Sha Tara

1.6K 225 12
                                    

Tunin Akan Inda Aka Tsaya: Ramlah, Lubnah da Rayyan sunje gidan amarya Zainab inda suka hadu da Yassar ya tabbatar mata da bashi bane mijinta har ta suma a hannun Rayyan.

Cigaban Labari:

Kara tallabota yayi zuciyarshi na dukan ukku dan tsoronshi bai wuce ace daga haka Ramlah ta rasa rayuwarta ba. Da hanzari ya karasa da ita kan kuraje su kuma sun raja'a kanshi. A hankali ya kwantar da Ramlah yayi baya yana kallon fuskarta, Lubnah wacce duk wanda ya kalleta yasan rike kukanta take ta tsaya a gefenshi, "Rayyan meke damun Ramlah? Da ranta ko?"

Zainab ce tayi karaf ta bata ansa, "Haba Lubnah, suma fa tayi ba wani abu ba..." sai a lokacin su dukansu hankulansu suka dawo suka kuma san abunda ya kamata suyi. Ko kafin ta farka saida suka tabbatar Yassar ya tafi dan ganinshi a wajen ba karamin kara dagula alamarin zaiyi ba. Hakuri Rayyan yake ta bashi shi kuma yana fadin babu komai kafin ya masu sallama ya wuce.

Waje Rayyan ya samu ya zauna yana kallon yanda Zainab da Lubnah ke kokarin taimakonta har aka samu ta farka idanunshi kyam saman fuskarta. Da kuka ta farka, tana bude idanta taga Lubnah nan take ta rungume ta jikinta babu inda baya rawa. Da kyar da lallashi Lubnah ta samu ta daina kukan har zuwa lokacin kuwa Ramlah ko kallon inda Rayyan yake zaune batayi ba.

Ta daina kukan ne bawai dan wutar dake kunar zuciyarta ta kare ba, saidan gidan mutanen da suka ciki, yana kallon fuskarta yasan hakan shine kadai dalilin zubar kwallarta amma ga kunci nan kwance malemale saman fuskarta. Zainab ce ta musu tayin abinci amma Rayyan yace Aa, dan kawo yanzu kalilan mintuna ne ya rage masu inba haka ba zasuyi missing flight dinsu.

Da mijin Zainab suka tafi yanda zai mayar da motar gidansu. Har suka koma hotel, Lubnah ta dauko masu kayansu sannan suka wuce airport Ramlah ko kallon Rayyan batayi ba, karshe ma daya juyo baya zata rufe idonta kamar tana bacci wanda kowa yasan bashi take ba. A haka jirginsu ya tashi babu umm bab um um saidai dukda bata kuka da kaga fuskarta kasan tana cikin kunci.

Ita dai Ramlah zaune take cikin mota tana kallonsu amma kwata kwata batasan abunda takeji cikin zuciyarta ba. Ga kunci nan kwance, tabbas. Sannan kuma ga wani abu mai kama da saukar damuwa ga kuma rashin tabbas. Tasan kuncin ko na menene, Abban Hanan da ta dauka da shi amma yace mata bashi bane ba. Sai kuma taji sauki a ranta dan da ace shine to ya zatayi? Me zasuyi? Da aurenshi kanta ko kuwa babu? Ga ko konta, dan har yanzu tanajin kamar shi amma ta riga ta masu alkawari bazata sake tunanin shi ba. Maganarshi ba.

Suna isa gidan Mama ta fita zataje taron su na yan siyasa, tana ganin yanda Ramlah ta fito daga motar da hanzari ta rungume ta, "Ramlah ince dai lafiya?" Kokarin yi mata murmushi takeyi amma sam ta kasa saidai ta girgiza kai, "Lafiya lau Mama. Mun sameku lafiya?"

Hannayen Mama saman kafadunta ta girgiza kai, "Aa ba lafiya ba," magana take kafin ta daga kai ta kallesu sai taga suma fuskarsu babu walwala, "Kai karku tsorata ni, lafiya?" Sai a lokacin Ramlah ta daure ta kakaro murmushin, "Allah Mama lafiya lau, gajiya ce kawai fa ba wani abu ba." Dakyar suka samu Mama ta yarda babu wani abun kafin ta wuce da alkawarin bazata dade ba zata dawo taji meya faru.

Saida Lubnah ta tabbatar tayi wanka ta fara sallah kafin ta wuce nata dakin. Zama Ramlah tayi saman sallaya tana kallon zanen dake jiki, taki yarda kwakwalwarta ta tariyo mata abunda ya faru yan awanni kalilan da suka wuce, a hakan ma a barta a haka ta gode. Hawaye taji suna neman sauko mata amma da hanzari ta goge su, tama kanta alkawari ta daina kukan, amma kam zuciyarta na cikin kunci.

Kwankwasa kofa taji anyi dakyar ta samu labbanta suka iya furta, "Shigo." Lubnah ce sanye da doguwar riga da alama itama tayi wanka tayi sallah. Zama tayi gefen gadon tana kallon Ramlah da tausayi akan fuskarta. "Ya kikeji, Ramlah?"

Dole dan karamin murmushi ya subuce mata, dan yanda Lubnah tayi maganar kamar wacce zatayi kuka. "Lafiya lau nake mana, Lubnah. Kawai dai zuciyata kamar an hura mata wuta amma nan da kwana biyu nasan zata warware."

MIJINA NE! ✅ Where stories live. Discover now