Hamsin Da Daya

1.6K 189 59
                                    

Zaune take tana dan juyawa tana kallon yanda office din yake, Lubnah tasan ba yau bace rana ta farko data fara shigowa office dinshi ba amma kuma sai yau ta natsu take lura da yanda wajen yake, ko dan kyaun da wurin yayi da tsari? Ko irin tarkacen takardun nan da likitoci ke tarawa shi nashi a kimtse suke waje daya. Murmushi tayi, a zuciyarta kuma Allah Allah take ya taho, ta kirashi yace a bude mata office din yaje ward round gashi nan yanzu zai gama.

Tana cikin wannan tunanin ta jiyo maganarshi a corridor din da alama hanzari yake dan umurni yake badawa kafin ya bude kofar. Kamar wata karamar yarinya haka ta mike da tsalle ta rungumeshi. Dariya Dr Aliyu yayi kafin ya rungumota yana rufe kofar office din da kafarshi. "Nayi missing dinki sosai da sosai, Lubnah." Wani taro taje port harcourt kwananta biyar. Duk kwanakin da tayi bata gida ji yake kamar yayi tsuntsuwa ya bita, kullum cikin waya suke idan kuma aiki ya mishi yawa to tabbas suna chatting.

Dariya tayi tana kara makalkaleshi, "Kasan yanda nakeji wai? Kamar zuciyata ta fito." Dariya yayi ya dako da ita yana kallon fuskarta, har zuwa yanzu hannayenshi na rungume da ita. "Kinyi haske kin kara kyau, kodai wayau kika man kikaje kina cin dadinki?" Dariya tayi tana girgiza kai kafin a hankali taji saukar labbanshi saman goshinta.

"Ba nace ki kirani nazo na dauke ki a airport din ba? Ko duk missing din nawa ne yasa bazaki iya jira ba?" Daga kai tayi tana lumshe idanu dan sai yanzu data ganshi hankalinta ya kwanta ta gane irin gajiyar da tayi ga wani baccin wahala da yake neman karya jikinta. "Na kosa na ganka sai nayi bolt kawai nazo nan. Mu tafi gida, ko baka gama ba?"

Dariya yayi yana aje abu saman table dinshi kafin ya dauko makullin motar. Hannayensu rike dana juna kowannnen su farin cikin dake zuciyarshi bazai misaltu ba. Watansu ukku da aure amma irin farin ciki da kwanciyar hankalin da suke ciki basu taba tunanin zasu sameshi ba. Shi ya bude mata kofar saida ta shiga ta zauna kafin ya zagaya ya shiga mazaunin driver yana tada motar. Fita sukayi daga asibitin ya juyo yaga yanda ta lafe kan kujerar, dukda cewar da murmushi kan fuskarta amma kallo daya zaka mata kasan ba karamar gajiya tayi ba, idanunta rufe ruf alamar bacci.

"Anya kuwa Lubnah? Tun kafin ki tafi kike wannan yawan kasalar balle ace gajiya ne." Sauri tayi ta bude idanunta, dan ita kam batasan yan maganganun nan. Lura da yanayin fuskarta yasa ya fashe da dariya, "Ba daidai na fada ba, koma kiyi bacci ranki ya dade ai kin gaji dayawa." Yanda yayi maganar sai ya bata dariya. Pharmacy ya tsaya ya siya bau ita dai bata san menene ba, daga nan kuma taga yayi parking kofar gidan Hajia.

"Na dauka gida zamu nayi wanka na chanza kaya." Dan girgiza kai yayi a hankali, "Hajia tace mu biyo mu karbi abinci tunda yau dai kam bazakiyi girki ba ai. Hafsah kuma ta dameni idan kin dawo nazo na kawota, to idan mukazo yanzu ta ganki shikenan ba sai na dawo anjima ba, sai muyi zamanmu har dare tare." Murmushi kawai tayi suka fita suka shiga gidan tare. Sai ta tuno ranar data fara zuwa gidansu Aliyu, tsabar fargaba dakyar take daga kafa tana tafiya dan ita a tunaninta bazasu taba amsarta ba tunda su kam Ramlah suka sani.

Amma tunda take bata taba ganin mace mai mutunci da kirki irin na Hajia ba, bata taba ma nuna mata cewar ai ba ita da Aliyu zai aura ba. Karshen soyayya tana ganinta wajen baiwar Allar nan, dan wani loacin haka kawai zata kirata tace mata tayi abincin gargajiya yau ba sai tayi girki ba tunda ga aiki, kawai idan ta tashi tunda tana rigan Aliyu tashi ta biyo ta karbar masu abincin. Lubnah ba karamin dace tayi ba da rayuwar aurenta, dan koda auren soyayya tayi kila sai an samu matsala. Amma yanzu watansu ukku da aure ko sau daya basu taba samun sabani dashi ba.

Zaune suka samu Hajia falo ga Hafsah gaban tv tana kallon tana cin abinci ita kuma Hajia tana latsa wayarta. Dagowa tayi ta gansu da hanzari Lubnah ta zare hannunta daga nashi. "Mutanen port harcourt, Allah yayi?!" Murmushin dake fuskar Hajia wani irin kayatacce ne. Lubnah takawa tayi har inda take ta duka zata gaisheta Hajia ta mikar da ita tsaye ta rungumeta tana dariya, "Lubnah na fada maki bani san yan duke duken nan. To ya hanya? Kamar ma ko gida bakuje ba?"

MIJINA NE! ✅ Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang