Biyu

2.4K 273 8
                                    

Saninta ne cewar mutuwa bata da tausayi, amma Ramlah bata taba tunanin cewar a yanzu yanda take rayuwa ba, akwai wani abu da zata kara rasawa ba. Ta dauka cewar mutuwa ko kuma rashi na koma menene zai daga mata kafa na wani lokaci. Ashe duk kuncin da taxi a baya wani wanda ya fishi yana nan tafe? Dama akwai wani abu da zai zarce zafi da radadin da mutuwa ta bata a baya? Tayi rashi a rayuwarta wanda hakan ya kasancewa saida mutuwa ta tabbatar ta rasa duk wani bango wanda zata rab'a taji sauki a ranta. Yanzu kuma Hanan din da ta rage mata itama saida ta tafi? Wannan wace irin rayuwa takeyi ita Ramlah?

Tsaye take har yanzu rungume da Ramlah tana jiran su gama dukkan wani cike cike da zasuyi kafin ta wuce gida. Shin inama zataje daga nan din? Wa zata samu a taimaka mata a rufo mata Hanan? Ko masallaci zata kaita? Tasan nan ne take da tabbacin wadanda zasu taimaka ma rayuwarta. Koda ta ciro sauran kudin dake jikinta ta bawa nurse din da sunan sauran cikon kudin da bata biya ba, saida wani abu ya tokare zuciyarta. Shin dama s likitocin haka suke? Babu ruwansu dame ka rasa ko kuma wa karasa? Babu hawaye ko daya saman kuncinta, kallonsu kawai takeyi da idanunta da suka kankance wanda dakyar take kallo dasu.

Nurse din da take bawa ajiyar Hanan ce ta karaso har inda take idanunta suna masu zubda hawaye, "Nasan kina cikin kunci me tarin yawa, Ramlah. Amma ki kasance baiwa me daukar dukkanin kaddarar da mahaliccinta ya miko mata, kinji? Bansan labarinki ba, amma ina tabbatar maki zakiji dadi nan gaba Insha Allahu."

Ramlah batace mata komai ba, amma tana mai tabbatar da cewa ita da jin dadi sunyi hannun riga. Yanda batazo duniya cikin jin dadi ba, ta tabbatar ma kanta haka zata kare rayuwar cikin kunci da tarin wahala. Girgiza kanta tayi, tanajin da kowane wucewar dak'ik'a jikin Hanan yana kara sanyi da kuma nauyi a nata jikin. Tasan bazata iya rufe Hanan ita kadai ba, yanzu kuma dare yayi ko taje masallaci babu wanda zata samu. Yanzu ina zataje? Shin ya zatayi da rayuwarta ne? Haka zataje ta tasa gawar Hanan tana kallo har fitowar almuru?

"Zan iya tafiya? Sun gama komai?" Tambayar data jefi nurse din da ita kenan. Amma ita da kanta saida taji tsoron yanayin yanda muryarta ta fito. Tamkar ba tata ba, tamkar muryar wacce tayi shekara da shekaru ba tare da ta furta kalma daya ba.

Hannu nurse din ta dora saman kafadunta, "Ki tsaya a asibitin ki kwana, Ramlah, yanzu ina zakije in kin fita daga nan?" Dan buge hannunta tayi kadan kafin ta duka ta dauki tsohuwar jikkar kayan Hanan, dan ita bata ma dauko kaya ko daya ba, kullum tana kan titi neman kudin magani bata da lokacin chanza kaya.

"Nagode da kulawar da kika bani nida Hanan, Nurse Khadija, Allah ya hada fuskokinmu da alkhairi." Tana furta hakan ta fita daga dakin. Tafiya kawia takeyi bawai dan tasan inda take saka kafafunta ba. Ita dai tasan ta tsallaka titi, sannan kuma jikin Hanan da take rungume dashi sai kara daskarewa yake wanda har takan ji sanyi yana ratsa bargon jikinta da wani iri rad'ad'i na zafi da bakin ciki da yake kwanciya malemale kasan zuciyarta.

Ita dai tasan idanunta a bude suke, kuma dukda cewar da duhun dare ai akwai hasken farin wata, amma bazata iya cewa ga inda take takawa ba ko kuma ga inda take a fadin garin Katsina. Titi tazo tsallakawa, amma bata lura tana kan titin ba saida taji karar mota da alama wanda yake ciki yanaso ta kauce ta bashi hanya, wanda hakan ma da hanzari ake bukatar tayi shi. Amma bata gane komai, batasan ina zata saka kafarta ya kaita gaba ko baya ba. Juyowa kawai tayi tana kallon motar idanunta kuma bude kyam amma ko kadan bata ganin gabanta.

Da wani k'ugin kara taji wanda yake cikin motar ya tsaya gab da za'a bugeta. Bata gane me yake faruwa ba saidai taji hannaye saman kafadarta, "Baiwar Allah lafiya kuwa? Kina bukatar taimako ne?" Muryar mace ce, tabbas ta gane wannan muryar mace ce amma bazata iya cewa ga kamannin me muryar ba.

A hankali kamar wacce aka yankewa duk wada mahad'a a cikin jikinta ta juya tana kallan fuskar matar, "Ki taimaka man, ki kaini makabarta na binne Hanan. Jikinta sanyi, banaso tasha wahala fiye da wacce tasha a baya." Sai yanzu kamar budar famfo haka hawaye suka fara zubo mata tana me kara kankame Hanan cikin jikinta tsam.

"Innalillahi. Diyarki ce? Rasuwa tayi?" Cike da firgici da tashin hankali matar take magana tana rikota kusa da ita. Daga mata kai kawai Ramlah tayi dan batasan me zata ce mata ba. Bakin ciki da kunci sunyi kane kane cikin ruhinta. Tana ji matar ta jata ta shigar da ita cikin mota. Cikin hanzari ta zagaya wajen zaman direba ta tada motar suka kama titi.

Tana tuki tana juyowa tana kallon Hanan wacce take rizga uban kuka tana kankame Hanan, "Kiyi hakuri dan Allah, bansan meya faru ba amma na tabbata kina cikin bakin ciki. Kinga yanzu dare yayi, zan kaiki gidana da asuba sai ayi mata sallah insha Allahu. Allah ya jikinta." Jikinta ya kidime, tunda take bata taba ganin gawa ba sai yau, dukda cewar bata ga fuskar yarinyar data rasu ba, amma jikinta yayi bala'in sanyi, tsoro ma ita duk ya shigeta.

Ramlah dai bata ce mata komai ba, haka har sukayi parking a bakin gate me gadi ya fito ya bude suka shiga. Da hanzari ta fito daga motar ta juyo ta bude ma Ramlah, "Kiyi hakuri dan Allah, ki fito mu shiga ciki, in Allah ya kaimu da asuba sai ayi mata wankan." Ita ta dauko jikkar su Ramlah sannan ta shigar dasu cikin gidan. Kuka takeyi amma babu sauti ko daya dake fita daga bakinta, da alamu idanun nata suna kukan ne kawai dan hakan shine daidai abunda ya kamata suyi.

Dakin data kaisu ta aje babba ne madaidaici. Rabawa Ramlah tayi ta kwantar da gawar Hanan wacce zuwa yanzu ta daskare. Juyowa tayi tana kallon matar, sai yanzu taga yanda take, ba babbar mata bace ba, haka zalika ba yarinya bace jagab. Hasali ma zasu kama kusan shekara daya ko dan banbancinsu daban ne da Ramlah. "Dan Allah ki taimaka mani da ruwa cikin kwano da dan tsumma in shafa mata a jiki."

Fita matar tayi kafin ta juyo tana kallon gawar Hanan dake kwance idonta rufe saman gadon. Da hanzari ta kawo mata abunda take bukata, tana dawowa ta tarar da Ramlah ta tasa gawar Hanan babu abunda takeyi banda kuka ta rike hannayenta bibbiyu tana kuka. "Hanan dan Allah ki dawo, ki taimaka man karki tafi. Hanan wallahi bansan ya zanyi da raina ba idan baki nan. Hanan kinsan bani da kowa daga ke sai Allah, yanzu Hanan ni kadai zan rayu? Nasan kina jina ko? Dan..."

Da hanzari matar ta aje kwanon ruwan akan gadon kafin ta zauna gefen Ramlah, "Nasan yarinya ce karama, kuma bansan labarin rayuwarki ba, amma fadi ma mamaci irin wannan kalaman ba daidai bane. Tamkar baki yarda da kaddarar ubangiji a kanki ba kenan. Dan Allah kiyi hakuri, muyi fatan rahama a kanta ke kuma Allah ya yaye duk wani kunci dake cikin zuciyarki."

Ramlah juyowa tayi tana kallonta da idanunta da sukayi jajir tsabar kuka, "Ta tafi din kenan? Ta rasu da gaske?"

A hankali ta dafa mata kai, dukda cewar matar nan ta bata tausayi kuma alamu sun nuna cewar yanzu a zaunen da take batasan abunda take furtawa ba, dole ta fada mata gaskia. "Ta rasu, ta tafi. Ke kuma ina da tabbacin Allah zai maki maimaici da abunda yafi zama alkhairi a rayuwarki. Kiyi hakuri, bansan yanda ake yiwa gawa ba danayi mata, amma ki goga mata ruwan kinji? Ina nan tare dake." Tunda take bata taba tausayin mutum kamar yanda take tausayawa wannan matar da ko sunanta bata sani ba. In da hakanan ne, da tsoro zasu bata, haka kawai kaga mace tamkar mahaukaciya tsakiyar titi tare da gawa? Amma samsam bata tsorata ba.

A hankali Ramlah ta fara matse tsunman ta fara gogawa jikin Hanan tana gyara mata kwanciyarta. Dan jikinta yayi fayau dashi ba kamar Hanan dinta da tae fama da ciwo ba. A haka suka zauna har asuba tayi, sai addu'a suke mata suna tofawa. Bayan sunyi sallar asuba ne matar ta mike ta kalli Ramlah, "Zanje na sami limamin unguwar nan, Insha Allahu zaayi mata sallah tamkar yanda addini ya tsara."

Ramlah wacce take zaune rungume da guiwowinta ce ta dago rinannun idanunta ta daga mata kai, "Nagode." Abunda ta iya furtawa kenan kafin taji ficewarta a hankali. Daga inda take zaune tun bayan da tayi sallar asuba ta juya ta kalli gadon, wanda zuwa yanzu sun lulube Hanan, babu abunda take hange face yanayin tozon da jikinta yayi ta jikin bargon da suka lallabeta dashi. Tasan yanzu babu gatan da zatayiwa Hanan wanda zai wuce a kaita makwancinta tamkar ko wace gawa. Runtse idanunta tayi, tana tunanin shikenan, daga lokacin da aka dauki Hanan domin binne ta, ya tabbata bata da komai bata da kowa a fadin duniya.

MIJINA NE! ✅ Where stories live. Discover now