SUKE TSERARWA DAGA AZABAR K'ABARI AKWAI*:

KYAWAWAN AYYUKA DA AKAYISU SABODA ALLAH
NEMAN TSARI DAGA AZABAR K'ABARI
KARANTA SURATUL MULK
DA SAURANSU.

*DAGA CIKIN WAD'ANDA AKE KARESU DAGA AZABAR K'ABARI AKWAI*:

SHAHIDI
WANDA YA MUTU WAJEN D'AUKAKA KALMAR ALLAH
MUMININ DA YARASU RANAR JUMA'A
WANDA CIWON CIKI YAYI SANADIN MUTUWARSA
DA SAURANSU.


*AIKI ME FALALA*👇

*MANZON ALLAH (S A W )YACE "DUK WANDA YA HALARCI JANA'IZA HAR AKAYI MATA SALLAH ,TO YANADA LADA KAMAR (KIRADI)D'AYA ,KUMA DUK WANDA YA HALARCETA HAR AKA BINNETA YANADA LADA KAMAR (KIRADI )BIYU,SAI AKACE :KAMAR YAYA KIRADI BIYU YAKE?SAI MANZON ALLAH (S A W)YACE" MISALIN DUWATSU GUDA BIYU MANYA MANYA.(ABDULLAHI D'AN UMAR )YACE"LALLAI MUNYI SAKACI DA (KIRADODI )DA YAWA*





🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏





***Suka isa gareta a tare kowa na k'ok'arin rik'eta ,wani mugun kallo Hamma sulaiman yabita dashi ya daka mata wata muguwar tsawa yace "matsa daga nan kafin na tattaka ki wallahi " nan da nan tafashe da wani irin kuka takasa matsawa  daga gurin illah rik'e hannun Hassana da tayi tsam ,Hamma sageer kuwa yana isa ya zube a gaban gadon ya d'ora kansa gefen cinyar Hassana yana wata irin ajiyar zuciya hawaye na malala akan fuskarsa ,yanajin zuciyarsa tamkar tafaso k'irjinsa tafito .

Tarin ya tsagaitawa Hassana ,idanuwanta har sun birkice saboda tsananin wahala amma haka tasa hannu ta kamo Hussaina ta kwantar da kan Hussainan akan k'irjinta daga gefe ,abinda bata tab'ayi ba shi tayi ,wato tasaka hannunta akan kan Hamma sageer tana k'ok'arin d'agoshi ,yana d'agowa taga yadda yake kuka saita girgiza masa kai tayi murmushi me ciwo tana kallon karyayyen hannunsa ,muryarta da rauni tace "nasan da kaida sisina zakufi kowa kokawa a y'an kwanakin nan ,gashi nikuma babu abinda banason gani irin hawayenku ,akwai babban al'amari da zai riskeku Wanda Allah ya kimsamin shi a zuciya ta ,Allah yasani bana ganin laifinku abisa k'in da kukewa juna ,sai dai kuma banida burin da yawuce a duniya yau naganku kundena k'in juna ,tun randa mukafara ganinka da sisina bantab'a d'ora goshina ak'asa ba face sainayi addu'ar Allah ya daidata tsakaninku cikin aminci " ta D'an numfasa yayinda duk mutanen d'akin suke zubda hawaye kowa jikinsa yayi sanyi ,takuma yunk'urawa tana son tashi, Hussaina ta d'agamata k'irji tanata kuka ,Hamma sulaiman da kansa ke masifar juyawa ya gyara mata zama ajikinsa ,saita kalli Hamma sulaiman tayi murmushi tanajin cikinta na azabar ciwo tace "D'an uwana in baka wata Amana...!? Yabita da idanuwa ya kasa magana ,gabad'aya Hamma sulaiman baya cikin hayyacinsa har wata rama yayi a ranar ,sai ta kamo hannun Hussaina da Hamma sageer ta had'a ta dank'asu a hannun Hamma sulaiman tace " Na amince dakai Hamma sulaiman ,shiyasa zan baka wannan amanar ,wad'annan mutanen ina sonsu fiyeda rayuwata ,don Allah Hamma sulaiman ka kula min dasu aduk lokacin da bana tare da su ,ko idan nayi wata tafiya me nisa ,kar ka barsu suyi kuka ,kar ka barsu susha wahala ,karka kuma dukan sisina ,idan tayi laifi kayi mata Nasiha ,sannan ka kula min da tarbiyyar Hamma sageer ,aduk lokacin da akaga zai kauce hanya adawo dashi dai dai... kar a hantareshi... kar a k'yamaceshi ,akula dashi kamar yadda za'a kula da k'aramin yaro ,inason Hamma sageer sosai ,amma Allah shi yabarwa kansa sanin ya zaiyi da Hamma sageer da sisina,na rok'eka Hamma sulaiman ka rik'emin amanata ,wad'annan mutanen sune amanata agareka .

HASSANA DA HUSSAINA Where stories live. Discover now