25

27 1 0
                                    

A nitse suke tafiya motar Deen a gaba sai tasu Mami dake biye dashi a baya, musamman mami tace ya shiga gaba dan suna ganinsa kar suce ya biyosu a baya yayi wata hanyar yanda ya nuna musu bayasan komawa dama.....
Minti minti Deen yake juyowa ya kalleta gabadaya zuciyarsa a dagule, shi bawai bayasan komawa prison din bane a'a so yake ta farfado ta fadamasa WACECE ITA? sannan ya kaita gidansu ya musu kashedi akan rashin kula da ita gashi ana so a cutar da ita....
Haka ya cigaba da sake sake har suka karaso prison, parking yayi yaki fitowa daga motar saima juyawa da yayi yana kallonta, nan wani tinani yashiga ransa kan meyasa koda yaushe take kunshe cikin hijabi? Kodai akwai wani abun da take boyewa ne? Shifa yanzu baze iya yarda da yarinyar nan ba, sai ya fara dana sani da be cire hijab din gabadaya ba ranar da ya mata allura, sai kuma yaga ai yana cikin tashin hankalin haukar data dingayi ranar, shi ko kallonta beyiba daya dage hijab dinta, amma zeyi maganinta dan sai ya gano me take boyewa, hardasu hand gloves da socks tsabar munafurci?...
Umm ce ta katsesa da fadin
"Ya kayi zamanka a ciki kuma, fito mana"....
Fitowa yayi yana addu'ar Allah ya dorasa akan Umm ta tayasa bawa mami hakuri a barsa ko zuwa gobe ne.. Cikin fuskar tausayi da damuwa yace;
"Umm na yanzu dawo dani kukayi da gaske?"...
Ba yabo ba fallasa tace;
"Ga zahiri ka gani"...
"Dan Allah ku barni zuwa gobe idan na mayar da ita gidansu".....
"Karka damu zamu mayar da ita"...
"Bazaku iya da ita ba, kinga fa yanda takeyi Umm"...
"Aljanu ne suke damunta ba kariga ka cire su ba? Insha Allah lafiya lau zata farka"....
"Ai basu fita ba, zasu dawo"...
Ya fada cikin rashin sanin abinda zece su yarda ya zauna".......
Harara mami tashiga aika masa batareda tace komai ba, Umm ce ta zaro ido itace;
"Ikon Allah wato fata kake mata su dawo kenan? Anya saif wannan taimakon na tsakani da Allah ne?"...
"Wallahi tsakani da Allah ne, ni nasan basu gama tafiya bane, ina ganewa idan aljanu na jikin mutum".
"Yaushe ka zama sheikh bamu sani ba? Kafa ji tsoron Allah saif!".....
"Ke kika tsaya kina kulasa ma yanata zuba miki shashanci, mu zaka maida wanda basu san abinda sukeyi ba, yaushe ka fara harka da aljanu bamu da labari?".....
Sai a lokacin mami tayi magana....
Shiru yayi yana shafa gemu kamar wani ustaz, ya rasa meyasa yake sakin layi akan yarinyar, idan yayi kokarin billewa wani gurin sai yaga ashe kama kansa da kansa yayi, in banda haka shi meya hadashi da gane masu aljanu? Bema taba yiwa wata karatu ba sai a kanta.....
Gyaran murya mami tayi tace;
"Ka bude kunnuwanka da kyau ka saurareni sannan ka gayamin iya gaskiyarka, hakan ze iyasa na maka sassauci, sannan inaso ka sani maganar nan daga gurinnan ba zaa kara tadota ba, ya rage naka ka fadi gaskiya".....
"Ina ji"....
"Are you in love with her? Dan wannan rawar kafar da kakeyi akanta ba kalau ba, so tell me kana sonta ne?".....
"Mami wani kalan tambaya ne wannan?"...
"Bansan dogon surutu, just tell me yes or no?"....
"NO!"....
"Good, Umm ki zama witness even though kema kin masa same question, we're not coming back to this, that no will be forever!! Wallahi wallahi baza a sake tada maganarnan ba!!"......
Gyada kai Umm tayi tace;
"I'm a living witness, Insha Allah maganarnan an barta har abada!!".....
"Ina mask din daka fita dashi?"....
"In the car"...
Deen ya fada murya a sanyaye.....
"Shiga ka saka, ta inda aka hau tanan zaa sakko".....
"Ok, amma mami ya zakuyi da ita, naga bata tashi ba haryanzu"....
"Karka damu!"...
"Zaku tafi da ita ne?".
"Yes"...
Wani sanyi yaji aransa datace zasu tafi da ita gida, ko banza yasan inda ze sameta"...
"Toh insa muku ita a motar ku?"...
"Who's car is this, nasan dai ba taka bace"....
"Ta sameer ce"...
"Ina yake sameer din"...
Dan jimm yayi yana tinanin abinda ya dace ya fadamata dan harga Allah bayaso yayi exposing dinsa......
"He left the country today"...
"It's a lie, yaushe kazama makaryaci Saifuddeen ?"......
Mami ta fada dan a iya saninta dashi komin dacin abu fadarsa yake ba ruwansa shiyasa ta tambayesa ko yana san yarinyar dan tasan in yana so kai tsaye ze fada.....
"I'm not lying, munyi dashi yau zebar kasarnan and probably ya tafi by now"...
"Oh kai ka bashi shawara ya gudu kenan? Yayi kyau, go get the mask"....
Bece komai ba ya shiga yasa face mask din ko kallon fatima zainab beyiba dan bayasan ya karawa kansa damuwa.....
Fitowa yayi suka bisa da kallo da jinjina wayo irin nashi na kawo idea din mask, ta ina zaka kallesa kace Deen ne when the mask looks so perfect kamar face din real mutum? har colour din skin dinsa yayi rhyming da mask din...
Dauke ido yayi be damu da kallon da suke masa ba ya sake komawa motar ya daukota ya sata a back seat din motarsu sannan ya sake dawowa cikin motar ya bude dashboard ya dauki wani abu a kulle a leda ya zira a aljihunsa sannan ya kashe motar ya zare key din ya boye a aljihunsa yana addu'ar Allah yasa kar mami tace ya kawo...
"Wayace ka daukota ka sata a motarmu?"....
Cewar mami bayan ya dawo inda suke....
"Naga kince tafiya zakuyi da ita"...
"Sai kuma akace ka dauketa? Naga you have legalized taba yarinyarnan kamar wata muharramarka, wani kalan sakalci ne wannan?"....
"Wallahi mami bada wani abu nakeyi ba, naga ku bazaku iya daukanta bane"....
"Haka muka fadamaka?"...
"No, I'm sorry"...
"This should be the last time da zaka taba yarinyarnan, am I clear?"...
"Insha Allah"...
"Good, muje ciki"....
Saida suka gaisa da securities din gurin da har lokacin basu gane komai ba sannan suka shiga ciki...

WACECE ITA⁉️(WHO IS SHE⁉️)Where stories live. Discover now