Talatin Da Tara

1.3K 212 39
                                    

"Mama bata yi sati a asibiti ba ta farko, dukda cewar ina cikin kunci amma hakan bai hanani yin tsananin farin ciki ba. Kuka kam babu irin wanda ban sha ba, gani takeyi kaman itama tafiya zatayi ta barni, duk yanda Hajia taso da in koma gida masu zuwa gaisuwa na karba a wajensu ban koma ba, dan gani nakeyi duk na matsa daga gefen Mama to zan dawo in rasata. Ana cewa gobe za'a sallami Mama da daddare sai ta fara wasu abubuwa, Hajia tace na fita na kira doctor, amma ina dawowa naga hannun Mama tana man alama da naje, rike hannuna kawai tayi saidai hawayen da take kawai, batace man komai.

Ta saba cewa ita bazata iya rayuwa babu Baba ba, amma ban taba yarda ba sai a lokacin danaji hannunta ya saki nawa, kuma likita ya tabbatar man da cewar ta rasu. Tunda Allah ya halicce ni ban taba kuka irin na ranar ba, gaba daya neman natsuwa ta nayi na rasa. Duniya ta mun kunci, to ina zan saka rayuwata? Gaba daya gatana ya fadi, duniyata ta tsaya cak. Bansan dan uwana ko daya ba, du dinne kuma Allah ya raba ni dasu." Tsayawa tayi ta fashe da wani irin kuka mai taba zuciya, ji take kamar yau ne Mama ta rasu, kamar kuma jiya ne Baba ya rasu. Yanda take kukan ba karamin taba mashi zuciya yayi ba, duk yanda yaso ya daure kasawa yayi.

Takawa yaje yayi har inda take zaune sai kuma ya tsaya cak yana kallonta da idanunshi da sukayi da kunci, bakin ciki da tarin damuwa. Tunowa yayi da shima tashi mahaifiyar, saidai yasan shi nashi kuncin bai kai nata, dan kuwa ita mai gaba daya aka mata.

A hankali ta mike tsaye, "Ba kace zaka tsaida ni ba idan ina kuka?" Da muryar kuka tayi magana, bakinta har rawa ga wani irin nauyi da zuciyarta ta mata. A hankali Rayyan ya janyo ta zuwa jikinshi. Kankame shi tayi ta fashe da kuka kaman ranta zai fita, Rayyan shiru yayi har tayi kukan da zai isheta. Sai yaji gara tayi kuka a hannunshi akan ace tayi kuka daban.

Saida ta raba jikinsu ta nufi wajen basin ta wanke fuskarta ta juyo tana kallonshi, "Abincin baiyi bane wai? Yunwa nakeji kaman naci babu."

Zuwa yayi inds take tsaye shima ya wanke tashi fuskar, "Bari na duba naga." Sukuku dai suka gama aikin suka tafi parlour, saida ta bari sun gama cin abincin tukunna sun koma sun zauna falo, shidai baice mata komai sai ta danyi gyaran murya.

"Meya faru? Zakiyi baccin ne ko kuma mu tafi gida?" Shi sai ma yanzu hankalinshi ya dawo kan abunda yake faruwa, ashe fa kafin suzo nan taga Abban Hanan kuma ta tabbatarwa kanta shi dinne.

"Bazaka ce man na cigaba ba?" Kallonta yayi ya girgiza kai, "Aa, ai kuka kike kuma kunci yana cika maki zuciya. Banaso na ganki cikin damuwa." Kallonshi tayi sai tayi murmushin karfin hali, "Idan nayi kuka kai me yake damunka?" saida ya sauke ajiyar zuciya tukunna ya mata magana, "Zuciyata kuna take, ji nake kaman duk saukar hawayenki daya kaman digon wuta ne a zuciyata, Ramlah. Banasan ganinki cikin damuwa, kinji?"

Tsayawa kawai tayi tana kallonshi, ba sai ta tambaya ba tasan tabbas da gaske yake. Murmushi ta sakar mashi mai tsananin kyan gaske, "To idan nace na daina kukan fah? Zakaji?" Girgiza mata kai, "Banaso naji, nasan daga mutuwar su Mama kika kara shiga wani kuncin, a nan kika auren wancan sakaran."

Wata irin dariya ta fashe da ita, "Kai! Miye haka wai? Mijin nawa ne kake cewa sakarai? Rayyan Abban Hanan ne fah." Yanda ta nuna da gaske ranta ya baci yasa ya jefa mata pillow ta kama tana dariya, "Ji bakka, kishin ma har da wanda bana kulawa kakeyi?" Batasan yanda akayi maganar ta fito bakinta ba, wani irin kallo ya wurga mata, "Eh hadashi, har diya kika haifa mashi ai."

Kallonshi ta tsaya tanayi, har ranta tunani take me zatace ya bashi haushi? "Yanzu idan yazo yace ni koma gidanshi fah?"

Saida ya tashi yazo har inda take zaune kawai ya fara buga mata throw pillows din dake hannunshi. Wani irin ihu take tana tari, "Kai! Kasheni zakayi ne wai? Dazun nan ka gama cewa bakaso na mutu. Wayyo Lubnah zai kasheni!" Tsayawa yana kallon yanda take dariya ga numfashinta kamar wacce tayi gudu. "Idan yace na koma zaka bari na koma?" Hararta yayi ta fashe da dariya, a hankali ta mike tayi baya daga inda yake tsaye, "To wai jika, idan har yanzu ina san miji na fah? Ni wata Hanan dinma nakeso ya kara bani, bakaga diyarshi ba sak Hanan dita?" Da gudu ya biyo ta ta ruga batasan ina bane kawai ta fada daki tayi hanzarin kullewa tana dariya.

MIJINA NE! ✅ Where stories live. Discover now