Goma

1.6K 218 13
                                    

Tsaye sukayi, itadai kallonsu kawai takeyi. Tasan dai a kanta suke magana amma bazata iya cewa ga abunda suke cewa ba. Kallonsu kawai take, wani lokacin kuma bata sanin lokacin da hawayenta ke zubowa saidai taji kuncinta sun jike amma sai tayi hanzari share hawayen dan kuwa batama san suga kukan nata.

"Ni yanzu kaga an kirani dole inje Lagos, dukda yau zan dawo amma Rayyan dole mu kai Ramlah asibiti yau. Ko zakaje da ita dan Allah?" Jiya Lubnah ko nan da can bata matsa ba, yanda taga rana haka taga dare sai bayn asuba da taga Ramlah tayi bacci shine t dan runtsa. Taso ace yau it da kanta zata kai Ramlar asibiti amma hakan bai yiwuwa, dole taje Lagos dan ta wakilci ma'aikatar su.

Rayyan juyawa yayi ya kalli Ramlah wacce sai share hawaye take tayi wani zuruzuru da ita kamar mutum mutumi. Wayarshi ya zaro ya tura ma sakataren shi sako cewar bazai samu damar zuwa ba. "Ba damuwa, kiyi sauri kar kiyi missing flight dinki. Karki damu zan kula da ita insha Allah."

Godiya Lubnah ta mishi kafin ta karasa inda Ramlah ke tsaye ta rungumeta a hankali, "Dan Allah ki saki ranki, Ramlah. Zan tafi sai na dawo kinji?"

Dan dagowa Ramlah tayi tana mata murmushin yake, "Insha Allahu. Sai kin dawo, Allah ya tsare hanya."

Daga haka Ramlah na gani Lubnah ta wuce wajen mot direba yaja suka tafi. Juyawa tayi taga Rayyan kallonta kawai takeyi, "Muje ko?" Abunda ya furta kenan kafin ya nufi motarshi. Bata mashi gardama ba suka shiga motar suka nufi hanyar asibiti.

Tafiya suke ita dai kallon titi kawai take, abunda bata sani ba shine Rayyan kallon duk wani motsi nata yakeyi, ganin ta fara hawaye yasa ya samu gefen titi yayi parking motar, bata san sun tsaya ba har saida akayi yan mintuna kafin ta juyo tana kallonshi, "Mun iso asibitin ne?" Ta tambaya tana waige waige sannan tana kokarin share hawayenta. Hankici ya mika mata ta karba ta goge hawayenta.

"Bamuje ba, sannan baza muje ba. Ki share hawayenki akwai wajen da zan kaiki." Abunda ya furta kenan ita dai iyakarta dashi ido kawai. Taka motar yayi ya chanza masu hanya, tana kallon titi bawai dan tana gane hanyar da suka nufa ba. Abun bai bata tsoro ba saida taga Rayyan yayi parking, basai ta tambaya ba ko yaro yazo wajen yasan inane.

"Makabarta?" Abunda ta tambaya kenan, bai amsata ba saima fita da yayi daga cikin motar ya zagayo ya hude mata kofar.

"Fito." Jiki a sabule Ramlah ta fito tabi bayanshi a hankali suna takawa. Saida suka tsaya bakin makabartar suka karanta addu'ar shiga makabarta kafin ya taka ya shiga. Ita dai jikanta duk yayi sanyi, batasan ma'anar Rayyan na kawota makabarta ba, amma tabbas tasan babban al'amari ne.

Saida sukayi yar tafiya kadan kafin suka tsaya suna kallon tarin kaburbura. Juyowa yayi yana kallonta, "Ramlah, ki kalli kaburburan nan, wasu daga cikinsu attajirai ne, wasu manyan mutane ne, wasu talakawa ne. Amma me, duk gasu nan waje daya a hali daya. Allah kadai yasan adadin wadanda sukeso ko na sakan daya ne Allah ya maido masu ransu dan suyi amfani da damar su samu biyan wata bukata tasu. Allah kadai yasan irin nadamar da dayawa cikinsu suke dan kin amfanuwa da lokacin da Allah ya ara masu da basuyi ba a duniya, Ramlah.

Haka kikeso rayuwarki ta kasance? Sai lokacin da nadamarki bata da amfani kikeso ki gane irin rahamar da Allah ya maki? Bansan labarinki ba, amma kowa ya ganki yasan tabbas kin shiga kunci, amma kuma hakan baya nufin da ki nunawa Allah butulci, Ramlah, ya barki da ranki, shin hakan baki lura wata dama ce wadda dubbannin mutanen da suka rasu suke nema ba?" Magana yake mata wadda tunda aka haifeta bata taba jin irinta ba, jikinta yayi sanyi, kukan ma daina yinshi tayi. Kallonshi kawai takeyi sai can kuma ga juya ta kalli tarin kaburbura. Nan wasu cikinsu yara ne, wasu mata ne, wata ya'ya ne, wasu uwaye ne wasu kuma ubanni ne, akwai shugabanni, akwai sarakuna...babu wanda baza'a samu ba.

Daga makabartar nan asibiti ya kaita, wajen accident and emergency ya shiga da ita. Ita dai binshi kawai takeyi da ido, haka ya rarraba ma mutane masu jinya kudi, karshe ma dawowa yayi inda tayi tsaye tana kallonshi ya miko mata damin kudi ya mata alama da kai akan taje ta basu. Haka tabi mutanen tana mika masu duk adadin data debo, kallon farin cikin da yake fuskokinsu tayi, sai ta tuno lokacin da take neman kudin maganin Hanan. Ko da wannan Allah ya barta ya gama mata, bata samu damar nan ba, amma da Allah ya bata damar taimakama wasu da yaye masu wani bangare na irin wannan kuncin, dukda bada kudinta bane, yaci ace ta gode ma Allah.

Mota suka koma Rayyan saida ya shiga supermarket ya siyo biscuits da lemuna kafin suka nufi wajen mabarata, ita duk ya tsayar da ita, ta rasa me zatayi, wata irin kunya da nauyin Ubangiji takeyi. Shin ko dan rahamar daya mata bazata gode mashi ba? Ya barta da ranta, lafiyarta sannan ya bata wadanda suke kula da ita tamkar yaruwarsu ta jini. Tunda suka baro wajen mabaratan nan take maimaita 'Astagfirullah' a zuciyarta. Ba sai Rayyan ya mata magana ba, wa'azi ya mata wanda ba'a taba mata irinshi ba.

Idanunta rufe bata lura sunzo asibitin ba saida taji alamar motar ta tsaya, juyowa tayi tana kallonshi taga ita yake kallo. "Nasan akwai damuwar da therapist yake iya taimaka ma mutum ya samu Allah ya yaye mashi, amma ina mai tabbatar maki da babu wani therapist kamar Allah. Ki roki Allah ya yaye maki dukkan wata damuwa dake zuciyarki, Ramlah. Ba lallai sai kin fada abunda yake ranki ba, Allan da yayi ki yafiki kusanci fiye da zuciyar dake bugawa a kirjinki. Ki rok'i rangwame da sassauci daga wajenshi. Zaki shiga asibitin muje?"

Juyawa tayi ta kalli asibitin kafin ta juyo tana girgiza mashi kai a hankali, "I want to talk, zaka saurareni?" Gyada mata kai yayi a hankali yana gyara zamanshi a cikin motar ta yadda zai zamana yana fuskantar ta.

"Na rasa Abban Hanan lokacin da bani da kowa saishi, Rayyan, bansan ya zanyi da rayuwata ba. Sannan kuma Hanan lokacin likitoci suka tabbatar man an haifeta da rami a cikin zuciyarta. Banda wanda zan fada mawa, ni ba karatu me zurfi nayi ba balle ace na samu aiki, idan kuma nace zan samu aiki gidan mutane ko kuma wani wajen wa zai kula da Hanan da kusan kullum bata lafiya?" Hawayenta ta share, a ranta tana rayawa Insha Allahu daga yau zata rungumi kaddarar rayuwarta hannu bibbiyu. A da ta dauka babu wani wanda ya kaita kunci, amma yau ta gane a hakan ma Allah ba karamar rahama ya mata ba.

Ganin mabaratan nan yasa ta fahimta cewar samun makwanci da abunda mutun zaici ba karamar rahama bace. Dataje asibiti taga koda kanada wadannan abubuwan lafiya itace komai. Sadda taje makabartar nan kuma sai taga a barka da rayuwar taka ma ya isheka ka gode ma Allah.

Magama takewa Rayyan tana fada mashi yanda takeyi a ranta, yanda take tunanin bazata iya hakura ba. "Nasan Hanan tana kaunata a matsayina na mahaifiyarta, amma kuma tana matukar kaunar Abbanta. Nasan raunin imani ne zan yadda da mafarkin da nayi a akanta, but I couldn't help it, Rayyan. I'm still young, amma life has been tough for me, wani lokacin sai naji inama ace na dade a duniyar nan yanda zan fahimci abubuwa da dama da suke faruwa dani..." haka take mashi magana saida ta tsaya ta share hawayenta. Tana sane da mutanen da suke kallonsu masu wucewa amma bata damu ba. Tasan Dr Aliyu da Dr Mahmud a shirye suke da suji labarinta, amma yanda Rayyan yake sauraronta kadai ya isa ya rage mata wani babban bangare na abunda ke damunta.

A hankali Rayyan ya fara mata magana cikin kwanciyar hankali yana nusar da ita. Tun tana kuka har ta daina ta dawo ta natsu tana sauraronshi. Koda suka dauki hanyar gida ji take kamar an daga wani dutse daga kirjinta, sannan kuma bata daina istigfari ba. Ajeta yayi ta juyo da dan guntun murmushi, "Nagode, and thanks for showing me the way."

Ranar yini tayi tana istigfari, koda Mama ta dawo ta iske Ramlah a kitchen tana girki ba karamin mamaki tayi ba. A tare suka gama girkin sai ga Ramlah ta dawo duk ta galabaita. Da fara'a Ramlah ta tarbeta abunda bata taba yi mata ba. Dukda cewar tayi mamaki amma sai ta maze.

Suna zaune su duka harda Rayyan suna cin abincin dare wayar Ramlah tayi kara, dan kallonsu tayi taga kowa hankalinshi yana kan abincin da yakeci kafin ta dauki wayar. "Hello Ramlah? Ina kofar gidan." Amsawa tayi da toh kafin ta kalli Mama da Lubnah.

"Dr Aliyu ne yazo, yace yaga banje asibiti ba yau shine zaizo ya dubani."

"Nidai anya Dr Aliyun nan? Mama kodai biki zamusha?" Lubnah ce ke fada cike da wasa tana dariya, itama Ramlah dariyar tayi tana fadin "Kai Lubnah, patient dinshi kawai yazo gani."

Mama ma da dariyar farin cikin yadda Ramlah ta saki ranta tayi magana, "Rabu da ita kinji Ramlah? Jeki sai kin dawo." Daga haka ta fita falon, dama jallabiya ce jikinta, dankwalin kawai ta warware ta yana shi saman fuskarta. Har ta bace da ganinshi Rayyan bai daina kallonta ba, sai a hankali ya maido hankalinshi kan Mama wacce take fada mashi yadda zasuyi investing a wani factory ita da mahaifinshi.

MIJINA NE! ✅ Where stories live. Discover now