Hudu

1.9K 251 7
                                    

"Ramlah! Ramlah!" Lubnah ce ke kiran sunanta a kidime tana jijjigata. Amma idanun Ramlah kyam tamkar wacce ake zare ma rai. Ramlah rugawa tayi da gudu ta kira Mama sukazo a inda tabar Ramlah a sandare waje daya haka suke iske ta, amma koda Mama ta duba sai taga bawai ta rasu bane.

"Gaggauta ki kira Doctor, Lubnah! Yi sauri kinji?" Ita sai a lokacin ma ta tuna indai babu lafiya to likita ake kira. Hankali tashe ta ruga dakinta ta dauko wayar kafin ta danna ma abokinta Dr Mahmud kira. Dakin ta koma kafin a hankali ta fara fada mashi abunda yake faruwa, cewar tazo dakin ne taga Ramlah tana kuka daga nan kuwa komai nata ya tsaya cak.

Dakyar yana fada masu ynda zasuyi har suka samu Ramlah ta farfado. Tana farfadowa kuwa ta fara kuka tana kiran sunan Hanan. Dama yana hanyar zuwa gidan, yana zuwa yai mata allurar bacci suka fita daga dakin. Mahmud juyawa yayi ya kalli Mama, "Mama ina ganin sai ta fara zuwa therapy gaskia. Inba haka ba gaskia damuwar da take ciki zai iya haifar mata da babbar matsala, dan zuwa yanzu jinin ta ya hau sosai ma ba kadan ba." Psychologist ne shi, hakan ya kara kwantar masu da hankali nan suka gama magana da Mama akan idan an samu ta dan marmaro zasu mata magana sai ta fara zuwa therapy din.

Ranar Lubnah a dakinta ta kwana, duk motsi daya sai ta juya ta kalli Ramlah tana tunanin ko wani abu ya kara faruwa. Da safe kuwa tashi tayi taga Ramlah zaune kan gado ta jingina da bangon gado ta zura ma bango ido kamar wacce taga fatalwa. Baka ganin digon wani yanayi a fuskarta. Tamkar bango haka. Babu kunci ko farin ciki tattare da ita. Ita dai gata nan kawai, kamar mutum kuma ba mutum din bace.

Da addua bakinta Lubnah ta zauna kusa da ita tana kamo hannayenta. "Ramlah dan Allah ki rika sassauta ma kanki kinji? Kowa fa da yanayin yadda Allah yake jarabtarshi, Ramlah. Idan kikace zaki tsaida rayuwarki gaba daya to me kika yima Allah kenan? Butulci ko rashin godiya? Daya barki da ranki ma da lafiyarki ai ba karamin gata Allah ya maki ba, Ramlah. Wata biyu kenan fa kina cikin gidan nan amma maimakon ma damuwar da kike ciki tayi sauki kullum kara gaba takeyi, dan Allah kiyi hakuri kinji?"

Juyowa tayi ta kalli Lubnah kafin a hankali ta daga mata kai, "Nagode, Lubnah."

Lubnah mikewa tsaye tayi, "Yanzu ki tashi kiyi wanka, yau asibiti zamuje kinji?" Batayi mata gardama ba ta sauko daga kan gadon tana dan layi. Ko da Lubnah tayi kokarin taimaka mata cewa tayi zata iya. Bandaki ta shiga tayi wanka kafin ta fito ta shirya tsaf. Tunda tazo rabon data fita daga cikin dakinta har ta manta, kullum saidai a kawo mata abinci, abincin ma ba ci takeyi ba saidai Lubnah tazo ta sakata gaba ko Mama.

Lubnah ce ta kwankwasa kafin ta bude kofar ta tsaya bakin kofa, "Ki sauko muci abinci sai mu wuce ko?" Fitowa tayi suka sauka kasa a tare. Babu umm babu um um tun lokacin data gaishe da Mama. Da hanzari sukaci abincin suka tashi saboda kar Lubnah ta makara a wajen aiki.

Babban psychiatric hospital sukaje, itadai Ramlah nata idone kawai. Har suka kai office din Dr Mahmud bata dago ba, idanunta kasa kyam bata dago ba saida suka shiga suka zauna. Bayan sun gaisa ne Lubnah ta mike tsaye, "Mahmud dan Allah idan kun gama ka kirani na aiko driver yazo ya dauketa kaji? Inada meeting ne bazan iya jira ku gama ba."

Juyawa tayi ta kalli Ramlah, "Na tafi Ramlah, sai mun hadu a gida ko?" Da dan guntun murmushin yak'e Ramlah ta daga mata kai tana fadin "Allah ya tsare." Wanda dakyar ake jin abunda take furtawa.

Tana fita hankalin Mahmud ya dawo gareta, "Sannu Ramlah, ya kikejin jikin naki?" Dagowa tayi sau daya ta kalleshi kafin ta dauke idanta.

"Da sauki, Alhamdulillah." Tun daga nan duk abunda zaife bata bashi amsa ba. Har ya gama surutunshi yana yan tambayeshi tambayenshi kafin can taji ya kira Lubnah akan ta aiko drivern ya dauketa. Da kanshi ya rakata harabar asibitin kuma ya jira har saida drivern yazo daukarta tukunna ya mata sallama da cewar sai ta dawo gobe.

Da yake drivern me surutu ne, babu irin yanda baiyi ya jata da labari ba amma daga yadda take kallo titi idanunta ko kyaftawa basuyi ya nuna cewar bata san inda hankalinta yake ba, dan dole yayi shiru ya kyaleta. Suna isa gida ta fito daga cikin motar tana fadin, "Nagode."

Tasan dai tafiya take amma har rantsewa zata iyayi akan batayi karar sautin horn din motarshi ba. Sai can taji karar tsayuwat mota da hanzari alamar an kusa bugeta. Fitowa Rayyan yayi cikin mota yana kallon yanda har yanzu a natse take idanunta na kallon kasa, kafin ta daga kafa daya sai an dauki lokaci. Miye ma sunanta? Shi yama manta.

A hankali ta dago ta kalleshi bayan ya fito daga motar ya tako har inda take, "Yi hakuri dan Allah, ban lura bane." Tana furta hakan ta kara gaba ta barshi nan tsaye. Shi kam da ido ya bita yana mamakin wannan matar. Zai iya cewa tun ranar da Lubnah ta dawo ya ganta bai kara ganinta ba sai yanzu. Wannan wace irin mutum ce ita? In har a cikin gida sai an kusa banke ta to idan ta fita kan titi ya kenan?

Bai ce komai ya koma cikin motarshi ya tada ya fita daga gidan gaba daya. Ramlah daki ta koma, batajin komai a zuciyarta amma koda numfashi sai tayi da gaske take fizgoshi ya fito. Nauyin da zuciyarta ta mata kuwa tana jinshi har kasan bargonta. Hakarkarinta har wani zafi suke idan tayi numfashi. Tasan haka Allah yake san ganinta, amma kuma ta rasa inda zata saka ranta. Wani lokacin ji take da ita idan mutum ya kashe kanshi baida zunubi da Ita Ramlah babu abunda zai hanata daukar ranta.

*

Tana fitowa daga bandaki taga Lubnah zaune kan gadonta tana latsa waya tana dan murmushi. Zama tayi kan gadon kafin Lubnah ta dago tana kallonta, "Na shigo naji kina bayi nace bari in jira ki fito. Ya kike?"

Ramlah ce tayi murmushi tana dan daga mata kai, basai ka santa zaka gane cewar wannan murmushin na karya bane ba, kawai yinshi tayi dan kar ace batayi ba. "Lafiya lau. Har kin dawo aikin ne?"

Yar dariya Lubnah tayi, "Kai Ramlah, dare fah yayi, yaushe na taba kaiwa dare? Kawai dai shigowa ne banyi ba tun dazu nace kar in takura maki."

"Allah sarki, to ya aikin?" Daurewa takeyi tana yar maganar nan, dan kuwa ta tabbata Lubnah bata san ganinta ta dinke duniya kamar yanda takeyi.

Da murmushin jin dadi Lubnah ta daga mata kai tana kara mikar da kafafunta a kan gadon. "Wallahi lafiya lau in fada maki. Amma kinsan me?"

Gyara zamanta Ramlah tayi tana girgiza kai, "Aa, meya faru?" Yanda take maganar ita har mamaki abun yake bata ma. Ta dade bataji tayi magana kamar ta yau ba, dukda cewar cikin sanyin rai take maganar kuma duk wanda yajita sai yagane tana cikin tarin damuwa.

"Ashe ba haka nan Mama ta dage sai Rayyan yazo gidannan ya zauna ba. Kin sanshi ko? Wannan wanda mukaci abinci tare dashi ranar da mukazo nan." Dan jim kadan tayi kafin tayi tunani, ko shine wanda ya kusa bigeta cikin gida yau? Shi dinne ma.

"Eh nagane shi. To saboda me?" Ta tambaya a hankali. Ita kuma Lubnah ganin yau ta dan tsaya ana magana da ita ba karamin dadi taji ba.

Yar dariya tayi kafin ta bata amsa, "Wai ita da babanshi aure sukeso su hadamu. Kuma nidai toh..." kafadunta ne suna dan fada a hankali kafin ta rufe fuskarta gaba.

Abun sai ya burge Ramlah bata san lokacin da tayi murmushi me hade da dariya ba. Ita har mamaki ma ya bata, "To kodai kina sanshi dama, Lubnah? Irin wannan murmushi haka kamar ance maki gobe daurin auren?"

Da hanzari Lubnah ta dago kai jin yadda Ramlah take magana da murmushi hade da zolaya. "Ke wallahi ba haka bane, nidai kawai. To yana dan burgeni, irin yanda yake abubuwan shi. Ba wani magana muka cika yi dashi ba amma yana da kirki. Ni banma so in fara sanshi."

"Ban yarda da maganar nan ba. Sanshin dai kikeyi. To Allah ya zaba mafi alkhairi. Allah ya dawwamar da farin ciki a rayuwarki." Ramlah ta fada tana fadada murmushinta. Bata da kowa amma Lubnah ta kasance komai nata yanzu, dan haka babu wanda take burin ganinshi cikin farin ciki kamar Lubnah.

"Ameen Ameen. Kema haka. Ya kukayi da Dr Mahmud? Ban samu na kirashi inji ba." Koda Lubnah tayi maganar sai taji dama batayi ba, dan sai ya kasance tamkar ta tunatar da Ramlah halin rayuwar da take ciki. Nan da nan kuwa murmushin dake fuskarta ya dauke saidai kawai ta girgiza kai alamar ba komai.

Dakyar Lubnah ta samu suka danyi fira kadan kafin ta mata saida safe tana tafiya dakinta. Amma a ranta babu abunda take buri face ace yau Ramlah Allah ya yaye mata duk wata damuwa da take ciki.

MIJINA NE! ✅ Where stories live. Discover now