Ashirin Da Takwas

1.5K 225 113
                                    

Tsaye tayi har saida motar ta bace mata da gani, ji take kamar tayi kuka ta rokeshi dan Allah ya bar mata ita. Amma ta ina? Yarinya da gidansu, dan murmushi tayi ta juya ta koma cikin gida, kwana biyun nan da tayi da Hafsah tana iya cewa tunda ta zo Abuja bataji dadin ranaku kamar rankaun ba, sai taha kamar da Hanan take rayuwa saidai wannan rayuwar cikin walwala da farin ciki.

Yamma yayi, tunani take taje ta zauna tayi kallo ko kuwa? Tunowa da tayi da wani online course da tayi register yasa ta chanza tunani, kitchen taje ta debo yan abubuwan da zataci kafin ta koma garden. Da system dinta a hannu sai notebook yanda zata rika daukan notes. Sosai Ramlah ta maida hankali akan abunda take koya, dan wasu abubuwan dama ta koyesu tun wajen Goerge okoro, wasu kuma yanzu take sani.

Tana nan zaune sai taji an rungume ta ta baya, "Wayyo Allah!" Ta fada a dan tsorace, tana juyawa sai ta lura ashe Lubnah.  "Ah ah, amaren bana ne ashe!" Dariya suka fashe da ita tare suna tafawa kafin Lubnah ta sami waje ta zauna, ko kafin ta fara magana saida ta cika baki abinci. "Kullum a yunwace kike dawowa Lubnah, gashi nan duk kin rame wallahi. Dan Allah ki rika kula da kanki, kodai lunch zan rika badawa ana kawo maki?"

Dariya Lubnah tayi tana girgiza kai, "Haba dai kamar wata yar primary school?" Lemu ta kurba tukunna ta cigaba da magana, "Ina yar albarka? Ko har ta tafi?"

Murmushi Ramlah tayi tana daga mata kai, "Hada kukanta wai ita sai ta jira Aunty Lubnah tukunna, amma yace shi he's busy yau dan squeezing ma yayi yazo ya daukota. Da kunkunai dai aka tafi, nace zan kirasu ki mata sallama ai."

"Allah sarki yar diyata." Da hanzari ta hude jakarta tunowa da tayi, "Kafin kuma in manta, kinsan ranar da mukaje bank kika cike abubuwan ki dawowa kikai saboda mutane kuma basu gama atm ba, to ya kawo mun atm din yau wajen aiki, gashi. Ina wayarki? Zan miki activating online banking, na saka maki kudi a cikin bank din." Ita dai Ramlah kallonta kawai take, bata jira amsarta ba ta dauki wayar dake aje kan table ta fara dannawa saida ta gama ta dago tana murmushi.

"Yauwa, gashi. Yanzu kinga zaki iyayin komai. Transfer, kati, ke komai. Da card din kuma zaki iya siyen komai da kikeso online..." tana magana ta dago tana kallonta, gani tayi kamar gawa haka Ramlah tayi zaune tana kallonta, "Ke miye haka? Kinsan Allah bansan haka Ramlah? Kin gode ko? Nasani, anshi ki gani, abinda baki gane ba in maki bayani kayan jikina kaikayi suke man inje in wanka!"

Jiki a sabule Ramlah ta amsa, farko a kan balance din kudin takai idanunta zaro ido tayi. Kodai bataga daidai ba? "Balance din fah? Ban gane ba."

Yar dariya Lubnah tayi tana mikewa tsaye, "Miliyan biyar na baki kija jari da ma duk abunda zakiyi. Sauran dubu dari biyar din sama kuma na kudin hoton Maiduguri ne..." bata ida magana ba Ramlah ta mike tsaye tana dan girgiza kai, hawayen dake cike da idonta suka gangaro.

"Lubnah ya... kudin shago fah? Gyaran shago da sauran kayan aikin shagon? Ya zaki hani wadannan kudaden? Lubnah..." kuka ne ya kwace mata, wai dama akwai mutane haka a duniya? Allah na tuba ba sabo ba amma tana da tabbacin da kafin Hanan ta rasu ta hadu da Lubnah to kila bazata rasata ba.

Kukan data fara ne yasa Lubnah matsowa ta rungumeta, "Ramlah komai kuma kuka kike mashi? Abun farin ciki da bakin ciki? Ramlah miye a ciki? Miliyan biyar har wani abu ce? Na saman kuma ai hakkin ki ne."

"To me zanyi dasu, Lubnah? Kofa assistants dina ke kika biyasu. To ki cire kudin shagon dana gyaran da cameras din da za'a siyo, kar kiyi komai da kudinki."

Da yar dariya Lubnah ta dago daga jikinta hannunta kan kafadunta, "Wannan daban, inaso nayi empowering dinki ne ai ko? Ba photography kadai zaki tsaya ba tunda shi hoto saidai lokaci ne. Zamu zauna ayi tunanin business idea. Kayan shago da cameras da kiketa magana kuma mantawa nayi ban fada maki ba, Rayyan yayi wannan, rabawa biyu mukayi."

MIJINA NE! ✅ Where stories live. Discover now