Sha Bakwai

1.4K 199 12
                                    

Yanda Ramlah taga rana haka taga dare. Duk yanda Lubnah tayi kokari ta kwantar mata da hankali kasawa tayi, dan ko baccin yaso daukarta firgigi takeyi ta tashi. Sai can gabannin asuba sannan ta samu ta fara bacci amma ko shida batayi ba na safe ta farka da wani kukan. Lubnah tsayawa tayi kawai tana kallon ikon Allah, ita yanzu abun ma ba karamin razana ta yakeyi ba.

Da hanzari ta karasa bakin gadon, hannayenta duka biyu ta dora kan kafadarta tana kallonta cikin natsuwa. "Ramlah, ki natsu dan Allah ki daina firgiga kanki haka nan, kinji? Nasan bazan taba gane halin da kike ciki ba amma daurewa zakiyi Ramlah. Yanzu ki tashi kiyi sallah..." da kyar da lallami Lubnah ta samu Ramlah ta shiga tayi alwalla, koda ta fito taga harda wanka tayi. Bata ce mata komai ba saidai ta fito mata da kayan da zata saka.

Koda ta gama sallar zama tayi kan sallayar tayi shiru kamar wacce aka ma rasuwa. Ita dai Lubnah har ta gama shiryawa bata tanka ta ba sai ta dawo ta zauna gefenta. A hankali Ramlah ta dago da rinannun idanunta ta kalleta sai ga hawaye yar yar. "Ramlah dan Allah kiyi hakuri, dan girman Allah. Yanzu ya kikeso ayi? Bama wannan ba, gaba daya jiya bakici abinci ba fah, me zakici?"

Kadan kadan Ramlah ta girgiza mata kai, "Bazan iya cin komai ba, Lubnah. Nidai kawai ki kaini na mashi magana, na fada mashi Hanan dinmu ta rasu, na rokeki."

Shiru Lubnah tayi dan ita bata gane dalilin Ramlah na yin wannan abu. Wai shin mutum ya taba mutuwa kuma ya dawo? Wannan wace irin kaddarar rayuwa ce Allah ke jarabtar Ramlah da ita? Saida ta numfasa kafin ta dan saki murmushin karfin hali, "Naji, zan kaiki wajenshi kodan kiga bashi din bane ki hakura haka nan, Ramlah. Amma kinga yau walima kuma yau za'a kai Zainab gidanta, kiyi hakuri ki bari sai an gama bikin gaba daya, kinji? Yanzu me zakici? Ko so kike wata cutar kuma ta kamaki bayan wadda ke cin zuciyarki?"

Ta corridor din Lubnah tana jiyo maganganun yan matan amarya alamar zasu wuce direct gidansu Zainab ayi walima daga nan kuma akai amarya. Tasan dole ta kasance tana wajen amma kuma yanzu Ramlah tafi bukatarta. Cikinsu babu wanda zata iya bari shi kadai bayan tasan amfanin da take masu.

Wayarta ce ta fara ringing, tana ganin sunan Rayyan ta sauke ajiyar zuciya. "Hello, Assalamu Alaikum. Rayyan ina kwana?" Ta furta a hankali, tana kallon yanda Ramlah tayi wani kasak'e da ita. Itadai bazace a raye take ba tunda bata nuna alamun rahuqa sannan bazakace a mace take ba.

"Lafiya lau, Lubnah. Ya Ramlar? Ta dawo hayyacinta ko?" Bata kai ga bashi amsa ba taji muryar kanwar Zainab daga kofar dakin tana kwankwasawa a hankali.

"Ya Lubnah, Aunty Zainab tace wai dan Allah kizo bataga rigar lace din da zata saka ba, tace ke kika kawo kayan." Kallon kofar tayi kafin ta kalli Ramlah dake zaune. "Dan Allah Rayyan taimako zakayi, Zainab da Ramlah sun sakani tsaka mai wuya, banma san yanda zanyi ba wallahi. Ko zaka zo ka kular man da Ramlah kafin naje na gama da Zainab?"

"To ba damuwa. In zaki iya barinta ita kadai kije kawai, that's in kinga babu matsala da ita, nan da five minutes zanzo." Daga haka suka kashe wayar ta juya ta kalli Ramlah data kura ma bango ido bama ka gane abunda take tunani.

"Bari naje kinji? Idan Rayyan yazo kome kikeso ki fada mashi dan Allah. Karki zauna da yunwa Ramlah, kinji?" A hankali da kamar bazatayi ba sai kuma ta dan gyada mata kai dan lura da ita indai tana cikin damuwa babu abunda yake hana Lubnah shiga damuwar itama. Lubnah tashi tayi ta ida daukar duk abubuwan da zata bukata kafin ta fita dakin.

Tana nan zaune kan sallayar taji ana kwankwasa kofa, tunani ta fara ita to waye yazo wajenta ko Lubnah ake nema? Dakyar ta daga ta tashi tana bude kofar da magana bakinta wacce takeyi a hankali in ba mutum ba natsuwa yayi ba sosai bawai zaiji abunda take cewa bane ba. "Lubnar bata nan sun tafi gidansu..." maganarta tsayawa tayi a kan labbanta ganin Rayyan tsaye da ledoji a hannunshi. Numfashi tayi a hankali, rinannun idanunta kuma babu abunda sune fadi face zallar kunci da bakin cikin da take ciki. "Ina kwana?" Ta furta a hankali kafin ta kara buda kofar tayi baya saida ya shigo sannan ta rufe.

Kujerun zaman dake dakin yaje ya zauna sannan ya mata alama data zauna kan daya daga cikin kujerun. Bata mashi gardama ba, dan ba ma karfin magana take dashi ba balle har ta mishi gardama. Zama tayi amma saida ta dora kafafunta ta dora su saman kujerar, tana dora kanta saman guiwowinta.

"Ramlah ba magana? Ko duk fushin jiya ne har yanzu bakiyi hakuri ba?" Dan dagowa tayi kafin ta girgiza mashi kai a hankali. "Aa, bana gaida ka ba?"

Dan murmushi yayi a hankali, ya lura ko a hakan ma daurewa kawai take amma kuka takesan yi. Yasan tabbas rayuwarta akwai kunci tattare da ita amma baisan kaunar da Ramlah take ma kuka ba. "To naji, ya kike? Lubnah tace bakici abinci ba, gashi na kawo maki kici."

Bai tsaya ma jin ansarta ba ya dauko ledojin ya fara budewa, saida ya aje komai gabanta ta kalli abinci sannan ta dago ta kalleshi tana girgiza kai. "Bazanci ba, na koshi." Har tabe baki takeyi kamar wacce zatayi kuka.

"Dan Allah Ramlah kici, ko so kike ulcer ta kamaki ne wai?" Girgiza kai tayi ta kara furta kalmar 'Allah da gaske nake na koshi.' So take ma ta mishi maganar Abban Hanan amma kuma bataso ta mashi dan tasan Rayyan bai taba bari taje ta ga Abban Hanan.

"To ko sai na kira maki Dr Aliyu sannan zakici abincin? Koma dai ince yazo ya daukeki tun jiya sai kukan rashinshi kike mana?" Wayarshi ya fara zarowa yana ganin yanayin dake kan fuskarta.

Da hanzari ta dago ta kalleshi tana girgiza kai, "Aa nifa ba kukanshi nakeyi ba. Basai ka kirashi ba." Turbune baki tayi kafin ta janyo abincin gabanta ta faraci kamar wacce take cin guba. Maida wayarshi aljihu Rayyan yayi kafin ya zuba mata idanu. Shi baisan menene matsalarshi ba amma kaf jiya kasa bacci yayi yana tunanin rayuwarta da kuma halin da take ciki yanzu.

*

Ba yadda basuyi da ita ba amma fir Ramlah tace ita lallai bazata koma Abuja ba har sai tayi magana da Abban Hanan, karshe ma abunda ta gane shine da sun fara mata magana sai ta fashe da kuka dole suka kyaleta. Rayyan juyawa yayi ya kalli Lubnah, baifi awa ukku ya rage ma jirginsu ba, indai Ramlah bata yarda ba to saidai suyi rescheduling flight dinsu tun wuri.

"Yanzu Ramlah ya kikeso ayi?" Rayyan ya furta a hankali, sun tasa ta gaba babu abunda take banda kuka kuma can can karfinta.

"Ku kaini wajenshi, na fada maku Abban Hanan ne dan me bazaku yarda dani ba?" Wani kukan ta kara saki, Rayyan juyawa yayi ya kalli Lubnah, sunfi awa suna abu daya shi yanzu baima san abunda zaiyi ma Ramlah ba.

Numfashi Lubnah ta saki a hankali, "Naji, zan kira Zainab yanzu muji in zamu iya ganinshi amma sai kinman alkawari nima, kin yarda?" Da hanzari Ramlah ta dago tana goge hawayenta tare da daga mata kai alamar ta yarda.

"Na yarda, menene alkawarin?" Har wani murmushi ta farayi amma daka ganshi zaka san akwai kunci tattare dashi.

"Indai mukaje kukayi magana kika tabbatar bashi bane ba zaki bimu mu tafi gida sannan bazaki kara maganarshi ba, kin yarda?" Tsayawa tayi tana kallon Lubnah, da kamar tace Aa sai kuma ta tuna cewar ai shidin ne ma dan me zataji tsoron ansa alkawarin nan?

"Eh na Yarda." Zumbur ta mike tana gyara gyalenta, "Muje?" Kallonta suka dago sunayi yanda guntun farin ciki ya samu mazauni akan fuskarta tamkar ba ita bace wacce ta gama sharban wannan kukan.

Murmushi yayi ya daga mata kai, "Eh muje, Ramlah rigima." Turbune baki tayi tana kallonshi, "Ni ba rigimammiya bace. Muje Lubnah." Saida ta jira Lubnah ta mike tsaya kafin ta sargafa mata jakart tana dan murmushi.

Murmushin itama Lubnah ta mata, "To kije ki wanke fuskarki ko? Ko haka zamuje gidan mutane fuska muju muju da hawaye, Ramlah?" Yar dariya Ramlah tayi.

"Kai Lubnah, ji yanda kuke magana kamar wacce take kukan yan yara." Daga haka ta wuce toilet ta wanko fuskarta. Koda ta fito dakin har sun fita, itama fita tayi ta kulle kofar kafin ta sauka kasa parking lot. A zuciyarta dadi take ji cewar zataje taga Abban Hanan, dukda cewar kunci na kara ziyartarta idan ta tuna ba tare da Hanan zasu ganshi ba. Amma ta riga tama kanta alkawari bazatayi kuka ba, dan bataso taje yaga idanunta sunyi ja.

Har ta isa motar tana tunanin to me zata fara ce mashi? Wani tsoro kuma ta fargaba yasa tayi tsaye cak gaban motar ta kasa shiga, shin wai tama shirya ganin Abban Hanan kuwa?

Saukar da gilas Rayyan yayi ya kalleta, "Zaki shigo ko kuma wani kukan zaki karayi, a koke?"

Turbune baki tayi batasan lokacin data ce, "Kai Rayyan." Cike da muryar shagwaba.

MIJINA NE! ✅ Where stories live. Discover now