10

37 1 2
                                    

          Rikicewa Deen yayi yanaji kamar yayi karamin hauka,fadi yake tabbas da zai iya dawo da moment dinsu baya daya dawo dashi ya tsige niqab dinta,infact dayasani sace ta yayi kawai ya huta,ya killaceta har sai ta fadamasa WACECE ITA?,amma how could he be so foolish hartayi fooling dinshi haka?,shi har zuciyarsa ya dauka aljanu ne da ita,ashe he was mistaken kawai ta masa wayo ne,be manta da abunda yaji ba,be manta da laushin jikinta da haryau ya kasa tantance wani irin laushine haka kamar wacce batada kashi a jiki?.... "Ya Salam" Ya fada yana dora hannu akai,sai kuma ya koma street din da suka hadu,still be ganta ba,sai ya cigaba da tafiya a kafa batareda yasan ina ya nufa ba,saida ya shiga duka streets din dake area amma begantaba,takaici ne ya kamasa kawai ya zube a kasa a tsakiyar titi dayake irin isolated area dinnan ne da baka samun mutane sai tsiraru,lumshe ido yayi ya cigaba da tinanin inda ze ganta......... Yana cikin wannan halin yaji phone dinsa na ringing,wayar dayayi abandoning for days,yana ganin ana kiransa amma baya dagawa,yana sane kuma yaki kashewa...... 'This Woman' ya gani akan screen din kamar yanda ya mata saving,for the past two months tana kiransa amma baya dagawa,yau kawai yaji yanasan dauka..... Picking call din yayi yasa a hands free....
Cikin muryarta me cike da kamala tace "Assalamu alaikum Saifuddeen"..... Shiru yayi yana me jin wani sanyi a ransa,sai kawai ya amsa sallamar a zuciya...
"How're you doing?"....
"Ina lafiya" Ya fada kamar bayasan magana
"Inata kiranka for months kana ignoring calls din,hakan ya dace?" Ta fada da kunan rai,kanaji kasan abun na tabata..... Be kulata ba ya cigaba da sauraranta......
"Where are you now?" Ta tambayesa
"Gida"... Ya bata amsa a gajarce
"Baka gida saifudden!, kabar inda kake".... Kashe wayar kawai yayi jin zata fara rainin hankalin data saba..... Cigaba da kira tayi babu kakkautawa,yana gani kuma yaki dagawa,daya gajima sai ya kashe wayar gabadaya.....
Cigaba da zama a gurin yayi kamar me neman gafara,ya lumshe ido yana tinanin yanda ze bullowa alamarin daya damesa.......
Kamar ance ya bude ido kawai yaga mutane kusan 20 sun zagayesa ko wanne dauke da bindiga a hannunsa fuskokinsu rufe da mask,kafin ma ya motsa suka fesa masa wani abu dan sunsan tsap zece zeyi kokawa dasu and he can play very smart,a take ko abun da suka fesa masa ya sumar dashi,suka kinkimesa suka sasa a mota sukayi gaba dashi......... Ogan su ne ya dauki waya ya shiga kiran wanda yasasu aikin..... Ana daga wayar yace "Deal done!,ko a kashesa kawai boss?".... Banji me aka ce a dayan side dinba,ogan su ya sake cewa "Your wish is my command".......

         
    Dialing number Hajiya fatima(aminyar mahaifiyar eesha) eesha tayi tana Allah Allah ta dauka..... Sake kira tayi nan ma shiru baa dauka ba,kasa hakuri tayi ta shirya ta fita,karasawa gate tayi tana ordering bolt,batafi 5mins da tsayuwa ba blot drivern yazo,shiga tayi dan already tayi plqcing location din hajiya fatimah........ Ko rufe motar batayiba ta fita,already tayi setting bolt dinta to pay with card so bata da case din tsayawa biyan kudi,karasawa tayi gaban gate din mansion din,knocking tayi me gadi ya bude ya laleko,ganin itace yasa be kira landline for confirmation ba,bude mata yayi ta shiga da sauri......
Da sallama ta shiga main parlour,as usual hotonsa ne ya mata welcome kamar yanda ya saba yiwa kowa welcome saboda daidai center entrance din parlourn ne,har wani lumshe ido tayi tsabar jin dadin ganin sanyin idaniyanta..... "My crush" Ta fada beneath her breath...... Mantawa da abinda ya kawota tayi tashiga bin hotonsa da kallo,tafi 10mins a haka harta farajin takun tafiya,sai a lokacin ta dago da sauri.......
Karasowa hajiya fatimah tayi tace "Daughter kece a tafe?,welcome"......
Murmushi eesha tayi tace "wlh nice Mahmah,tun dazu na shigo fa,na tsaya ina bin hoton yaya da kallo,wai dan Allah yaushe ze dawo"....
"Soon,na fadamiki akwai wani course dayakeyi abroad ne,yana gamawa ze dawo"
"Can't wait wlh,Allah ya dawo dashi lafiya"...
"Ameen,naganki haka by this time,thought you're supposed to be in class by now?"....
"Yes but....,labari nazo kawo miki"....
"Koma menene stop joking with your education,everything can wait okay?"... Mahmah ta fada on a serious note,dan ita haka take she's so jovial amma da taga yaro zeyi badede ba zata taka masa birki........
"I'm sorry Mahmah,bazan sake ba Insha Allah"
"Yauwa good girl,ina jinki meya faru?"...
"It's about that my roommate,the unknown girl,yau ta dawo".... Ta fada cikin farinciki sosai
"Kai masha Allah,hankali ya kwanta kenan,toh ya kukayi da ita?"....
Dariya eesha tayi tace "wlh there was a progress a big one"... Nan tashiga bata labarin yanda sukayi da fatima zainab.....
Murmushi Mahmah tayi ganin yanda eesha ke bada labarin with so much joy,sannan tace "I'm so happy for you daughter,ki cigaba dabin tactics din dana baki a sannu zaki gane wacece ita as I said earlier,meanwhile if anything come up call me on phone,karki dinga katse abubuwan ki,okay?"
"Yes mom,kuma na kiraki ma ganin baki dauka bane ya sani zuwa,I couldn't hold it".....
"Ehyah I was charging my phone bansan kin kira ba,now get yourself comfortable".... Nan ta kira laure ta landline din parlourn domin ta kawowa eesha refreshment........

WACECE ITA⁉️(WHO IS SHE⁉️)Where stories live. Discover now