Ashirin Da Shida

1.3K 250 98
                                    

Magana ya fara mata a hankali cikin natsuwa, ita dai Ramlah bata tanka shi ba dan kuka take bil haqqi kamar yau tayi rashin Hanan. Dan numfasawa yayi kafin yayi shiru ya tsaya kawai yana kallonta, jin shirun nashi yayi yawa yasa Ramlah ta juyo tana kallonshi sai taga ai ita yake kallo. "Kayi shiru." Maganar ma dariya ta bashi, sai da yayi yar dariya tukun ya bata amsa, "To Ramlah ya kikeso na miki? Naga ai kamar dadin kukan kikeji ko?"

Da sauri ta turbune fuska tana girgiza kai, "Kawai inaso kaita magana ne, sai inji raina na mu sanyi. Ko har ka gaji?" Zuwa yanzu hawayen nata sun daina zuba, itama juyowa tayi na yanda zasu fuskanci juna. "To inta magana me zance? Hakuri zanta baki ke kuma kina kukan ai ko?"

Hannayenta duka biyu tasa ta goge sauran hawayen dake kwance kan kuncinta, "Na daina kukan yanzu ai. Ka bani labarin Maman Hafsah." Sai bayan tayi magana ta lura fuskanshi ya chanja sai kuma taji dama bata yi ba. Sai a lokacin take jin haushin kanta, kullum itace tasa bawan Allahn nan gaba tana mashi kuka bayan shima fa yayi rashin nan a rayuwarshi. "Yi hakuri, muyi wani maganan na daban."

Murmushin karfin hali ya mata yana girgiza kai, "Nima yau ki zama therapist dita, I'm just realizing ban taba maganar ta da kowa ba tun bayan rasuwarta." Dan daga mashi kai tayi a hankali tana kallonshi. Magana ya fara kamar wanda be san ayi, "Sunanta Fatima, kuma tanada kyau kamar ita tayi kanta. A makaranta muka hadu, itama likita ce amma bangaren mata. Tunda nake ban taba ganin mace kamar Fatima ba, ga sanyin rai, ga fara'a..." saurin tsaida kanshi yayi, dan lura da yayi tunano suffarta da halayyarta zai iya haddasa mashi wani ciwon a zuciya. "Anyways, da kawata ce kawai muan haduwa wajen karatu daga nan muka zama abokai sosai da sosai har naji na fara santa. Koda na fada mata ina santa bata ce bata so na dan itama ta dade tana kaunata. Daga nan muka fara soyayya mai tsanani tsakaninmu amma lura da nayi kullum santa karuwa yake a zuciyata haka zalika kusancinmu yana karuwa, nasan tabbas wata rana dole shedan yayi galaba tsakaninmu, hakan yasa na nemi shawararta akan inaso nawa Baba magana aje gidansu a nema mun aurenta.

"A farko kamar bazata yarda, dakyar na samu nayi concinving dinta ina nuna mata hadarin soyayyar da muke a wata kasa da babu wanda zai fada mana muji kuma kusan ko yaushe muna tare bacci kawai ke raba mu. Koda su Baba sukaje wajen iyayenta basu fito gidan ba saida aka daura aure. Tunda nake ban taba farin ciki irin na ranar ba a rayuwata." Tunda ya fara magana Ramlah bata ga murmushin shi ba sai a lokacin. Wanda daka gani kasan cewar har yanzu farin cikin ranar yana tattare dashi kuma bazai taba mantawa dashi ba.

"Kinsan miye abun dariya?" Girgiza kai tayi, tana mamakin yanda dariya ke san subuce mashi bayan su dukansu sunsan wannan labarin ba'a dadi ya kare ba. "Tunda na fada cewar an daura mana aure itama yan gidansu suka fada na daina ganinta, ko makaranta muka hadu rugawa take idan na tambayi friends dinta sai suce wai kunyata takeji. Tun abun yana bani haushi har yazo yana bani dariya dan ita da gaske kunyar tawa takeji. Ranar dai naje dakinta a hostel nayi sa'a a bude, dan kuwa ko bude bata barinshi tun abun, tana zaune tana cin abinci ga littafi gefenta tana karatu." Shiru yayi daga nan.

Ramlah juyowa tayi tana kallon yanda murmushi ke kwance kan fuskarshi, "Me kake nufi?"

"Bazan ida baki labarin ba ai." Batasan lokacin data banka mashi harara ba. Dan daga ganin murmushin dake fuskarshi da kuma kallon dake idonshi kasan tunano abubuwa yake wanda suke faranta mashi rai. "Yo har ma ka isa? Nan ji nake kamar ina karanta hausa novel sai murmushi nake inaso in ji yanda amaryarmu ta kare. Ai wallahi ci gaba kawai."

Dariya ya farayi ganin ita fa da gaske take dan yasan nan da yan mintuna haushi ma zata fara ji, "To in inajin kunyarki fa?" saida tayi yar dariya tukunna ta daga kai, "Cire kunyar na yafe maka na yau kawai." Dan daga kafada yayi alamar ke kika siya da kudinki. "Idan na fara bazan tsaya ba, kin yarda?" Da zakuwa ta daga mashi kai alamar na yarda, "Nidai fada man koma menene inaji."

MIJINA NE! ✅ Where stories live. Discover now