Ashirin Da Biyar

1.3K 182 8
                                    

Takowa yayi yazo har inda take da wani murmushin jin dadi kwance kan fuskar, "Amma kin taimakeni da yau saidai inyi sumar karya a kaini asibiti dan bansan ya zanyi ba." Dariya Ramlah ta fashe da ita tana mika mashi file din a hannu. "Ji yadda kake binshi da kallo kamar wata sabuwar amarya." Ta fada da sigar wasa, Rayyan dago da fuskar shi yayi daga kan file din yana kallonta, har zuwa yanzu murmushin dake kan fuskarshi bai gushe ba.

"To ke kikeso na kalla haka?" Matso da fuskarshi yayi saitin tata tayi saurin kaucewa tana dariya kafin ta kama hanyar barin dakin gaba daya, "Duk me yayi zafi? Muje karka makara, nima mutane na can suna jirana." Bayanta yabi da kallo yana murmushi har ta fita daga dakin kafin kayan da ya janyo ya maidasu ya fito ya iske ta can waje.

Basuce kala ba har suka suka mota saida ya fara tafiya ya dan juyo yana satar kallonta. Shi kam yaga ta kanshi, bai taba jin wata ta mishi kyan da Ramlah take mashi a kowace rana, ko dai asiri ta mashi? Tunanin hakan ne yasa yayi dariya ba tare da yasan lokacin data subuce mashi ba. Juyowa tayi tana kallonshi, "Lafiya kake dariya kuma?"

Saurin girgiza mata kai yayi, "Babu komai, kawai na tuno wani abu ne." Zata kara magana yayi saurin taran numfashinta. "Kinyi kyau yau, ko wani abu kike shafawa?"

Juyawa tayi ta kalli fuskarta jikin mirror din motar, "Me zan shafa ni kuwa? Ko lipbalm ma babu a fuska ta. Zaku hadu da Lubnah yau?" Ya lura tana yawan san mashi magana a kan Lubnah, amma bai kawo komai a ranshi ba kasancewar tare duk suke abubuwansu su ukku dan wani yakan iya dauka ma su ukun best friend's ne.

"Kina da sako wajenta ne, Yan mata?" Shekeke ta tsaya tana kallonshi, "Wai Yan mata sai naji abun banbarakwai wallahi, miye haka?" Kasa ida magana tayi ta tsaya tanata dariya. Ita kam rabon da taji kalmar yan mata har tama manta. "Kinata dariya, ba yan matan bace?"

Cikin dariyar take girgiza mashi kai, shi kuwa ji yake dama duniyar ta tsaya cak, dan yanda take dariyar bai taba ganin abu mai kyau irin haka ba. "Da diyar tawa kace mun yan mata? Aa."

Bai bata amsar hakan ba, dan bayaso maganar Hanan ta ratsa tsakaninsu dan kuwa nan da nan wannan farin cikin dake cikin zuciyarta dole sai ya gushe. "Dariya na miki kyau sosai, kamar aita maki pictures." Sai lokacin ta dan tsakaita dariyarta. "Nidai yanzu duk ba wannan ba, dan Allah ka sayi wani abu ka kai mata, nasan bata ci abinci ba sai ta dawo duk a firgice ta wahala."

"To ai nima aiki zani ko? Ko na fasa nawa naje na kula da yar lele?" Girgiza kai tayi da hanzari, "Ranar ai ta mana order din abu, kayi ka bada address dinta a kai mata, dan Allah." Baice komai ba ya juya yana kallon titi, "Rayyan manaa," da wani shagwaba tayi maganar wanda hakan kiris ya rage bai taka burki ba yace ta maimaita. "Naji, zanyi." Murmushi ta mishi me kayatarwa daga haka ya cigaba da tuki babu abunda suka furta har ya isa bakin shagon.

"Idan kin kammala ki kirani ko Lubnah, cikinmu duk wanda ya gama sai ya biyu ya dauke ki." Daga mishi kai tayi tana rataya jakarta a hannu, "It's high time ma ace kin fara tuki Ramlah, zadai muyi magana da Lubnah gaskia, tunda ga motoci can a gidan sai ki dauki daya." Sai taji maganar kamar daga sama, wai ita Ramlah ake cewa ta koyi tuki, lallai rayuwa babu yanda bata juyawa dan adam.

Murmushi me tattare da kunci ta sakar mashi, "Aa, ban ma iyawa ai." Zaiyi magana tayi saurin tarar numfashinshi, "Kar na bata maka lokaci, Rayyan. Idan na gama zan kiraku naji, Nagode Allah kuma ya bada sa'a." Daga fadin hakan ta fice daga motar, yana lura da yanayinta dan saida ta tsaya ta saita fuskarta kafin ta shiga cikin shagon tana me kakaro murmushi.

Ajiyar zuciya ya sauke, yasan hakan bai rasa nasaba da labarinta, dukda cewar bai gama jin labarin ba amma yanada tabbacin labarin cike yake da kunci da zallar bakin ciki. Kila kuma taji dadi, wata ajiyar zuciyar ya sauke kafin ya juya kan motar.

Tunda ta iske mutanen nan suke aiki, ita wasu abubuwan ma batasan Lubnah ta siya ba saidai ta gansu, abubuwan kawata shago ga kuma wajen da zata zauna a matsayinta na me wajen sai kuma studio din daukar hoton, nan ne kyan yake. Duk yanda take bukata haka ta nuna masu, abunda bata sani ba kuma dayake su sunsan abubuwa sun saba irin abun nan sai su nuna mata yanda zaiyi kyau, basu gama aikin ba sai wajen karfe hudu da rabi, tana niyyar kiran Lubnah taji sai ga kiran Dr Aliyu ya shigo.

"Hello, Dr?" Ta furta da murmushi kwance kan fuskarta. "Dama banaso ace banda hakuri ne amma ina alkawarina?" Yar dariya tayi jin yanda yayi wata murya.

"Ammi kice mata ta barni nayi bacci da daddare zan kawota, tun wajen 4 aka kira asibiti ban huta ba dawowata kenan amma ta tada man bala'i." Dariya Ramlah ta karayi. "Ahh diyar Ammi bata kyauta ba..." bata ida magana ba sukajiyo muryar Hafsah, "Ammi! Yaki ya tashi mu taho, yace sai yayi sallah, yayi wanka, yaci abinci kuma fa duk yayi, kice yazo mu tafi."

"Haba Hafsah na, baza'abar Daddy ya dan huta ba zuwa anjima?" Ai kafin ta rufe baki suka jiyo ihun Hafsah, ita shikenan ma Ammi tace bata san ganinta. Daga Ramlah har Dr Aliyu dariya sukeyi, "Yi hakuri yar Ammi. Dr aiki fa ya ganka, ka daure ka kawota sai ka koma kayi baccinka ko?" Dan daga murya tayi dan tasan Hafsah na nesa da wayar tana kuka, "Hafsah yanzu zai taho dake, ina shago ma ku biyo ku daukeni."

"Har ta mike zata kaini kara wajen Baba Alhaji, wai ai tunda nime shine Babana dole inyi abu idan yace inyi. Tun wednesday danace na yarda zatazo ake shela." Da dariya ya ida maganar, itama Ramlah dariyar takeyi. Mikewa tsaye yayi, "Tashi muje toh, ai kinma su Hajia sallama ko?" Da muryar kuka Hafsah ta amsa kafin ya ma Ramlah sallama cewar gasu nan tahowa yanzu.

Bakin shagon ta fita tana kallon wucewar mutane cikin motocinsu. Ita Ramlah yau itace a Abuja har take shirin bude shago? Lallai Allah babu yanda baya al'amuranshi. Yan watanni da suka wuce idan aka ce mata zata rasa Hanan sai tace inhar hakan ta faru to tabbas zata iya daukar ranta, amma yau gata, ta rasa Hanan sanna cikin ikon Allah farin cikinta a hankali yana dawowa, wanda rabonta da irinshi tun kafin aurenta.

Shigowar motar Dr Aliyu ya katse mata tunani, jakarta ta sakala a hannu ta nufi motar, saida ta shiga ta zauna kafin Hafsah ta makalkalo ta baya, "Ammi!!!" Ta fada cikin muryar da take nuna zallar farin cikinta. Da dariya Ramlah ta janyo tata mayar da ita saman cinyarta. "Hafsah diyar Ammi, nayi missing dinki." Rungume ta tsam tayi cikin kirjinta, ko dan tayi tunanin Hanan ne? Amma sai takejin kewar yaro a tare da ita. Hawaye ne ke neman sauka a saman kuncinta amma tayi saurin danne su ta dago da murmushi tana kallon Dr Aliyu daya kura mata ido yana kallonta, "Kuka ko, Ramlah? In dai kuka zata rika sakaki to sai na maida ta gida."

"To ai sai ka fadi taji ko." Kallon Hafsah dake saman cinyarta wacce ke wasa da wayarta tayi sanna ta dago ta kalleshi tana kokarin tura hawayenta su koma ciki. "I just miss her, wani lokacin sai naji kamar dana kira sunanta zatazo. Idan ina bacci sai naji kamar idan na juya gefe zanji jikinta wajen, idan ina farin ciki sai naga kamar zatazo ta tambayeni meya faru. Idan ina kuka sai inta jin kamar zanji hannayenta saman kuncina tana goge man su. So nake naje naga koda kabarinta ne, I miss her alot." Hawayenta ne suka kubce mata ta fara kuka marar sauti, shi kuma Dr Aliyu kallonta yake ko kyaftawa bayayi.

"Hafsah, king Ammi bata jin dadi sosai, ki koma baya kiyi game ko? Ai Ammi baki goge game din ba ko?" Ganin Hafsah zata dago yasa Ramlah tayi hanzarin goge hawayenta tana karbar wayar, "Ya za'ayi na goge ma Yar Ammi game dinta? Kawo na saka maki." Tunda Hafsah ta koma baya Dr Aliyu baice komai ba har suka isa gida, ita dai Ramlah tasan jira yake su rabu da Hafsah tukunna.

Cikin sa'a kuwa suna isa motar Lubnah na sauka, da fara'arta tazo wajen motar amma sai tayi turus ganin hawayen dake kwance malemale fuskar Ramlah, "Dr Aliyu ya naga mutuniyar taka haka?"

Dan murmushi ya mata, "Ai yanzu so nake muyi magana da ita amma..." ya dan juya ya kalli Hafsah da take kallon gidan tana murmushi. "Oh, Hafsah ko?" Juyawa tayi ta bude kofar, "Hafsah zo muje Ammi zasuyi magana kinji? Muje na siyo miki wata toy me kyau." Ai ko bi ta kan Ramlah Hafsah batayi ba ta sauko, jakarta Lubnah ta dauko suka shiga cikin gidan.

Dr Aliyu juyowa yayi ya kalli Ramlah wacce daidai lokacin ta saki hawayenta da ke neman fin karfinta, "It's hurting me alot, Dr."

MIJINA NE! ✅ Where stories live. Discover now