Ukku

2.2K 242 5
                                    

"Ni sunana Lubnah, bansan labarinki ba amma zan fada maki dan takaitaccen labarin rayuwata. Kinga nidai shekarata 23, sannan kuma ni ba yar garin nan bace. Banida aure sannan kuma gidannan da kika gani Mamata ta siya mun saboda nazo service a Katsina. Bamusan kowa ba nan garin dan dole na zauna ni kadai. Masters gareni amma sai yanzu nayi masters dina. Ina zaune da Mahaifiyata a Abuja, yar siyasa ce kuma yar kasuwa, mahaifina ya rasu lokacin ina shekara sha shida. Ina tunanin wannan ya isa ko?" Da dan guntun murmushi Lubnah take kallon Ramlah wacce cikin kwana daya ta wani jeme kamar ba mutum ba.

Da rinannun idanunta da zuwa yanzu ko hawayen sun daina fitarwa ta dago ta kalli Lubnah, "Ni sunana Ramlah, Hanan diyata ce." Abunda ta iya furtawa kenan. Dan fani take duk a labarin rayuwar tata babu wani abun azo a gani. Abu daya ne take alfahari dashi, shine haihuwar Hanan da Allah ya bata. Tana da tabbacin dukda cewar Allah ya karbi abunshi, amma har ta mutu bazata daina alfahari da Hanan ba a rayuwarta.

Lubnah mikewa tayi tsaye, "To Ramlah, sannu kinji? Allah kuma ya kara maki hakuri da juriyar rashinta. Bari naje na samo maki abunda zakici." A hankali ta daga ma Lubnah kai kafin ta maida idonta kan kasa tana me sauke ajiyar zuciya. Kwana daya kenan da mutuwar Hanan, amma har yanzu batajin komai a zuciyarta. Tamkar an daskarar da ruwa haka takejin ilahirin jikinta.

Mintina kadan sai ga Ramlah ta shigo cikin dakin da plate a hannunta. Ajiye plate din tayi a gaban Ramlah kafin itama ta zauna. "Dan Allah ki daure kici abinci Ramlah, ko so kike wani abun kema ya sameki? Mutuwa wata abace wacce duk wayo da dabar mutum bai taba kaurace mata idan yazo. Koda duniya zata taro tace zata maido ma Hanan ranta babu wanda ya isa. Dan Allah ki daure ki fawwala Allah komai, shine yasan yanda zaiyi da rayuwarki." Da kyar da magana me dadi Lubnah ta samu har Ramlah ta dan tsokaci kadan daga cikin abincin sannan ta koma tata duniyar. Wacce babubkomai banda kunci da tarin damuwa cikinta.

Daga nan wajen Lubnah fita tayi ta kira Mamarta, Hajia Bilki wacce ta kasance daya daga cikin yan siyasar najeriya. "Hello Mama?" Ta fada da murya me cike da damuwa. Bata san Ramlah, hasalima a daren nan ta fara ganin ta amma bata tabajin tausayin wani ya shiga cikin zuciyarta ba kamar yanda taji tausayin Ramlah a rayuwarta.

"Lubnah yan mata. To ya kike? Yaushe kuma za'a dawo gida? Nasan dai shekaran jiya kukayi passing out ko? Ki dawo hakanan, inada kyautar da zan maki." Yar dariya Lubnah tayi, tunda take bata taba ganin mutum wanda baya saka damuwa a ranshi ba kamar Mama.

"Zan dawo, Mama. Nima nayi kewarki ai sosai. Amma dai ynzu alfarma nike san na rokeki kafin na dawo din." Zuciyarta na dar dar take maganar, dukda cewar tasan bai zama lallai Mama tace Aa amma ta kasance mace mai tsantsan da alamuranta.

"To Lubnar Mama, me kuma ya faru? Me kikeso?" Ta tambaya tana murmushi.

"Mama wallahi wata mata na hadu da ita. Ko ince wata budurwa dukda dai ta fita layin yan mata amma kuma shekarunta kamar nawa ne ko ta girme ni kadan..." daga nan a hankali ta bawa Mama labarin ynda ta hadu da Ramlah da kuma abubuwan da suka faru har zuwa binno Hanan da akayi.

Sauke ajiyar zuciya Hajia Bilki tayi, "Wayyo Allah, duniya kenan duk yanda kake tunanin kana cikin damuwa to tabbas akwai wanda ya fika. Yanzu to me kikeso ayi? Ko gidan da kike cike zaa bata ta zauna?"

Da hanzari Lubnah ta girgiza kanta, "Bata fada man ba, amma daga gani bata da kowa ne Mama. Tunda in har tanada wani a rayuwarta Mama har sai ta nemi me rufe mata gawar diyarta? Kuma wai a bata gidan nan duk bashi bane ba, Mama. Dan a yanayin da take ciki tana iya kashe kanta in har aka barta ita kadai. Dan Allah in taho da ita gida?"

Dan jim Mana tayi kafin a hankali ta daga kai, "In kince hakan bazance Aa ba Lubnah. Tunda nasan a halinki ma in nace Aa to tabbas zan rika neman in rasa ne, kice kin taho Katsina duba Ramlah. Ba komai, ki taho da ita, Allah ya bamu ladar taimako." Da farin ciki Lubnah tayi ma Mama godiya kafin ta koma dakin daga baro Ramlah ta zauna kusa da ita.

Hannayent ta riko tana murmushi, "Ramlah in tambayeki dan Allah?" Ta furta a hankali tana dan kokarin tayi murmushi.

Zuba mata idanu kawai Ramlah tayi bawai dan tana da tabbacin zata bata amsa ba. Dan ita yanzu ji tke bama zata iya magana ba. "Yanzu idan nace ki bini gidanmu zakije? Bansan ko kinada inda kikeso na kaiki ba, ko gidan yan uwanku ko wani wajen."

A hankali ta fara girgiza kanta, "Banda kowa Lubnah, Hanan kadai gareni itama ta tafi." Tana fadin hakan wash hawayen suka fara zarya saman kuncinta.

"To zan dauki hakan a matsayin amsa. Idan kinada abunda kikeso ki dauka sai muje ki dauka kinji? Insha Allahu Allah bazai barki haka nan ba." Haka akayi. Dakyar da lallami Lubnah ta samu Ramlah ta kaita dan dakin da suka kama. Ba komai ta dauka ba sai yan tarkace kadan suka fita.

Washe gari da sassafe suka kama hanyar Abuja. Dukda abun ya baga mamaki cewar Lubnah da kanta ta tukasu har Abuja, amma bata da natsuwar da zata lura da hakan. Koda suka tsaya a kan hanya iyakarta yin duk abunda Lubnah tace. In sallah ce to, in abinci ne shima haka. A haka har suka isa gida, koda suka shiga gidan Ramlah ta daga tai ma harabar gidan kallo daya ta sauke idanta.

Da fara'a Lubnah suka gaisa da maigadin yana mata barka da dawowa haka zalika tana me umurtar shi daya shigo masu da kayansu. Har falon Mama na sama Lubnah ta kaita kafin ta shiga daki dan kiranta. A tare suka fito fuskarsu cike da annuri da murmushi. Zama Mama tayi, a hankali Ramlah ta daga ido tana kallonta.

"Ina yini Hajia?" Ta furta a hankali.

Hajia Bilki murmushi tayi tana dan murmushi. "Ki kirani da Mama, Ramlah. Lubnah ta fadaman cewar diyarki ta rasu ko? Allah ubangiji ya jikanta, ke kuma ya baki ikon hakurin rashinta."

Dukar da kanta tayi, sai taji wani nauyi a cikin ranta. Da gasken dai Hanan ta rasu kenan? "Nagode, Mama." Abunda ta furta kenan, tanajin wani daci dake ziyartar ruhinta.

Mikewa tsaye Lubnah tayi, "Muje in kaiki daki, Ramlah. Kiyi wanka ki dan huta sai ki sauko muci abinci kinji?" Ita dai binta kawai tayi. Taga kyau da girman dakin, amma banda nagode babu abunda take iya furtawa.

Har Lubnah tazo fita Ramlah ta juyo tana kallonta, "Nagode sosai Aunty Lubnah, Allah ya saka maki da mafificin alkhairi." Dawowa cikin dakin Lubnah tayi tana wani kayataccen murmushi, "Dan Allah ki daina karma wani yaji, miye wani Aunty? In baki girmeni ba to zamuzo shekaru daya dake Ramlah. Sunana Lubnah kinji? Ki shiga kiyi wanka."

Koda Ramlah ta fito wanka gani tayi an kawo mata kaya akan gado hada na bacci, tasan Lubnah ce, dan jikinsu kusan zai kama daya in baccin yanzu da duk ta rame ta lalace. Doguwar riga ta saka kafin ta tada sallah. Tana gamar sallar kamar a zaunar da ita inda take, ita batayi kuka ba sannan ita bataji komai a ranta ba. Tamkar wacce aka tsiyayar da dukkan wani abun ji da ganewa na jikinta.

Dan kwankwasawa akayi a kofar kafin Lubnah ta shigo itama cikin dagowar riga me laushi tana daura dankwalin kanta. "Kin gama? Muje Mama na jiranmu."

Tasowa tayi ba dan taso ba, dan ita inda so samune ma to su barta kawai ta zauna dakin nan har illah masha Allahu. A tare suka sauka kasa Lubnah tana dan nunnuna mata abubuwa na gidan, ita dai ba wani ganewa takeyi ba. Kan dining din suka iske Mama ita da wani suna gaisawa cike da girmamawa.

Zama sukayi Lubnah tana kallon Mama kafin ta juya ta kalleshi, "Mama kamar Rayyan ko?"

"Eh shine, dama banace maki inada kyautar da zan maki ba? To Rayyan dai ya dawo Abuja, dakyar nida Alhaji Hameed muka samu ya yarda zai zauna nan gidan." Lubnah ta taba ganinshi sau daya a wani taron siyasar su Mama data halarta. Sunanshi Rayyan Hameed Ibrahim, babban dan Alhaji Hameed wanda ya kasance abokin siyasar Mama.

Juyowa tayi ta kalleshi, "Allah sarki, muna maraba da babban bako. Sannu Rayyan." Ta furta da murmushi mai kyau kan fuskarta.

"Nagode, Lubnah." Ya amsa yana mayar mata da murmushinta. Suna yar firarsu sama sama haka suka fara cin abincin, yawancin firar ma da Mama da Lubnah suke abunsu. Dan ta Ramlah ma bazata iya cewa ga abu daya da suka tattauna akai ba. Karshe ma ji tayi in har ta kara minti daya nan wurin babu abunda zai hanata suna, mikewa tayi a hankali ta kalli Lubnah da Mama.

"Zanje na kwanta. Saida safenku." Suka amsa mata da murmushi. Sai bayan data wuce a tare suka furta, "Allah ya kawo maki sauki, Ramlah." Basu santa ba, amma tausayinta sukeji.

MIJINA NE! ✅ Where stories live. Discover now