Arba'in Da Shida

1.4K 206 23
                                    

A hankali take bude idanta, tunani ta fara a hankali komai ya dawo mata cikin kai. Nan take wani irin bakin ciki ya mata dabaibayi a zuciya tunani take yanzu ta ina zata fara zama da wannan mutumin? Yunwar data kwana da itace take neman ruda ta, duk yanda Ramlah taso ta kwanta tayi tunanin mafita kasawa tayi, da rigar baccin jikinta ta fita parlour. Ita duk daukarta ma yana wajen aiki, tunda ai sai aure yayi dadi ake wani daukar hutu ko? Dan tanada tabbacin yasan wannan kaddararren auren nasu wahala kawai zaisha ba komai ba.

Zuwa tayi zatayi hanyar kitchen taga har anyi girki an jera komai saman dining table, wani irin yatsina fuska tayi, ita koma mai zaiyi bazai taba burgeta ba. Dama tayi brush dinta already, zama tayi ta fara zuba abincin a hankali tana tunanin yanda zatayi. Ko ta kira Lubnah? Amma idan ta kirata ya zata ce mata? Ai da kunya wannan irin cin amana haka.

Takun tafiyarshi taji amma ko dagowa batayi ta kalleshi ba, da murmushi kan fuskarshi ya zauna kan kujerar dake kusa da tata. Mamaki yake ta fito ko wanka batayi ba ga kayan bacci jikinta, haan yana nuna tun jiya dama da yunwa ta kwana kawai tsabar masifa ne irin na Ramlah. Dan murmushi yayi yana kallonta, yasan tasan kallonta yake amma bazata taba nuna ta ganshi ba.

"Gaba muka koma yi ne, Ramlah? To ina kwana, bari ni na gaidaki." Dagowa tayi, amma maganar da tayi niyar watsa mashi ta makale a makoshinta. Wani irin kyau taga ya mata, ga murmushin da yakeyi sai taji kaman har zuciyarta yake saka hannu yana wani yamutsawa. Saurin dauke idanta tayi daga kanshi tana hanzarin kurbar lemun daya fiddo masu.

"Ina kwana." Murya can kasa kasa ta gaidashi, bai taba tunanin zata gaidashi ba. Amma yasan halin Ramlah sarai da wulakanci, kawai dai bataso yaga ta mashi rashin kunya ne shiyasa amma shi yanada tabbacin nan da wasu yan mintuna sai ta mishi abunda sai yaji kaman ya fiddo zuciyarshi ta sha iska.

"Lafiya lau, Ramlah. Kinyi kyau abunki yau, ko duk amarcin ne?" Dariya taso kufce mashi ganin yanda ta hade fuska kamar taga mutuwarta, shima da gangan ya mata maganar yasan zataji haushi. Har ta gama cin abinci bata tanka shi ba bata kuma kara kallon inda yake ba.

Mikewa tayi tsaye tana kallonshi a shekeke, kamar ta wankeshi da mari takeji tsabar takaicin da yake bata. "Zanje gida yau." Abunda ta furta kenan tana jira tajoi me zaice kafin taje tayi wanka. Ita koba gida ya kaita ba tadai bar gidannan. Tunowa take ranar daya kawota dan tayi bacci ranar da suka fara haduwa da Yasir a shagonta. Gidanne dai babu abunda ya chanza, dukda ba yanda Mama batayi dasu ba akan ta sayi kayan daki su duka dagashi har Dr Aliyu sukace Aa, tunda komai na gidajensu sababbi ne. Saidai kuma duk yanda sukazo saida ta basu kudi dukda da kayan zata siya kudin sai sunfi haka.

Amma abu daya ya chanza, farin ciki. Ranar da sukazo cike da farin ciki suke, wasa da dariya, tana iya tuno yanda yace mata da addu'a ake shiga gidan miji ashe dai da gaske gidan mijin nata ne. Kallonta yake ya mike yana kallonta. Saida ya tako daidai gabanta tukunna batayi aune ba taji ya sakar mata kwanya saman kai.

Baya baya tayi tana turbune fuska tana sosa kanta, "Wai miye haka? Wannan ma ai zalinci ne." Kamar wata karamar yarinya haka take magana, bata lura da yanda take turo baki gaba ba ko yanda take kallonshi narau narau duk wannan tsanar ta tafi.

"Haka ake tambaya unguwa?" Murmushi yake har kasan ranshi, yanda tayi yanzu haka kadai ya faranta mashi rai.

"Naga ai tun jiya mun gama magana ko? Gida zan koma ni, idan kuma bazaka maida ni ba to zan kira bolt in tafi." Harara ta balla mashi tana jiran amsa.

"Dawa kika gama magana? kindai yi wulakancin ki ni kuma na saurara, amma ba inda zaki." Tafiya yayi ya barta nan tsaye, kallon bayanshi take har ya shiga daki tanaji kamar taje ta shake shi. Wani irin tukukin bakin ciki ne ya mamaye mata zuciya, amma ta gama sakawa a ranta duk bala'in da za'ayi yau sai taje gida amma bazata kara kwana a nan ba.

MIJINA NE! ✅ Där berättelser lever. Upptäck nu