Ashirin Da Daya

1.4K 216 15
                                    

Koda ta kirashi taga bai dauka ba har ta fidda rai, dan tasan sarai Rayyan bama zai dauka ba kuma ba kiranta zaiyi daga baya ba. Zama tayi kafin tayi order din abincin da takeso taci, tunowa da sakon da Ramlah ta turo mata hakan yasa wani dan guntun murmushi ya subuce mata. Tana nan zaune tana tunanin ta wace hanya ya kamata ace tabi domin jawo hankalin Rayyan zuwa gareta sai ga me kawo abincin ta aje mata shi a gabanta.

Godiya ta mata ta gyara zamanta yanda zataci abincin ta koma wajen aikinta ba tare data makara ba. "Aah, yan mata ya gajiya?" Magana taji kamar daga sama, kuma wanda yayi maganan ya janyo kujerar dake gabanta ya zauna harda su kiran me kawo abinci. Hade fuska tayi kaman bata taba dariya ba tana dagowa taga Rayyan yana mata dariyar wasa.

Lubnah bata san lokacin data sauke wata ajiyar zuciya ba hade da fashewa da dariya. "Wai yanmata ya gajiya." Har zuwa yanzu dariyar take, shi kuwa idonshi kan fuskarta ganin yanda take dariyar alamar taji dadin ganinshi. "Ai na dauka bazaka zo ba."

Gyara zamanshi yayi ya harde hannayenshi saman kirjinshi. "Lokacin da kika kira ina masallaci sai ysa ban dauka ba. Dama ina ganin kiran nace to Lubnah tana nan wajen." Murmushi tayi ta daga mashi kai a daidai lokacin da me kawo abincin ta miko mashi nashi. "Ya kike? Ya aiki?"

Yar ajiyar zuciya ta saki hade da aje cokalin da take cin abincin dashi ta bude lemun da suka kawo mata. "Kasan Allah ji nake kamar nayi resigning na barwa mutanen nan aikinsu. Yar karama dani aiki kaman ya kasheni, wannan ai sai su saka ma mutum hawan jini bai shirya ba."

Yar dariya yayi yana fara cin abincin shi, "Wai yar karama dake. Kiji tsoron Allah Lubnah, masu shekarunki a kauye suna can neman fara tara jikoki suke bama yara ba." Hararar wasa ta fara binshi dashi, "Zanzo ma dai ince ma Mama ya kamata a aurar dake."

Dariya tayi, "Sai inga da abunda za'a aurar dani ai. Badai ta siyen gida da kayan ciki ta kaini ni kadai in zauna. Sai a jira in samu saurayi."

"Saurayin ma ai zaa samu." Da haka suka cigaba da hira sunayi suna dariya wanda duk wanda ya shigo ya gansu to tabbas zai dauka wasu masoya ne da suka dade tare da juna. Ita kau duk maganar da suke kalmar 'Saurayin ma ai zaa samu' tafi tsaya mata a rai. Har Allah Allah take ta koma gida ta tambayi Ramlah.

Koda suka gama cin abinci har bakin motarta ya rakata, dan shi a kasa ma zai iya gangarawa office. Saida ta shiga yazo zai rufe mata kofa yace, "Wannan murmushin dai dan Allah ba kowa za'ai ma shi ba. Inba haka ba aja ma yan office daukar zunubin kallon matar da ba tasu ba."

Har ranta wani sanyi taji ya ratsata. "Kodai kishi kake ne?" Da dariya tayi maganar, bai mata amsa ba shima yana dariya saida ya kulle kofar ya danyi baya kadan. "In ma kishin nake ai banyi laifi ba." Wayyo Allah! Yinin ranar duk juyin da tayi maganar dake fado mata a rai kenan. Murmushi kuwa kasa daina yinshi tayi. Ji take kamar ta kira Ramlah ta fada mata sai kuma data tuno labarin zaifi dadi baki da baki sai ta hakura.

Bata taba k'agara ta koma gida ba kamar yau, sai kuma ana gab da zaa tashi CEO dinsu ya kirashi emergency meeting, Lubnah kuwa ji take kamar ta kurma ihu tace bata zuwa. Amma tunowa da idan ta koma gida zasu hadu da Rayyan, zata kuma tuna da abunda yace mata yasa ta danne zuciyarta.

A da ta dauka bazata iya ba, amma kuma tunda ta fara sai taji abun yafi komai sauki. Karshe ma da marece yayi garden din gidan ta koma da dan lemunta da snacks tanaci tana editing pictures din. Bata san da zuwan mutum ba saidai taga hannun mutum ya dauki cookies gefenta. Wani irin faduwa gabanta yayi tana juyawa taga Rayyan, shima zaune da yar laptop dinshi a hannu.

Bai kalleta ba, ita da hanzari ta dauke idonta. In fushi ma yakeyi ya dade baiyi fushin ba wallahi. Sunfi minti talatin a haka babu wanda ya cewa wani komai kuma har lokacin bai daina mata dauki dai dai ba. Karshe ma cup din da takeshan lemun ya mayar gefenshi yanasha.

"Wai dan Allah miye haka? Idan so kake sai kace na kawo maka naka ni ba bakuwar zafi bace ba ai kasan kawo maka zanyi." Bata san ma tana hararar shi ba sai dataga yanda yake kallonta da mamaki kwance kan fuskarshi. Amma alamu sun nuna dadi ma yakeji in ya bata haushi.

"Maida wukar malama, lemu dai baya hadani fada dake." Cup din ya maido gefenshi ta girgiza kai. "Tunda ka fara sha ai kawai ka shanye, na koshi kuma." Shi mamakin tsiwa irin ta Ramlah yakeyi. Da kila ko damuwar da take ciki ne yasa halinta bai fito ba? Kila kuma duk haushin ne bai saketa ba oho. Inma fushin ne ai shine ya kamata yayi.

"Oh yanzu kuma kyamata kike?" Cup din ya aje tsakiyar ya rufe system din tashi, itama rufe tata system din tayi ta juyo cike da tsiwa tana kallonshi. "Yaushe mukai haka dake? Nifa wallahi ka daina man abubuwan da kake man."

"Oh yanzu kuma banda kyamata fada ma zaki man, Ramlah? Nan gaba kuma ai sai zagi Ramlah ko?" So yake yayi dariya ganin yanda take fushi bil haqqi amma ya daure shima ya hade fuska.

Juyowa tayi sosai suna facing juna, "Wai dan Allah me kake nufi? Nifa ba kyamarka nake ba," cup din ta dauka, tana kallonshi cikin ido, shan lemun ciki saida ta aje cup din sannan ta bashi amsa, "To ka gani ko? Ni ba kyamarka nakeyi ba."

"Amma dai ai haushi na kikeji." Bata fuska tayi ta juya, "Wannan kuma daban, kai kamun abunda zanji haushin naka." Murmushi yayi ganin bata ganin shi. Ji yake kamar ya fiddo wayarshi ya fara daukarta hoto, komi tayi kyau yake mata, shidai ji yake idan zaa aje mashi Ramlah gaba daya yinin rana kawai yaita kallonta bazai gaji ba.

"To na baki hakuri ai ko?" Juyowa tayi, idanunsu na haduwa tayi hanzarin dauke nata idon. "Ai bance na hakura ba." Turbune baki tayi tana bashi amsa.

"To yanzu ya kikeso ayi? Nidai gaskia fadan nan namu bana sanshi. Ramlah kiyi hakuri na hanaki taba namijin da ba naki ba, na hanaki aikata sabon Allah. Kiyi hakuri, kin yafe man?" Ita bata san habaici, wannan ban hakuri ko jefa magana.

Juyowa tayi da yar harara a idonta, "Kai din daka tabani sai naga miji nane kai ai." Dariyar da yaketa kokarin dannewa ce ta fito. Gani yayi ta tashi buu zata koma ciki shima yayi hanzarin mikewa yana tsaida tashi dariyar, "Aa ni ba mijinki bane ba, amma ai Allah kadan yasan ikonshi ko? Kuma ni dalilina shine ina gudun ki ruga ko ki kara suma. Astagfirullah, na goge wancan zunubin."

Tsayawa tayi kawai tana kallonshi. Harararshi takeso tayi sannan ta gaggaya mashi magana amma bataso yaga kamar ta raina shi. Basu kara minti daya ba a haka saiga Lubnah wacce daga gani a gajiye take. Murmushi ta sakar masu dukansu, "Ya na ganku haka tsaye kamar masu fada?" Bata jira sun bata amsa ba ta zauna kan kujerar da Ramlah ta tashi ta dauki cookies daya tana ci, "Yunwa nakeji kamar naci babu."

"Lubnah kawarki fada take dani, dan na hanata sabama Allah." Rayyan ne ya koma ya zauna kafin ya bata amsa, ita kau Ramlah kallonsu kawai takeyi amma ji take kamar ta makeshi ta huta.

"Ah, Ramlah Rayyan din yau kuma ake fushi dashi? Sabon me ka hanata yi kai kau? Kasan wani sa'in zunubi dadi gareshi." Dukda fushin da takeyi hakan bai hanata fashewa da dariya ba, su duka ukkun suke dariya kamar Allah ya aikosu sai can Ramlah ta tsaida tata.

"Ni dama karki saurareshi. Bari inje in fara girkin dare, kuyi hira dan Allah ki fada mashi yanda ake ma mata magana. Ni wallahi haushi yake bani kamar inta bugunshi." Tana fadin haka zumbur ta kara gaba.

Wata irin dariya Rayyan yakeyi, wallahi yarinyar can ta rainashi. "Dawo nan Bakatsina, duka ake cewa!"

"Kaidai ka sani! Ni karma ka kara nuna ka sanni!"

"Aa Ramlah sai munzo biko gaskia, ayi hakuri!" Lubnah ce tayi magana a tare ita da Rayyan suka fashe da dariya. Saidai suka daina dariya ta sauke ajiyar zuciya, "Yanda kasan an ciremun kaya haka nakeji, ba abunda nakeso kamar inga Ramlah tana walwala."

"Naga ta saki ranta ai, ban taba ganin mutumin da yake kaunar kuka kamar Ramlah ba." Yar dariya Lubnah tayi tana mikewa tsaye. "Ai dazu da safe danace mata ya akai naga haka sai cewa tayi sallar dare tayi sannan kuma Dr Aliyu ya mata yan maganganu." Dariya ta farayi, "Bari ma inje inji yan maganganun miye yai mata."

Yar magana sukayi batafi ukku ba kafin tace ta gaji zatace ta dan watsa ruwa ta huta. Bai nuna mata komai ba har ta bar wajen sannan ya tuno kalmar. Wato su duk abubuwan da suka dade suna fada mata bataji ba sai na Dr Aliyu? Baisan abunda yasa ba, amma a duniya bashi da burin daya wuce ya mantar da Ramlah rayuwar Dr Aliyu. Takaici ke kasheshi in ya tuno yanda suke.

MIJINA NE! ✅ Where stories live. Discover now