Talatin Da Bakwai

1.3K 199 35
                                    

Kina ina kawata? Ramlah! Mrs Tilde❤️ Wannan shafin kacokam naki ne, Maman Hanan. Allah ya bar kauna da soyyayya tsakaninki da Baban Hanan, saidai shi Baban Hanan dinki dan Aljanna ne. Amma Abban Hanan din Ramlatu ta Rayyan saidai a hankali😂❤️ Ina sanki kawata❤️

Fira suke har suka isa wajen saida laces din, da kyar Lubnah ta samu ta zabi wanda takeso shima saida Ramlah ta dage akan in har ta bari wannan ya wuce mata to tabbas bazata samu wanda ya kaishi kyau ba. Saida suka biya wajen Dazeita sukayi booking makeup nasu duka, duk yanda Ramlah ta kaiga gaddama akan ita ai ba bridal makeup zatayi ba, Lubnah kin yarda tayi, biyan kudin sukayi tukunna suka koma gida a gajiye.

Da daddare bayan isha'i sai ga kiran Dr Aliyu, lokacin kuwa suna tare suna cin abincin dare Mama sai shan labarin Lagos takeyi. Tana dauka yace mata gashi yazo ta kashe wayar tayi hanzarin mikewa, "Mama, idan na dawo zan cigaba da baki labarin, yazo."

Mama tsayawa tayi tana kallonta tana yar guntuwar dariya, "Waye yazo haka Ramlah duk kike ta zumudi?"

Caraf Lubnah ta amsa, "Waye kuwa inba mijinta ba, Mama? Wannan baiwar Allar ki barta kawai, shine wai dan nayi mana booking makeup bridal mu duka take kunkuni wai ita ba yanzu zatayi aure ba nan kusa, kiji mata." Dariya suka fashe da ita a tare. "Yi maza kije kinji diyata? Ki shiga dashi falon baki a daina zancen motar nan bana sanshi."

"Ah toh, dan wallahi ni ban yarda da wannan zancen ba cikin duhu babu me gani sai Allah. Dan wannan uban zumudin dake dashi bansan gwani ba." Turbune fuska Ramlah tayi tana niyar kai mata duka ta goce. Mama ce tana dariya take fadin, "Rabu da ita mana Ramlah, imma zumudin ne ai babu wanda ya kaita, in kinga haukan da tayi ranar da aka saka bikin nan zaki mamaki. Ai ban yarda dasu ba nima, zance yazo ya koma gidanshi kafin zance ya chanza."

Wata irin dariya Ramlah tayi tana mata gwalo. cikin hanzari ta shirya ta feshe jikinta da turare tukunna ta fita ta bude falon bakin. kiranshi tayi a waya akan ya shigo, fuskarta cike da murmushi. Da motarshi ya shigo har saida yayi parking tukunna ta tako inda yake, murmushin dake kan fuskarta a bayyane yake kamar karamar yarinya wadda ta dade bata ga babanta ba sai lokacin. Ji take kaman ta rungume shi tsabar dadin ganinshi da tayi.

"Allah nayi kewarka sosai ba kadan ba." Dan narke murya tayi tana dariya kaman yarinya. "Sai naga kaman ka chanza ma."

Tsayawa yayi yana kallonta sosai, ji yake kaman ya rungume ta, "Ramlatu bakuwar haure, sai yau Allah yayi?" Dariya tayi tana mashi hararar wasa, "Nima dai nayi kewari sosai, kaman na saceki na gudu nakeji."

"Kana saceni zan kurma ihu, Lubnah bazata bari ka tafi dani ba ai." A hankali suka fara takawa suna yar fira, "Haba ai akwai ranar da ita da kanta zata kawoki wajena."

Saida ya zauna ta bude fridge ta dauko mashi ruwa da lemu tukunna ta zauna a kujera da ke kusa dashi, "Toh fah, gajiya zatayi dani kenan?"

"Aa, bakisan akwai stage din da idan mace ta kai ba ake gajiya da ita? Nan kiris ya rage Mama tace inzo in tafi dake, nace a dai jira ki dawo." Dariya ita abun ya bata, "Yo haka kawai sai ka tafi dani? Ni ban taba ji ba ai."

"Idan na aureki ai dole kowa yazo yace in tafi da Matata ko? Ko zaki zauna nan ne ni kuma ina can gidanmu?" Dariya tayi, ita sai yanzu ma hankalinta ya dawo kan maganar da yakeyi. "Eh gaskia, shine daidai ai. In zauna gidanmu iyaka ka kawoman diyata."

"Kin yarda ayi auren kenan?" Kallonta yake cike da so da kauna, ita tunda take bata taba lura da kallon da Dr Aliyu yake mata ba face yau. Gabanta taji ya fadi, "Eh na yarda, amma in ka yarda in zauna gidanmu ko?"

Yar dariya yayi irin ta yarinya zaki gane kurenki, "Na yarda. To zan turo su Baba. Da gaske fa nake, Ramlah." Koda ta kalleshi bataga alamar wasa tattare dashi ba, shi har kasan ranshi da gasken yake. "To ai nima ba wasan nake ba, kowa yana gidanmu. Saidai kazo mu gaisa sai ka tafi, shikenan."

MIJINA NE! ✅ Where stories live. Discover now