Ashirin

1.4K 198 3
                                    

Maganganun da Dr Aliyu ya fada mata jiya ba karamin amfani suka mata ba. Koda ta dawo cikin gida bacci ta kwanta tayi badan tanaso tayi, tolasta kanta tayi sai can cokin dare ta tashi tana sallah kamar ynda ya bata shawara. Yin hakan kuwa ba karamin amfani ya mata ba, dan kuwa koda ta farka yau zata iya cewa ranta ya saki sannan tana jin natsuwa cikin kirjinta. Kasa bacci tayi sai yasa ta sauka kasa domin hada masu abincin safe, tasan akwai masu aiki, kila ma harsu yanzu basu tashi ba amma tanuwa da tayi Lubnah zatayi fitar wuri yasa taje domin ta hada mata kar ta fita babu komai cikinta.

Karatun Kur'ani ta saka a hankali tanabi tana girki, koda me aikin abincin ta shigo kitchen din cewa tayi taje ta cigaba da baccinta yau zata hada komai. Ba karamar godiya ta mata ba kuwa, dan dama a gajiye take. Ramlah aikinta ta cigaba dayi cikin natsuwa tana gamawa ta fita taje dakinta tayi wanka, wajen karfe bakwai da rabi ta kwankwasawa Lubnah kofa.

"Kin tashi ko?" Abunda ta furta kenan bayan Lubnah ta bude mata kofa sai ganinta tayi da tawul a jikinta alamar ta fito wanka. "Inata sauri kar ace kin makara ashe ma har kin tashi."

Ita dai Lubnah tsayawa tayi tana kallonta, dan bazata tantance cewar wannan Ramlah ce ko ba ita ba. Wai shin ba ita bace jiya kamar Allah ya dauki ranta ta huta? Amma ga yanda take murmushi ynzu da natsuwa tattare da ita. "Ke kodai gizo idona keman?" Kasa boye mamakinta tayi, wanda hakan yasa Ramlah da ta fara gyara mata gado ta fashe da dariya.

"Sallar dare nayi fah, kuma yan maganganun Dr Aliyu sun taimaka man sosai. To Allah ya taimake ni ya saukar man da natsuwa, dama ba haka kukeso ba?" Murmushi me kayatarwa ne saman fuskarta, wanda dukda Lubnah tana zaune bakin mirror saida ta juyo ta daga mata kai itama tana maido mata da murmushin.

"Alhamdulillah, sai ki daure kita adduar, Ramlah." Lura da tayi da gyara gadon da take yasa ta fara magana, "Tsaya, ki daina gyaran gadon mana anjima zasu zo su gyara."

"Aa yau yan aikin nake san yi. Kiyi sauri ki shirya." A haka suna yar fira Ramlah ta gama gyara dakin ita kuma ta gama shiryawa tsab suka fita dakin tare. "Su Mama yau kila sai Sha biyu za'a tashi, jiya bat dawo da wuri ba ai." Dariya sukayi tare, sunsan data farka zata fara mita kan irin gajiyar da tayi da yadda baccin baima isheta ba ita.

Kan dining suka zauna Ramlah ta bude kulolin abinci, "Ni nama manta yaushe rabon dana girka wannan abun, ci kiji in har yanzu na iya." Da hanzari Lubnah ta mika mata plate dinta tana murmushi. "Ai baka manta yanda ake girki Ramlah, ni zanzo ma in fara daukar darasi gaskia."

Suna dariya suna cin abinci Lubnah sai sauri take dan kuwa ta kusa makara. Ta mike tsaye kenan zata wuce sai ga Rayyan ya shigo, suna hada ido ta sakar mashi murmushi shima ya mayar mata. "Kardai har zaki wuce, Lubnah?"

"Na makara ma a hakan, Rayyan. Restaurant din wurin office dinku zanzo lunch yau, in kiraka in nazo?" Gyada mata kai yayi kafin ya jira ansarta gudu gudu sauri sauri ta fice tana fadin "Sai na dawo Ramlah!"

"To Allah ya tsare!" Da yar dariya Ramlah ta bata amsa kafin ta maida idanta kan plate din dake gabanta. Data sani bata tsaya labari ba tun dazu taci abincinta, yanzu gashi bata koshi ba ga kuma Rayyan. Ita fa har yanzu haushinshi takeji.

"Ina kwana." Can kasan ranta ta hida shi shima dan bata iya banza ta kyaleshi shiyasa. Tsayawa yayi ya harde hannaye saman kirji yana kallon yanda ta wani yi kicin kicin da fuska kamar wacce akai wa mugun laifi ita ala dole fada suke dashi. Abun sai ya burgeshi baisan lokacin da yayi murmushi ba, yanda take wani turo baki tana yan abubuwa.

Jin bai ansa ba yasa ta dago taga ko yabar falon, kila shima haushin abunda ta mishi yaji ko? Tana dagowa tana yanda yake kallonta hankali kwance. Saurin dauke idonta tayi, "In bazaka ansa gaisuwa ta ba ai basai ka kureni da ido ba."

Jin ya kara shirun yasa ta kara dagowa kamar wacce zatayi fada amma kafin tayi magana ya rigata, "Wai Ramlah yaushe kika fara tsiwa haka?" Wata hara ta galla mishi ta dauke idanta. Ita haushin kanta ma takeji yanzu, sai wani abu take kamar yar yaye kuma batasan yanda zatayi ta hana kanta abu ba indai wajen Rayyan ne. "Harara ta kuma aka dawo yi yau? Allah ya baki hakuri, yanzu dai zuba man abincin ko shima hanani zaayi?"

Kamar bazata zuba ba amma dan ta nuna mashi ita fa ba yar yarinya ba bace yasa ta tashi ta zuba ta aje mashi gabanshi kafin ta koma ta zauna. Yi yayi kamar baiga abincin ba ya tsaya kawai yana kallonta. Tunani yaketa yi wai shin me yayi mata ne? Shidai yasan har suka shiga gidan Zainab lafiya lau suke da Ramlah. Dagowa tayi taga baima taba ko cokalin ba.

"Nikau har ga Allah banisan kallo. Kuma idan abincin yayi sanyi ba dadi zai maka ba." Bata dauke idanta ba a kanshi, dan yanda yake takura mata da kallo kila in ta fara kallonshi shima yaji ya tsani kanshi.

"To ai inata tunanin laifin dana maki ne da kikejin haushi na." A hankali ya fara cin abincin, dan ya fahimci kallon da take mashi dan taga ya fara cin abincin ne.

"Nace maka tun jiya babu laifin daka mun, kawai na fita harkar maza ne su duka." Kash! Danme zatayi wannan maganar? Yanzu shikenan taja ma kanta tasan tabbas sai ya mata maganar abunda ya faru jiya. Wai meyasa ba kowane lokaci ta cika wayau bav kamar ta shake kanta ta mutu.

Yar dariya yayi, dama tasan zaa rina ai. "Oh, an tsani maza dayake shi Dr Aliyu ba namiji bane? Halan shi anmai wata lamba ta daban da bamuda ita?" Dagowa yayi daidai lokacin idanunsu suka hadu, da hanzari Ramlah ta dauke idanta daga kan nashi.

"Ni bance ba," ta fada can ciki kamar ta cigaba, "Nifa haushin daka baki dan ka hana naga ko wancan mutumin yanada tabon nan, yama sunanshi?"

"Wai Yassar?" Ya tambaya a hankali, sai yanzu ya gane duk inda ta dosa, wato wani abun idan Ramlah tayishi kamar yar shekara goma.

"Eh shi. To ni haushi ka bani gaskia, amma yanzu ya wuce bama sai kace nayi hakuri ba. Dr Aliyu yace..." guntun tsaki ya saki wanda bai shirya yinshi ba saima gaba daya ya mike tsaye.

"Ni da kin fada kan tuntuni ai da na baki hakuri. Yanzu dai Ramlah kiyi hakuri, zunubi na hanaki aikawata ba wani abu ba. Zan wuce." Abincin ta kalla ta kalli yanda yayi kicin kicin da fuska.

"Wai dan nace Dr Aliyu shine..." wai ita kau indai batayi wayau a shekara 24 ba yaushe zata yi wayau? Wane irin sakarci ne haka? "To shikenan, sai ka dawo Allah ya tsare." Bai ce kala ba ya fice daga falon wani murmushin mugunta tayi, ai ba ita kadai keda zuciyar jin haushi ba.

Dakinta ta koma, dama Dr Aliyu ya bata shawarar ta fara editing pictures din biki hakan zai dauke hankalinta. Hakan kuwa tayi, duk hoton data gani sai tayi murmushi, sudai kyau garesu gasu yan gayu. Yanda taga Zainab na murmushi duk hotonsu da Mijinta sai taji inama ita. Daka gani zakaga tsantsar soyayyar da suke ma juna basai an fada ba.

Wai shin itama zata samu wanda zai sota haka? Ita dai kan ta taba so, so kuwa mai tsanani amma ba'a maida mata soyuyar ta ba. Saiyasa yanzu ita kalmar soyayya in har an alakanta ta da ita tsoro abun yake bata. Maza sukan so jikinka, wani abu naka, ko sh suko dan ace kaine masoyinsu, amma so na gaskia wanda bashi da dalili yana da wuyar samuwa, ita kuma irinshi takeso.

A haka dai tana zaune har yar waka ta saka, dan ta lura tunani zata saka ranta. Wayarta ce tayi ringing tana dauka Lubnah ke magana, "Ramlah na manta na fada maki, na tura ma Driver address din wajen zai kaiki kuje kiga shagon dana fada maki, idan wurin ya maki sai a kama hayarshi. Idan kuma baiyi ba to sai mu nemi wani."

"Ai yama yi kawai Lubnah, dan Allah bar zancen rashin yi." Yar dariya Lubnah, Ramlah dai har abada bazata chanza ba. "Yanzu dai kuje toh. Idan yayi already na tura masu gyaran shago sai su nuna maki designs, ke ki zabi komai dai ku gama magana dasu. Bye! Zan shiga meeting!" Da ihu ihu ta karasa maganar, Ramlah na aje wayar tana murmushi. A duniya bata taba ganin mutum kamar Lubnah ba, kuma batajin tanasan wani kamar yanda take san Lubnah.

Kullum burinta Allah ya dawwamar da Lubnah cikin farin ciki, tunowa da tayi da hakan yasa ta tura mata text. 'Lubnah, kija hankalinshi dai yau. Dan Allah ki dawo mana da kyakyawan labari gida, kinji? Ke yama isa? Dole fa ya fara sanki!' Fatanta kullum Allah yasa Rayyan yaso Lubnah, dan in har yasata cikin kunci saboda bai maida mata da soyayyarta ba to tabbas zata tsaneshi tsana kai tsanani.

Hmmm...Su Malama Ramlah Manya.

To mudai TeamRR ne, ehe!

MIJINA NE! ✅ Where stories live. Discover now