Hamsin Da Biyu

1.4K 182 15
                                    

Sunyi kukan, sunyi dariya da labarin abubuwan da suka faru a cikin rayuwarsu watanni uku da suka shude. Ramlah tun tana so ta nuna fushin abun taga Lubnah nata janye jiki da maganar sai ta kyaleta. A lokacin data shaida mata cewar tanada juna biyu kuwa babu irin ihun da Ramlah batayi ba. Zaune take a kitchen Ramlah kuwa tana girka masu abincin dare, dan kuwa Rayyan yace sai bayan isha'i zaizo daukarta.

"Yanzu ke Lubnah, wayyo Allah na, na kasa yarda wallahi cikin nan gareki." Dariya ita Lubnah abun ya bata, yanda Ramlah take magana sai ka daka ita bata taba haihuwar bama.

"Kema idan aka bibiya wannan cikin naki tabbas akwai ajiyar Rayyanu ciki." Mamaki take can kasan zuciyarta yanda babu ko digo daya na san Rayyan daya rage a ciki. Dadi ma takeji yanda Allah yasa har tunaninta na ta sadaukar wa Ramlah da wannan wahalalliyar soyayya yazo mata, dan idan baccin haka ta tabbata da bazata taba yin farin cikin da take ciki yanzu ba. Kuma alamu sun nuna itama Ramlar tana cikin farin ciki.

Hararar wasa ta galla mata kafin ta rage wutar gas din ta dawo ta zauna gefenta, "Lubnah, nagaji da yanda kike basar da maganar nan. Bazan taba samun natsuwa ba idan har bamuyi maganar nan ba, Dan Allah." Yanda taga fuskarta ta sauya zuwa alamun yanayi na rashin jin dadi yasa Lubnah ta juyo a hankali ta riko hannayenta tana bata dukkan hankalinta waje daya.

"Ina jinki, Ramlah. Maganar mecece wannan da take neman saka man ke kuka? Ko fada kukeyi da Rayyan dinne har yanzu?" Yar dariya tayi Ramlah ko kafin ta bude bakinta hawaye sun sauko kan kuncinta. "Ke kike sakani kuka, Lubnah kullum banida kwanciyar hankali. Bansan meyasa kikayi abunda kikayi ba bayan ni shaida ce irin soyayyar da kikewa Rayyan, dan Allah meyasa kikayi haka?"

Kallon hawayen dake bin kuncin Ramlah tayi kafin tayi kokarin danne nata, dan idan ta biye mata suka fara kukan wannan abun yanzu babu mai iya tarosu. "Ramlah, yanzu ke miye amfanin wannan maganar dan Allah? Ba komai ya wuce ba? Yanzu kuma kowa yana cikin farin ciki? Kalli fah, ni ciki ma gareni." Dariya suka fashe da ita a tare ganin yanda tayi maganar kafin Ramlah ta kafeta da idanu alamar dole fa sai ta amsa mata. "Toh, ranar danace kije ki kai mashi abu a daki yana parking? Na biyoki da wayarki Dr Aliyu yanata kira naji duk abunda kuke cewa..." Jikin Ramlah saki yayi gaba daya dan bata taba tsammanin abunda yasa Lubnah tayi abunda tayi ba kenan. Allah sarki bawan Allah ta dauki alhakin shi, taita cewa shi yaje yace mata Ramlah yakeso.

"To aini bakiji nace ina sanshi ba ko? Dan me zaki sadaukar da soyayyarki a wajena? Lubnah tunda nake ban taba ganin mutum irinki ba." Kuka sosai Ramlah takeyi, dan ta tabbata kaf cikin rayuwarta babu mai mata irin soyayyar da Lubnah take mata.

Yar dariya Lubnah tayi, amma duk yanda taso ta danne hawayenta saia suka sauko. "To ai shi so ba sai ka furta a baki ba, Ramlah. bazance ga ranar daya fara sanki ba amma saida abun ya faru na lura da abubuwa da yawa wanda ya kamata ace na lura dasu, Rayyan yana maki soyayyar da bazai taba yiwa wani mutum ita ba a duniya. Kema kina sanshi, kuma kar kiman gardama," Ganin yanda Ramlah ta taso yasa ta fadi haka da yar dariya. "Kina sanshi sosai ma ba kadan ba, dukda ke karfin taki soyayyar baikai na yanda nashi yake ba, zaki iya hakura dashi amma kuma zaki dade cikin kunci dukda cewar bama ki gane kina sanshi dinba. Ko kuma kin gane a zuciyarta amma wani sashi na zuciyarki yana fada maki cewar haramun ne kiso wanda nakeso." Ajiyar zuciya Lubnah ta sauke, tana tunano irin bakar azabar da tasha lokacin da abun ya faru, saidai yanzu jin komai take kamar bai faru ba, babu  komai a zuciyarta banda zallar farin ciki.

"Rayyan ya riga daya furta bazai taba yin rayuwar aure cikin jin dadi tare dani ba, ke yakeso bani ba. Koda bai fadi hakan ba Ramlah bazan iya zama dashi ba saboda a kalamanki na tabbatar kina sanshi ni kuma a duniya banga abunda zan hana maki shi ba, koda kuwa Rayyan dinne a lokacin." Ganin yanda Ramlah ke kuka kamar zata shide har dariya yaba Lubnah, "To duk miye na kukan? Ke dallah malama ki saki ranki kishi soyayya da mijinki kinji? kar nayi aikin banza wallahi." A tare suka fashe da dariya.

MIJINA NE! ✅ Where stories live. Discover now