38

17 0 0
                                    

"Wani country kikeso mu tafi? I don't know if you have any in mind?".....
Zatayi magana kenan taji khaleel ya kwallara ihu, ko kafin ta fahimci abinda ke faruwa khaleel ya sake sakin wani ihun dayafi wanchan saboda yanda yaji kamar anbuga masa guduma akai gashi he wasn't prepared bare ya kare kansa, daga sama kawai yake jin bugu....
Juyowa tayi da sauri daidai lokacin sukayi ido hudu da Deen daketa naushin khaleel ta baki ta hanci ta ko ina, idanuwannan nasa sunyi jawur ga muscles dinsa da suka fito rado rado kana gani kasan ma'abocin karfi ne da cikar halitta...Gashi dai dukan khaleel yake amma idonsa na kanta.....
Sandarewa tayi a tsaye tana kallon Deen da sai jibgar khaleel yake ta kasa yin komai......
Sake kaiwa khaleel da bakinsa ze zubar da jini naushi yayi yana fadin;
"Ashe dama duka danginku mugayene azzalumai? Na dauka soyayyar tsakani da Allah kake mata ashe kaima wani abun kake nema a gurinta kamar ubanka Ibrahim?! Ubanka be kyaleta ba kai baka kyaleta ba kasheta kuke sonyi ne? Toh kunyi naku kungama a sannu kuma zanyi maganinku gabadaya! Kaje ka gayawa ubanka ni Saifuddeen nasan abinda kuke shiryawa kiris ya rage na tarwatsaku duka, sannan zan baka last warning ka fita harkarta dan ko a mafarki bazaka taba samunta ba, she doesn't deserve a useless stupid person like you!!".........
Da sauri khaleel ya mike yaci kwalar rigar Deen yana hucin wahalar bugun da yasha yace;
"Kayi kadan ka rabani da wifey! Kayi kadan! Waye kai? Yaushe kasanta? Get the f**k off out of our life!!"......
Wani zazzafan mari Deen ya daukeshi dashi ya fizge hannun khaleel daga rigar shi yace;
"A gidan ubanwa ta zama wifey din? Naga kamar baka dakuba tinda kana da bakin gayamin maganar banza!!"....
Deen ze sake kai masa mari kenan kawai khaleel ya zaro bindigar daddy daya fito da ita ya saita akan Deen.......
"In baka kasheni ba ni yanzu zan kasheka!".....
Cewar khaleel yana dada saita bindigar daidai kirjin Deen.......
Ganin abun nasu ya fara wuce na hankali tinda har bindiga aka fara zarowa yasa fatima zainab saurin shiga tsakiyarsu, murya na rawa tace;
"No khal karkayi haka, dan Allah karkayi haka, karka kasheki".......
"Akanme zakice karna kasheshi? Ko son shi kike?".......
"Wallahi bana sanshi, na fika tsanarshi ma, karka kasheshi because of his family".......
"It doesn't matter! To hell with his family!".....
Ganin fa dagaske khaleel so yake ya harbi Deen yasata rungumeshi da sauri dan dagaske bata so ya kasheshi kodan Mami da Umm da suke nuna mata kauna sosai, a take jikin khaleel ya mutu jinta a jikinsa, abinda bata tabayi gashi kuma beji irin abinda yaji lokacin daya tabata ba saima wani sanyi da dadi dayaji ya saukar masa lokaci daya......
"Please ka kyaleshi, muda zamu barmusu kasar? Ka rabu dashi kawai".......
"Okay wifey"....
Ya fada chan kasa jin yanda ta saukar masa da kasala lokaci daya......
"Give me the gun".....
Fatima zainab da har lokacin hankalinta be kwanta ba tana ganin kamar khaleel ze harbi Deen tace ya bata.......
Ba musu kamar wanda ake controlling da remote ya mika mata bindigar.......
Kamar a mafarki Deen yaga ta rungume khaleel, sosai ya shiga shock har saida yaji komai na jikinsa ya tsaya, kamar statue haka ya tsaya yana kallonsu yanajin kamar yayi kuka wai a gabansa zasu rungume juna? Abun da ciwo gaskiya, kamar wanda aka mintsina ya dawo hayyacinsa, fuzgota yayi daga jikin khaleel sannan ya zare bindigar dake hannunta.
Janta ya shigayi kamar akuya yayi hanyar barin wurin da ita, nan khaleel yace masa be isaba, sai aka fara jaye jaye, wannan yajata wanchan yajata kamar dai rago, last last Deen yayi succeeding ya janyeta, sunkutarta yayi da sauri ya nufi inda yayi parking motarsa da ita, yana zuwa ya bude back seat ya wurgata ko tsoron taji ciwo bayayi tsabar yanda ransa yake a bace........
Ko kafin khaleel ya karaso sun bar gurin, shiga motarsa yayi ya bisu a baya a shima......
Wani irin mugun tuki Deen yake kamar ze tashi sama, kauce masa kawai ake a hanya, tuni ta dade da galabaita tin a jaye jayen da suka dingayi da ita har numfashinta dakyar yake fita, sosai tsanar Deen ta ninku a ranta dan ya zame mata tamkar karfen kafa tinda ya shigo rayuwarta, ada ita ake bi kuma sai abinda tace amma yanzu dole yake mata saita bishi ko tana so ko bata so, yazo yayi kane kane akan lamarin rayuwarta kamar wani ubanta.......
Ikon Allah ne kawai ya kawosu gidan mami dan duk inda sukabi sai andinga Allah yasa karsuyi hatsari da mugun tukinnan da me motar yake.......
Horn yake babu kakkautawa a bakin gate din gidan mami, sai akayi rashin saa gateman din daya gama jinya ya dawo ya tafi ya dan zagaya, da sauri yazo ya bude kofar bayan ya fito, yana ganin Deen ne ya manna a guje dan be manta illar dayamasa ba last time, a halin yanzu ma hakorinshi guda daya ya tafi.....
Ko daidaita parking Deen beyiba ya fito daga motar, janyota yayi ya fito da ita sannan ya fara janta da karfi har ya kaita parlour mami, wurgata a kasa yayi ya cire belt din jikinsa dan yasan inbe fasa mata jiki yau hankalinsa baze kwanta ba, zuga mata guda daya yayi ta saki wani karar da saida gidan ya amsa, ze kara zubamata kenan Umm ta rike hannunsa tana fizge belt din tace;
"Ashe baka da hankali saif? Meh tamaka zaka duketa? How can you even think of beating a lady, ashe bakada imani baka da tausayi? Tarbiyyar aka baka kenan?"........
Tinda Mami da Umm sukaji wannan mugun horn din sukasan Deen ne, da sauri suka sauko saidai anyi rashin saa dan har ya fara zuga mata belt din......
"Umm dan Allah ki barni in babballa yarinyar nan ko zuciyata zata samu salama, kinsan metayi ne?"........
"Koma me tayi be kamata ka tabata ba kodan lafiyarta sannan a responsible man won't beat a lady kome tayi kuwa"...........
"Count this stupid girl out, dan Allah ki bani in fasa mata jiki!"......
Ya fada yana fizge belt din a hannun Umm ya daga da nufin cigaba da dukanta mami ta sauke masa wani lafiyayyen mari tana sake kwace belt din.......
"Wai me yake damun brain dinka ne? Akanka aka fara zafin zuciya ne, kai a wa zakazo kana dukan yarinyar mutane? Meyasa bakada tinani ne? Tana fama da kanta zaka duketa, inka kasheta ai sai kafi kowa shiga damuwa, bismillah cigaba da dukanta"......
Ta fada tana mikashi belt din.....
Durkushewa yayi a kasa yanajin kamar yasa kuka, tabbas da ze iya kuka da yau yayishi saidai duk girman abu taurin zuciyarsa bata bari yayi kuka, ko mami da dad da suka haifeshi basu taba ganin kukansa ba, haka Umm ma data renesa.......
"Kunsan me suke shirin aikatawa ne? Guduwa fa zasuyi itada yaron mugunchan da bamusan dame yake nemanta ba, amma saboda karamar kwakwalwarta take cemishi zata bishi su gudu suyi aure gasu tantabaru, har fa I love you tace mishi mami, wai har wannan yarinyar tasan soyayya Umm?"......
"Au yanzu kuma tayi yarinya ta fara soyayya? Ina cewa kayi zaka mata aure dama? Tinda ga wanda takeso sai ka aura matashi"....
"Wallahi bazata aureshi ba Umm, yes she's too young for love kamata yayi ta maida hankalinta kan karatunta! Ko auren zan mata bazan aura mata shashasha irinta ba bare na fasa mata auren, karatu nakeso tayi".......
Yana fadin haka ya fice daga parlourn....
"Wai meke damun brain din yaronnan ne Umm?"......
"Hmmm mu tayashi da addu'a kawai, I'm speechless".....
Lallashin fatima zainab data fara kuka bayan fitarsa suka hau yi, birkice musu tayi ita saita bar gidan bazata zauna da wannan mugun a gida daya ba dan dagaske fushinsa ya tsoratata, hakurin duniya sun bata taki hakura sai kuka take musu ita bazata zauna ba, Umm ce ta kalli mami tace;
"Innalillahi yanzu ya zamuyi? Kinga abinda ya janyo ko".....
"Huh meye abunyi banda mukirasa yazo ya san nayi tinda shi ya jawo komai!"......
"Bari in kirasa".....
Fita Umm tayi ta tafi part dinsa da beda wani tazara dana mami, samunshi tayi yanata safa da marwa kamar wanda aka yiwa wahayin masifa, harararshi tayi tace;
"Tace bazata zauna a gidannan ba, sai kazo kasan yanda zakayi da ita!".....
Ta fada tana ficewa daga parlourn......
Da sauri yabi bayanta dukda har lokacin be wuce ba, so yayi yaki zuwa ya nuna musu yayi zuciya da ita taje duk inda taga damar zuwa sai zuciyarsa taki bada hadin kai kawai yabi bayan Umm......
Kukanta ne ya fara masa iso tin kafin ya karasa parlourn, sosai yaji zuciyarsa ta karaya akan yanda yaga tana kuka, shida ko wani ne yasata kuka sai inda karfinsa ya kare sai gashi shine ya sata kuka da kansa? A kuma lokacin ya fara nadamar yunkurin dukanta dayayi har yakai ga zuba mata belt sau daya, meya aikeshi meya kaishi? Yanzu da badan an kwace belt dinba me zai faru?.... Girgiza kai yayi ya tsuguna daidai inda take, su mami na ganin haka suka haura sama suka barsu su karata......
Hannunsa yasa ya goge mata hawayenta sannan cikin kwantar da murya kamar bashi ya gama masifa dazu ba yace;
"Stop crying baby girl! Banaso kan ki yayi ciwo".....
Bige hannunsa tayi tace;
"Bazan dena kukan ba kuma bazan zauna a gidannan ba!".....
Pecking hannunta yayi ya dauko belt din yasa matashi a hannu yace;
"I know I did you wrong, gashi ki rama ko guda nawa kikeso, amma dan Allah karki kara cewa bazaki zauna a gidannan ba".....
"Wallahi bazan zaunaba, kai mugune".....
"Naji ni mugu ne but I'm a changed person now, I promise bazan kara miki masifa ba kuma bazan kara dukanki ba amma ki rama naki yanzu sai ki dena jin haushi".......
Batace komai ba ta shiga shauda masa belt din da karfi a jikinsa, daga baya dataga kamar dukan baya shigansa tace ya mikohannunsa, mika mata hannun yayi ta shiga jibgarsa kamar mallama dalibinta.....
Dariya ta bashi sosai har saida ya kasa rikewa, betaba tinanin yarinyarta takai haka ba sai yau, wannan aka mata aure yanzu ai akwai matsala, harda ce mishi karya janye hannunsa sai tace ya janye, toh kawai yace mata ya cigaba da kallon ikon Allah dan an zuba mishi belt yafi so talatin a hannu and he didn't complain kamar yanda yace.......
Sake sakkowa su Umm sukayi jin karar duka su a tinaninsu Deen ne yake sake dukanta, sai dai me? Gani sukayi Deen ya mika hannu tana zuba masa bulala yana murmushi kamar wanda ake yiwa abu me dadi, tabe baki mami tayi tace 'sunfi kusa', suka juya suka koma sama......
Saida tayi me isarta lokacin hannunsa yayi ja kasancewarsa farin mutum sannan ta dakata dan itama ta gaji.......
"Ya kika tsaya, ya isheki haka ne?"......
"A'a sai anjima zan cigaba"......
"Ba matsala yanzu kin dena fushi dani baby girl?"....
"I'll decide later"......
A ranta ko cewa take kome zakayi saina bar gidannan kuma bazan taba dena fushi dakai ba.....
"Allah ya kaimu, zo muje muyi girki kinga bakici abinci ba muka fita"......
"I'm not hungry and I can't cook"....
"I know, muje in koya miki".....
"Banaso!".......
"Ki daure muje in koya miki karki auri foodie yace ze miki kishiya saboda baki iya girki ba, dama irina zaki aura baki da case dan babu abinda ban iya ba".....
"Khaleel knows that I can cook and he loves me like that".....
Nan da nan fuskarsa ta chanza, belt din data gama dukansa dashi ya dauka, a tsawace yace;
"Idan muna magana kina sakomin maganar wani namiji saina fasa miki baki".........
Tashi tayi ta shige daya daga cikin bedroom din dake kasa dan bazata tsaya ya hallakata a banza ba gashi ya dauki belt, in yace ze rama dukan data mishi ai suma zatayi yanda bata da kwarin jikinnan......
"Da kin tsaya ai, mara kunya fisararriya kawai!".....
Zama yayi a parlourn ya kunna tv yana gadinta dan tsoro yake karta gudu dukda yaga kamar ta hakura amma ita ba abin yarda bace dan ya kula tanada wayo sosai, murmushi ne ya kwace masa daya tina abinda ya faru last night, wai yar yarinya da ita harta san tayi seducing mutum ya mata abu?, sai kuma ya hade rai tuno yanda ta rungume khaleel harya mika mata bindiga kamar wawa, yanzu duka khaleel yaji komai na jikinta, tudun kirjinta da komai?, kodai haka take yiwa maza idan tanaso su mata abu tinda rannan ce masa tayi tasan abinda zatayi a bata codeine kyauta, glass cup din dake center table ya dauka ya fasa shi ko zeji sanyi a ransa, chan kuma sai ya tashi ya fara bubbuga kofar dakin da take cikin daga murya yace;
"Ki zo ki bude kofarnan kona ballata! Yau sai kin gayamin wa da wa kika taba runguma a rayuwarki,Ki bude nace!".......
Banza ta mishi kamar bata jishi ba, haka ya karaci bugunsa bata bude ba, karshe barin part din yayi gabadaya ya tafi yayiwa kansa allurar bacci ko zai samu saukin abinda yakeji, nan take bacci me nauyi ya daukesa.........

WACECE ITA⁉️(WHO IS SHE⁉️)Where stories live. Discover now