Sha Daya

1.7K 340 84
                                    

Saida ta shiga motar ta zauna kafin ta juyo da dan guntun murmushinta. "Ina wuni?" Ta furta a hankali tana fara wasa da yatsun hannunta. Ita kam nauyin Dr Aliyu takeji. Eh tasan kunya tana daya daga cikin dabi'unta amma nauyi da kunyarshi da takeji daban ne, kila hakan yana da alaka da kwarjinin da yake mata.

Yar dariya yayi ya juyo yana kallonta hade da girgiza kai, "Wannan hausa taki da anji ansan daga Katsina kike ko baki fada ba. Ina yini ake cewa ba ina wuni ba." Sai lokacin ta fahimci dalilin kallonta da yakeyi da kuma murmushin dayake mata.

Dan turbune baki tayi a hankali, "Kaidai kawai ka ansa shikenan ba sai an zauna ana kidayar hausar wane gari nikeyi ba."

Dariya ya fara yanzu, "Nakeyi ba zakice. To in zan amsa ki me zance?" Daga gani dukda ba wata hira suke ba amma abun yana mashi dadi. Saida ta kalleshi da kamar bazata amsa ba can kuma ta dan dake irin to koma menene ai ba laifi nayi ba.

"Lahiya lau zakace ko? Da ya ake amsa gaisuwa?" Dr Aliyu baisan lokacin daya fashe da wata irin muguwar dariya ba. Sai kara maimaita 'Lahiya Lau' yake kamar wanda yau ya fara jin ana cewa haka. Ganin ta bata fuska yasa ya daina dariyar ya juyo yana kallonta.

"Yi hakuri toh, na daina dariyar. Amma yanzu tunda Abuja kike ki daina maganar yan Katsina. Ba wannan ba, naga bakizo asibiti ba yau, ko lafiya ta samu?" Kallonta yake kyam yanaso yaga yanayin yanda zata mashi magana wanda ta hanyar ne zai fahimce ta.

Dan murmushi tayi kafin ta gyada mashi kai. "Eh toh, Alhamdulillah zance. Zan iya daina zuwa ko kuwa dole sai naje?"

Cikin girgiza kai ya bata amsa, "Aa, muda mukesan kima manta kin taba zuwa asibitin. In har kinaji you can cope, ba sai kinzo ba. Amma ni zan iya zuwa?" Dakyar ya samu maganar nan ta fito bakinshi kamar wanda yayi laifi yana jiran hukuncin alkali.

Ramlah wani kasake tayi tana kallonshi, itadai ba yarinya ba balle ta nuna mashi cewar bata gane abunda yake nufi ba. Dukda cewar girman nata itama rayuwa ce ta mayar da ita babba bawai dan takai shekarun girman ba. Dan wayincewa tayi, "Kazo? Ina zakazo?"

Sarai yasan da gangan take nuna bata gane abunda yake nufi ba, "Nan gidan mana, ko kar nazo?"

"Me zakayi in kazo?"

"Wajenki zanzo mana."

"Me zan maka toh?"

"Ganinki kawai zanyi, muyi labari, kiman hausar Katsinawa sai na tafi na bawa Hafsah labarin Amminta." Ita ba kasafai ta cika san irin yan maganganun nan ba, duk yanzu a haka ma yanda suke ya gama dagula mata lissafi. Jin ya ambaci sunan Hafsah yasa ta samu mafita.

"Allah sarki Hafsah, ya take? Nayi missing dinta."

Baice mata komai ba ya ciro waya ya kira Hajia Mama, kamar kuwa yasan wayar ma tana hannun Hafsah muryarta sukaji tana fadin, "Hello? Wake magana? Hajia Mama tana bangaren Baba Alhaji, kuma munyi fada dashi nace bazan kara zuwa wajenshi ba, idan ta dawo zan gaya mata an kira."

Dama a speaker ya saka wayar, dariya kawai suke fashe da ita a tare. "Innalillahi, Hafsah yanzu da Baba Alhajin ake fada?" Ramlah batasan lokacin da tayi magana ba muryarta cike da dariya.

Shiru sukaji kafin a hankali Hafsah ta fara magana, "Ammi? Tsaya, wai dama Abba ne?! Ammi karki fada mashi nayi fada da Baba Alhaji, shima wai sai yace tunda nayi fada da Babanshi shima ba ruwanshi dani."

Ramlah juyawa tayi tana kallon Aliyu da sai murmushi yake, ba sai ya fada ba zakaga tsantsan soyayyar diyarshi cikin idonshi. "To indai bakisan Abba yaji da mun gama waya sai kije kibawa Baba Alhaji hakuri kinji?"

Hafsah sai gyada mata kai take kamar tana gabanta, "Eh Ammi. Ina yini? Ammi nayi missing dinki." Fira suka farayi har suka gama Aliyu yana jinsh amma ko kadan baice ko kala ba. Karshe ma komawa yayi ya tsaida nashi idanun akan Ramlah wacce sai dariya take suna fira da Hafsah. In ka ganta tana dariya bazaka tana tunanin ta taba shiga kuncin rayuwa ba.

MIJINA NE! ✅ Where stories live. Discover now